MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljan, Fita Ta 15

MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljan, Fita Ta 15

*Shafi na Goma sha biyar.*

 

 

Cikin tujara da masifa Inna Huraira tace, "Ba wanda ya dake ni Malam so nake ka mutu dan haka nake kukan banza da na wofi."

 

"Ikon Allah! To Allah ya baki sa'ar kukanki Huraira."

 

Yasa kai ya bar ɗakin Inna Huraira na ta zubar da ruwan masifar Malam ya rainata, zata miƙe tsaye kan lamarinsa, dan ita ba sakaryar mace nace da namiji zai wahal.

 

Bilkisu na zaune ɗakinsu tana buɗe tsarabarta da Major Nasir ya kawo mata, ta ji ana gardama da wasu muryoyi masu ban tsoro, dan haka ta bar motsi ta ƙame waje guda.

 

Sai kuma ta ji an kwashe da dariya ana cewa......

 

"Yarinyar nan dai da tsiya so ta ke ta fice tarkon mai gidanmu , ku ji bi yanda saurayin banzar nan ya kawo mata tsaraba sai murna ta ke."

 

Wata narkekiyar murya tace ..

 

"Allah da zai yarda da mun kaita fada tai masa bauta harta ƙare ƴan shekarunta a can."

 

 

Gaba ɗaya sai hankalinta ya tashi ainun har ƙwalla suka ciko mata idanuwa, to wai daga ina muryoyin ke fitowa ne ?

 

"Daga cikin ɗakinku." (Inji wata tsantsamar murya).

 

Toshe bakinta tayi dan kar kuka ya ƙwace mata, ta fara ambaton sunayen Allah.

 

"Ke daman ai haka kike, da anzo gunki yanzu kin ƙone wanda ya zo ɗin." (Wannan karon a fusace a kai maganar.)

 

 

Ita dai ta dage sai karanto addu'ar neman tsari take daga abokan gaba kamar haka;

 

 _"Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi ihzamil ahzaba, allahumma zumhum wazalzilhum_ ."

 

 

Sai ta ji tsit dan haka ta tattara kayan ta nufi shirin islamiyya dan zasu fara karatun saukar Alqur'ani ƴan ajin nasu.

 

Tana cikin tafiya dai-dai matoya ta ga Malam Aminu zaune kan kwalbati yana duba wani littafi, sadda kanta ƙasa ta yi dan bata ƙaunar ganinsa ko da wasa dan tafi son ta  wuce ta kusa da shi ba tare da ya gane ta ba ma.

 

Sai dai tana zuwa gab da shi ya ɗago kansa ya sauke mata idanuwansa masu razanar da ita , dole ta kalle shi amma ta kasa ko da ɗaga halshenta balle ya samu arzikin gaisuwarta.

 

Tana wucewa ba da jimawa ba ya ga ta dawo rai ɓace hannunta ɗauke da wani jan ƙyalle yana fidda jini ta sake wuceshi .

 

 

"Innalillahi! Yarinyar nan wata sabauta yau kuma?

 

Wuf ya mike tsaye ya cigaba da bin bayanta, ba tare da ta sani ba.

 

 

 

Tun ranar da Major Nasir ya je gun yarinyar yaso ace ya samu damar shiga ɗakinta dan aiwatar da ƙudirinsa a kanta hakan ya gagara, tabbas ba zai taɓa shafa ma rayuwar yarinyar lafiya ba tunda ta shiga rayuwarsa harma tai sanadin zubewar kimarsa a idon tawagar sa dan haka ya zama wajibi ya ɗauki fansar abin da tai masa.

 

Damuwarsa guda yarinyar akwaita da riƙon addinta, bata wasa da sallah hakama bata wasa da addu'ar neman tsari, bayan haka da tuni ya manta da wanzuwar ta doron duniyar baki ɗaya.

 

Duk wata hanyar da ya kamata yabi dan ganin ya samu nasara kanta ya bi amma saboda yawan ibadarta da addu'ar ta tamkar yana rubutu kan ruwa haka komi ke wucewa idan ya tsara .

 

Wani baƙin jini ya zubo daga idanuwansa mai tiriri da kauri.

 

Ya yi wata uwar gwaza yayi ihun da dajin gaba ɗaya ya amsa amo ya fara ɗaukar alwashi cike da tafasar zuciya.

 

Abin da ya razana fadawansa da sauran tawagar ta sa kenan suka shiga tashin hankali , dan rabon da Yah Malam yayi irin wannan ɓacin ran tun wani yaƙi da yaje shekaru Tamanin da takwas kenan, sai yau , alamar suma su shiga hankalinsu kenan inba haka ba zasu yabama aya zaƙinta.

 

Ta wani fannin kuma sai wasu suka fusata da lamarin harma suke jin ya kamata su ɗauki matakin gaggawa kan shegiyar yarinyar da ke fusata masu shugaban nasu a banza a wofi karma reshe ya juye da mijinta dan haka garama su taka ma  lamarin burki kafin ta jawo masu fushin shugaban nasu.

 

To fa! Ya ya kenan ?

 

To wai da gaske Bilkisu ce Malam Aminu ke bi ?

 

Idan itace jan ƙyallen jinin miye cikin sa ?

 

Ina zata je kuma ?

 

 *Ina gaisuwa  Ibnah .*

 

 *Taku ce Haupha