RINA A KABA
Ruƙayya Ibrahim Lawal
Runtse idanuna na yi da ƙarfi ina saka hannuwana na ƙara dafe su sosai, wai don kawai na daina ganin munanan hotunan da afkuwar motsin su ya haddasa mini matsalar da nake ciki. Sai dai duk da hakan da na yi bai hana hotunan kokawarar janye jarkokin juna daga bakin famfon da muka yi da Zainab haskowa a ƙwaƙwalwata ba.
"Don kin riga ni zuwa nan ai ba ki riga jarkata zuwa ba, dole sai na ɗibi ruwan nan Aliya kafin na bari ki ɗiba." Sautin muryar margayiyar ya dawo a kunnena raɗau kafin wasu hautsinannun sautuka suka dinga shawagi a kunnuwana ina jin ƙarar amsawar su tana barazanar tarwatsa saitin ƙwaƙwalwa da wayoyin massarafar sautina. Ina shirin saka hannu na toshe ramukan kunnuwana na tsinto sautin da ya fi kowanne taratsi da ɗaga mini hankali yana faɗar "Ku kama ta ita ce ta yi kisan, macijiyar sari ka noƙe ce."
Da hanzari na janye hannu daga fuskata na zurma yatsuna biyu manunai na toshe ramukan jin nawa ina ƙwalla firgitacciyar ƙara da maimaita faɗar "Ba ni ba ce, wallahi ba ni ba ce." Da nake yi.
Sai dai kuma na yi imani da cewar ba wanda zai gasgata furucin da ni kaina na kasa gasgatawa don haka a hankali na cire hannayena ina ƙara ƙanƙame cinyoyina da na cusa kaina a tsakiyar su sai kyarma na ke.
'To idan ba ni ba ce wa ya kashe mini ƙawata kenan? Me ya sanya hannuna ya sauka a jikinta? Waya taɓa ta ta faɗi matacciya?'
"Ni ce, tabbas ni ce." Na amsawa ƙwaƙwalwata tambayoyin da take yi mini aringizon su cikin raunanniyar murya.
Idan ɓera da sata fa daddawa ma da wari don haka idan an bi ta ɓarawo a bi ta ma bi sawu. Azancin da suka faɗo raina kenan da suka tilasta mini ɗago kaina na sauke idanuna a kan ƙarafunan ɗakin mai kamar keji da nake ciki a killace.
Kamar a majigi na fara ganin wulgawar hotunanmu masu motsi ni da Zainab a lokacin da muke ta kici-kicin janye jarkokin juna daga bakin famfon, kowaccen mu tana janye ta 'yar'uwarta tare da ɗora tata a bakin famfon da ke zubo da ruwa. Can na hango ni tsaye ina fuskantar Zainab a fusace na cika fam kamar balambalam ina maida mata amsar furucinta na cewa sai ta ɗebi ruwan kafin na ɗiba.
"In kin isa ba mace ce ta haife ni ba, ta ya zan zo nan tun da azahar na kwashe awanni biyu ina jiran layi ya zo kaina ke da ba ki fi mintuna talatin da zuwa ba ki ce sai kin ɗiba, dake famfon na tsohonki ne ko?"
Furucin da ya fusata ta kenan ta mayar mini da martani a kausashe. "Idan ni ba na tsohona ba ne ina ganin ke kam na tsohon naki ne banza da ba ta san darajar iyaye ba."
Wannan zancen nata ya ƙara hassala tunzurarriyar zuciyata mai saurin fusata na yi kanta kamar kububuwa ban jira komai fa na falle ta da lafiyayyin maruka guda biyu da suka haddasa mata tangaɗawa. Ina jiran na ga ta sake direwa a kan ƙafafunta sai kawai na ga ta faɗi sharaf kamar tsohuwar katanga.
Ba shiri magidantan da suke zaune a gefe kusa da mu da wasu samarin da suke cikin dogon layin famfon burtsatsen suka yo kanmu suna salati. Magidantan suka shiga jera mata sannu da ƙoƙarin su tashe ta, ni kuma samarin suna ta faɗa da ni a kan rashin haƙurina. Kawai sai na ji wani ya rafka salati yana shaidawa mutanen wurin cewa ruhin Zainab ya yi bankwana da gangar jikinta.
Wata irin hajijiya da jiri na ji suna ɗiba ta na kasa motsawa daga inda nake a tsaye tsabar ɗimaucewa. Daga mari sai mutuwa? Ta ya hakan za ta faru? Ko dai sharri ake son a yi mini.
Kafin giyar firgici ta sake ni na ji ana faɗar ku riƙe ta ita ta yi kisan macijiyar sari ka noƙe ce. Sai a lokacin na samu kuzarin zabura da niyyar guduwa aka rirriƙe ni sannan aka kirawo 'yan doka suka taho da ni nan.
Ɓat hotunan namu suka yi ɓatan dabo daga idanuna dalilin saukowar ruwan hawaye daga girgijen idanuna zuwa doron kumatuna.
Ban damu da share su ba zuciyata ta shiga ƙara karanto mini wasu shafukan da ke cikin labarina da suke saka ni amincewa da sashen zuciyata da yake ba ni tabbacin ba ni ba ce mai laifi na dai taka sawun ɓarawo ne.
'Taya za ki amsa laifi bayan ga manyan 'yan siyasa da masu kuɗin unguwa? Shin kin manta cewa haƙƙin samar muku da wadataccen ruwan amfani a wuyan su ya rataya? Ko kin manta cewa ke da ita da sauran al'ummar yankinku duk amanar da Allah ya ba su ce? Shin sun sauke wannan nauyin ko kuwa suna ci gaba da yi muku kisan mummuƙe ne? Me ya haɗa ku faɗa har kika taɓa ta ta mutu? In ce sanadin rashin ruwan ne dai.'
Zuciyata ta ci gaba da zuga ni a kan lallai na watsar da zancen farko na yi ƙoƙarin ƙwatar 'yancinmu don kuwa an cutar da mu duba da cewa shekaru takwas kenan muna fama da tsananin rashin ruwa a yankinmu har duka fanfunan gidajen yankinmu sun ƙafe.
Mafi yawan mazauna unguwar tamu masu ƙaramin ƙarfi ne da yawan su da ƙyar suke ciyar da kansu, masu wadatar unguwar ba su fi biyar ba. Duk da cewa a cikin su har da Chairman na gundumarmu wanda ya kamata a ce shi ne mai ɗauke ɗawainiyar komai tamu tun da yana sane da cewa idan lokacin kakar zaɓe ya zo shi ne mutum na farko da yake zo mana da romon baka kana ya yi ta tattalinmu kamar ƙwai yana rarraba mana abubuwa.
Ashe duk yanayin haka ne saboda ƙuri'unmu da yake zawarci wa na saman shi. Duk da cewa sai a wannan shekarar na isa yankar katin zaɓe amma na san matsalolin da ake fama da su yayin jefa ƙuri'a don kuwa ni kaɗai ce 'ya a wurin mamana kuma nake bi mata dogon layin da ake hawa a lokacin jefa ƙuri'a wanda na kan iya wuni a layin kafin a zo kan ta.
Sai dai abin takaicin bayan haɗiye waɗannan ƙwayoyin wahalhalun suna ɗalewa kujerar mulki suka wofintar da mu. Yanzu ga shi a silar hakan na tsinci kaina a hannun hukuma ana shirin miƙa ni kotu. Abin da yake ƙara ɗaga mini hankali shi ne yanzu idan aka ce alƙali ya yanke mini hukuncin kisa wane hali tsohuwata za ta shiga? Shin za ta iya jura kuwa? Shin su waɗanda suka yi silar rayuwar ƙawata, tawa da ta sauran al'ummar da wannan matsalar ta yi sanadin su za a ɗauki mataki a kan su ne ko sai sai mun haɗu a ranar sakamako? Tabbas akwai sauran rina a kaba matuƙar aka bar su suka ci gaba da cin duniyar su da tsinke, za a ci gaba da ƙyanƙyashe ire-irenmu a cikin al'umma. Idan haka ne kenan za a ci gaba da yin kitso da kwarkwata.
Ƙarshe