INA HUJJAR TAKE: Labari Mai Sosa Zuciya, Fita Ta Tara
Page 9
Tunda Lantai ta kwasa da gudun tsiya bata zame ko ina ba, sai ƙauyensu Barbushe kai tsaye gidansu ta nufa tana ta haki.
Inna ce ta fara ganinta,don haka ita ce ta tarbeta da fara'arta domin jiya Isah Barbushe ya bayyana mata yadda yarinyar take da matsayi gunsa, don haka a kiyayi ɓacin ran yarinyar gida da waje .
Turus tayi don bata ga Barbushe ba, kuma taga alamar ɗakinsa a rufe yake ga alama.
"Inna wai yo ina Yayan nawa yake ? Cewar Lantai kamar zata fashe da kuka.
"Kada ki kuka ya je farauta, yace so yake ya samo maki nama mai yawa wanda za a soye maki shi ki ta ci a hankali."
Bakinta ta dargaje "Au yo to ai ban san hakan ba, bari na jira shi." Ta shige ɗakin da take tsammanin na Barbushe ne.
Sai ga Inna da kwanon sha cike da kunu da fanke sai ƙamshi yake ga alama ta ji haɗi yadda ya kamata.
Lantai ta gyara zama ta kama kallabinta ta ƙulle kudin aiken Inna Kande ta fara cin fanken tana surutunta.
"Yo Inna wai ke kikai fanken nan ? Gaskiya zan ba Inna Kande shawara itama ta dinga mana fanke akan shegen ƙosan da ake siyowa mai tsada."
Innarsu Barbushe ta dinga dariya tana cewa, "Gaskiya inaga dai fanken nan yayi maki daɗi ko a ƙara soya maki wani ne ɗiyata ?
Lantai ta cika baki da fanke ta ce, "Wannan ma ai ban iya cinye shi, har na rage in kaima Inna Kande da Musa su ci irin wanda yafi kowane daɗi."
Haka Lantai da Inna sukai ta surutu har wajen sha biyu na rana sai ga Barbushe da tawagarsa sun shigo sai uban kirari ake masa.
Da gudu Lantai ta isa gunsa tana masa sannu da dawowa.
Kallonta yayi yai murmushi ya dafa kanta yace, "Babu wanda ya ɓata maki rai dai ko Nuratu ? Kai ta ɗaga masa alamar e babu .
Ba ƙaramin naman dawa suka samo ba, ya ware ma kowa nashi ya kama aikin gyaran sauran Lantai na zaune tana ta zuba ma shi surutun tsiya,da yake bai cika magana ba sai dai wani lokacin yayi murmushi ko yace kin kyauta Nuratu.
Inna da sauran yaransa mamaki suke yadda yake ma yarinyar kowa yasan miskili ne na ƙarshe bai surutu bai son zama da mai surutu amma ita wannan yarinya kamar wadda aka yankawa bakin sai zuba take batasan ta dinga kintsawa ko dakatawa ba idan ta tsinke da zuba masa surutu.
Tas ya gyare naman ya dubi Lantai yace, "Nuratu ya za ai da naman nan soyawa ko dahuwar daddawa wane za ai maki da shi ?
Cike da farin ciki ta ce, "Yayana a ɗiba a soya sai a dafa wani."
Inna ya kalla yace, "Kin ji abin da ƙanwata ta ce, Inna a ɗaure ai hakan don Allah."
Ya wanke hannunsa ya ja hannun Lantai suka fita inda dabarsa take .
Duk wanda zai wuce idan Lantai ta kula da yana ta kallonta sai ta nemi fashewa da kuka ta ce ga wani can zai cinye ta da kallo ƙilama zaginta yake a ransa.
Sai Barbushe ya kira mutum ya dinga burma masa zagi sai ya bata haƙuri, wasu da dama sun sha mari akan Lantai ranar.
Ba Lantai ta nemi komawa gida ba sai bayan magriba sannan Barbushe ya kama hannunta da uban namanta suka nufi ƙauyensu Lantai ɗin.
Ko a can mutane sai kallon su suke suna mamakin me ya haɗa Lantai da wannan mugun mutum amma ba damar furtawa domin kowa na shakkar yarinyar da Kakarta a ƙauyen, amma duk da haka wasu sun ci alwashin kaima mai gari maganar .
Inna Kande kuwa ganin Lantai taƙi dawowa yasa ta nemi wani abincin ta fita da kanta ta je ta siyo goronta ta dawo tana ta masifar Hure mai ƙosai, sai tayi-tayi sai kuma ta koma faɗan yawon Lantai ya ishe ta bari Yayanta ya dawo ya san yadda zai da ita , ta gaji da yadda take ɗauko mata magana ita.
Ƙofar gidan Barbushe ya dakata don bai san tsohuwar ta sake ruɗewa irin na jiya.
"Ki gaida min tsohuwar sai na zo gaidata." Cewar Barbushe .
Musa na hangensu ya ɓoye don yasan halin Lantai ba ƙaramin aikinta bane ta kirashi gaban Barbushe ta nemi sawa ya kashe shi a banza.
To amma me ya haɗa Nuratu da Barbushe ?
Kowa tsoron Barbushe yake a ƙauyen ko ace a ƙauyukan dake wajajen to ita ya akai har ta saba da shi haka ? Lallai Nuratu ta musamman ce dole a kiyaye ta inba haka ba mutum ya ja ma kansa.
Yana ganinsu har ya bata ledojin dake hannunsa ya shafa kanta yana kallonta ta shige gidansu shi kuma ya juya fuska murtuk ya bi hanyar ƙauyensu.
Inna Kande kawai ji tai an faɗo jikinta, tasan aikin Lantai ne don haka ta kauda kai ta haɗe rai tayi kamar bata ganta ba.
Lantai tayi tsuru-tsuru ta manta ashe ita mai laifi ce don haka sai ta aje ledojin dake hannunta ta ce, "Nasan Hure ta zo ta kawo ƙarata ko ? To wallahi da kin ji abin da take ce maki da kin mamaki kuma wallahi da sai kin jinjina min abin da nayi mata.
Sai Kaka ta fara kallon Lantai don taji me Huren tai mata.
Lantai ta karkace kai ta ce, "Daga naje na ce taban ƙosai na murtala biyu shi ne tai banza da ni, da aka jima na sake cewa aban ƙosai Hure sai kawai ta dubeni a fusace ta ce, "Ke Lantai daman haka kike ai, Allah ya kiyashemu da riƙon Kaka yarinya kin koma sakarai kamar yadda Kakarki ta addabi mutane haka kema kin addabemu ?
Kowa yasan Kande bata da mutunci a ƙauyen nan kema kin ɗauki halinta kin yafa ma kanki to wallahi tun wuri garama ki san ba halin kirki take ɗora ki kai ba yarinya."
Inna Kande in taƙaice maki labari sai tasa yara suka fara min dariya, ni kuma daman zagin da take maki duk yaban haushi shi ne fa don na fara dukan yaran ta shigar musu tana cewa, "Ai ba don Allah kike siyen ƙosan ba don ƙyashi da hassada ne daman shi ne na zubar da kayan kawai na ruga ƙauyensu Yaya Isah abina."
Inna Kande ta fusata sosai da zancen ta kuwa miƙe ta yafa gyalenta ta ce, "To wallahi bata isa ba, ashe ita ce bata da gaskiya harta zo nan tana masifa ta amshi jaka huɗu da rabi hannun yaro ? To mu je ta ban kuɗin ko taga ruwan masifa bance ki saurara ma tukwane nta ba idan taƙi ba da kuɗin, shari'a daga nan har Maraya zuwa zan ."
Lantai ta fara murna, ta kwance naman da ta zo da shi, ta ce, "Inna Kande fara cin namanki sannan mu je , Innarsu Isah ta ce a kawo maki hada su fanke.
Ta ɗauki fanke uku ta dumtsi soyayyen naman ta ce, "Ki ci, bari na je naba Musa wannan Inna kina gamawa sai mu je gidan Huren." Ta fice da gudunta .
Musa na dawowa Sallah ya zauna ƙofar gidansu yanata mamakin Lantai daya gani da uban daba Barbushe sai ya hangota da gudu ta fito kai tsaye tayo inda yake.
Tana zuwa ta zauna kusa da shi tana nishi
"Musa ai nasan ka warke daman ba wata wahala kasha ba kawai don ka ci fanke da alale kaita kwanciya kana nishi cikin ɗaki."
Girgiza kanshi yayi yasan fiye da hakama zata iya cewa.
"Ga wannan ka ci gidansu Yaya Isah aka ban shi shi ne na kawo maku kai da Inna Kande kasan abin da yasa nake maka kyauta ?
"Sai kin faɗa Lantai ban sani ba."
Ta ɗauki nama guda ta saka baki ta ce, "Saboda kai ne ka koyamin karatu da rubutu, kai ne kasa na iya karanta littafin Jarumi Nasimat duk da naji haushin ranar farko baka gayamin sunan littafin daidai ba kace min wai INA HUJJAR TAKE bayan ba haka sunan littafin yake ba INA DA HUJJA shi ne sunan mahaifinsa."
Sosai abin ya ba shi mamaki yadda Lantai da gaske ta iya karanta littafi harma tana cin shi gyara lallai idan ta shiga secondry zata ba mutane mamaki .
Musa na san cin naman yana tsoron abin da zai je ya dawo, ta ce wai Yayanta Isah ya bata waye hakan ?
Ashe a fili yayi maganar ta kuwa fashe da dariya ta ce, "Kai Musa baka ganewa ni fa Barbushe nake nufi ai sunansa Isah ."
"Tab ai kuwa na gode Lantai ba zan ci ba, amma ke kam me ya kai ki gun wannan mugun ?
Ta ɓata fuska ta ce, "Ba mugu bane Allah kuwa yana da kirki sosai ."
"To ke Lantai baki gudun mai gari ya ji labarin kina tare da Barbushe ?
Kamar wata babba haka ta taɓe bakinta ta ce, "Wa ye kuma mai gari ? Ai na rantse da Allah wannan azumin sai ya gane kurensa domin ba zan bari gidanshi su sha daɗin sukari da geron da ake kawowa daga Maraya ba dole a raba kowa ya samu ko in ba shi mamaki."
"Ke Lantai kin manta shi ne mai gari yana iya korar mutum daga ƙauyen nan ?
Ta kwashe da dariya "Idan mutum bai da wayau ko ?
Kai dai Musa ka ci nama ka ci fanke ka jira sabon labarin abin da za mu je gidan Hure mai ƙosai mu rama rashin mutuncin da ta zo taima Inna Kande har gida akan ƙullu da man tuyar ƙosanta ."
"Ki ce daman shi ya sa da safe naji gidanku ana ta hayaniya anya kuwa Lantai idan Yayanki Hafiz ya dawo ba zai maki duka ba ? Kin fa tsokani mutane da yawa ƙauyen nan kin san kuma halinsa ."
"Kasan Allah yau sai mun je mun mata rashin kirki tunda bata san ƙaddara ba ita, ba sai tayi haƙuri ba tunda yau haka Allah ya nufa ba ? To wai ma waye ya biyata har jaka huɗu da rabi in ji Inna Kande ?
"Malam Muntasir dai naga ya shige gidan kafin zuwanta ."
"Na shiga uku ni Lantai kar dai ya gane ni ce na tura aka ɗauko littafin ?
Kallonta yake cike da al'ajabi wai Lantai kuwa kanta guda ? Anya ba aljanun karatun littafin Nasimat bane a kanta ba ? Kai zai ba Inna Kande shawara ayi mata ruƙiyya ko a samu sauƙin abin, komi dai ta ce Jarumi Nasimat ? Nan gaba wayasan abin da zatai kan Nasimat ɗin ?
Sanda zai dawo daga tunaninsa sai hango ta yayi ita da Inna Kanden sun nufi gidan Hure mai ƙosai ta aje masa fanken da naman kan dardumar da yake zaune.
Basu zame ko ina ba sai gidan Hure mai ƙosai, tana zaune tana tsintar wakenta tana waƙa sai jin maganar Kande tai bisa kanta.
"Hure maimata abin da kika ce ɗazun dana aiko Lantai siyen ƙosai wato ni ce sakarai ko ?
Hure tai banza ta ƙyale su taita tsintar wakenta.
Lantai ta ce, "Ai dayake bata da gaskiya kin ga taƙi kulaki har cewa tayi kin zama annoba a ƙauyen nan wai."
Hure dai bata tanka ba, domin ta amshe kuɗin ta harta ci riba don haka duk abin da za su ce ba zata bi ta kansu ba ita kam.
Inna Kande ta zuba masifar son ranta Hure bata tanka ba sai ta fara dube-duben inda zata sa Lantai tai mata ɓarna amma babu komi don haka ta sunkuya ta ɗauke waken taba Lantai ta ce mu je ai ba ubanta ya bada kuɗin ba wato an samu kuɗin banza dole ake siyen wake tun yanzu a gyara."
Hure dai bata tanka ba ita jira take ma su bar gidan ta isa gun mai gari domin ta kai ƙararsu tunda abin ya koma haka to zatai maganinsu domin dai mai garin bazawarinta ne don haka za su gane kurensu.
Haka su ka bar gidan suna ta surutansu da waken a hannunsu .
Basu jima ba aka aiko kiransu daga gidan mai gari, Inna Kande duk ta bi ta ruɗe Lantai kuwa ta kama ɗokin murna ta dubi Inna Kande ta ce ki zamanki gida bari na je ni ai ni ce na je siyen ƙosan ba ke ba."
Ita dai Inna Kande bata aminta da maganar Lantai ba, domin kowa yasan yadda mai garin yake bai da mutunci abu kaɗan sai yace zai kori mutum daga ƙauyen ko ya baka gonarshi yace ka noma ma shi duk abin da ka noma na shi ne ko kara bai bar maka.
Haka dai Inna Kande ta kama Lantai suka isa gidan mai garin.
Lantai kuwa na riƙe da littafinta cikin hijabinta ko Inna Kande bata san da shi ba har suka isa gidan mai garin.
Suna isa suka iske Hure mai ƙosai sai kukan munafurci take mai gari ya cika ya batse an taɓa masa Jawara.
Wajen yayi tsit ana jiran mai gari ya fara magana Lantai ta dubi fuskar kowa ta kwashe da dariya da ƙarfin gaske .
To ko me Lantai ta shirya aikatawa ? Gata dai riƙe da littafin Jarumi Nasimat a hannunta wanda ga alama da shi zatai wani ƙullin.
To mu haɗe page na gaba don jin me zai faru a gidan mai gari .
Haupha
managarciya