MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Biyar
_*MEE'AD*_
*- Page -* 11 & 12
Zaune suka tarar da Yaya Majeed bisa kan farar kujera hannun sa rike da littafi da 'alama karatu yake, da sallama suka isa wajensa kafin su zauna bisa grass carpet din dake shimfide a garden din, harara Yaya Majeed ya bisu dashi kafin yace sai yanzu kuka ga daman fitowa ? Cikin sarkewan harshe Mee'ad tace Yaya kayi hakuri na sameta tana wanka ne, a hasale Majeed yace to kuma sai nace kuzo ku zube a kasa ko ? A hanzarce suka tashi suna cewa sorry Yaya! Murmushi Majeed yayi kafin yace ku nemo abin zama now karku bata mana time i hope u understand ?" A tare suka amsa da yes! Tare suka nemo kujera suka zauna, Majeed ya fara musu lesson cike da kwarewa.
----------------------------------
Haka kwanaki, sati da watanni sukaita shudewa, bayan tsayin wannan lokacin Umman Majeed ta kara haifuwa ta haifi ya mace mai kama da ita sak! Anyi suna an gama lafiya ba'a dade da yin suna ba Mommyn Mee'ad ta haifi yan biyu duka maza 'ansha hidima sosai yara sun amshi sunan Abban Mommy da Abban Daddy, gasu masha Allah, yayin da ita kuma Umman Amal bata kara samun haifuwa ba tin daga kan Amal, Amal ya' daya tilo a wajen mahaifanta 2 wannan dalilin yasa Hajiya suwaiba ta shagwaba Amal sosai sai abinda take so ake mata, idan tace batason abu to baza kuma 'ayi wannan abinba duk muhimmancin da yake dashi kuma.
MAFARIN SOYAYYA! bayan kammala secondary skull din Majeed ya fara preparation din tafiya makaranta, Daddyn shi ya samar mashi da makaranta a kasar india domin kuma yasan babban burin dan nashi nason zama cikakken medical doctor kamar babanshi.
" Amal zaune take cikin dakinta bisa gado tana danna remote da 'alama kallo takeyi, Majeed ne ya turo kofar dakin da sallama a yatsine ta 'amsa masa sallaman tana cewa sannu da zuwa Yaya, murmushi Majeed yayi kafin yace Kanwata kallo kike yine ? Shiru Amal tayi kafin tace eh kallo nakeyi, murmushi ya karayi a karo na biyu kafin ya zauna kusa da ita ya kamo hannunta cike da kulawa ya tsareta da ido
managarciya