WATA UNGUWA: Fita Ta 33
BABI NA TALATIN DA UKU
"Jafaru ka yi masu bayanin cewa ba kai ba ne suke nema ko za su fahimci yarenka tunda sun kasa fahimtar nawa."
Wannan zancen na mahaifinsa ne ya katse masa zancen zucin da yake, ya ɗago a diririce ya fara kame-kame.
Ya kalli Irfan yana faɗar "Ka ga bawan Allah ɓatan kai ka yi, ni a rayuwata ma ban taɓa sanin wata mai irin wannan sunan ba."
Irfan ya kalle shi da kyau, sosai ya karanto rashin gaskiyar da ke zane a allon fuskarsa. Sai dai ganin yadda dattijon ya tashi hankalinsa ya saka shi yin murmurshi.
Har ya buɗi baki zai yi magana Abban Ja'afar ya ce "Yaro yanzu ka gamsu ko?"
Ya gyaɗa masa kai da cewa "Zan dai gamsu bayan na tsaurara bincike, akwai yiwuwar ba za mu sake haɗuwa ba sai a magirba."
Duk da ya fahimci cewa Abban bai fahimci inda kalamansa suka dosa ba, amma bai damu da tsayawa yi masa tarjarmarsu ba. A maimakon hakan ma kawai sai ya yi masa sallama, suka hau mota shi da yaronsa suka tafi.
Bayan tafiyarsu Abban ya shige ciki ya bar Ja'afar tsaye a wurin hankali a tashe yana bincike wasu sashe na ƙwaƙwalwarsa don nemo mafita.
Ya ji a ransa cewa wajibi ne ya bi fatawar kurege wajen ginawa kansa ƙofofi da yawa ta yadda zai iya ɓullewa ta wata ƙofar yayin da aka ritso shi ta ɗaya ƙofar. Da wannan tunanin ya shige gida don kai wa ummansa cefanenta.
A ɓangaren Irfan kuwa bayan ya bar wajen ya je ya shigar da ƙarar Ja'afar wurin jami'an tsaro. Duk yadda Ja'afar ya kai da zille-zille da wasan ɓuya tsakaninsa da Irfan da jami'an, ba a jima ba suka yi masa ƙofar rago suka kama shi, irin kamun da kuku yake yi wa kaza suka wuce da shi ofis ɗinsu.
Abba da bai taɓa kawowa cewa Jafarunsa zai aikata aiki irin wannan ba. Da ƙyar ƙwaƙwalwarsa ta iya ɗaukar bayanan jami'an na laifin ɗansa. Nan ma sai da ya ji a bakin Ja'afar ɗin sa'annan tosasshiyar ƙwaƙwalwarsa ta karɓi saƙon.
"Amma ka ban mamaki Jafaru, ban taɓa tunanin ko da a ce kai mayaudari ne zaka iya yaudararmu ba, ashe kallon kitse muke yi wa rogo. Shin ma wai a ina ka koyo waɗannan ɗabi'un banzan da aka siffanta ka da su?"
Jafsee dai ba baki sai kunne, sai hawayen nadama da yake yi nan fa mahaifinsa ya fice cike da ɓacin rai ya bar wurin, ba tare da ya sake kula shi ba.
Hankalin Ja'afar ne ya yi tashin gwauron zabi, tun da yake a rayuwa bai taɓa yin yaudarar da ya yi nadama ba sai akan ta Maheerah, ita ce mace ta farko da alhakinta ke neman raba shi da abin da ya kasance shi ne alfaharinsa wato albarkar iyaye.
Kodayake masu azanci sukan ce mutunci madara ne, idan ya zube ba ya kwasuwa.
A ɓangaren Sofi kuwa bayan gama makokin mutuwar yayarta sai ta nutsa cikin kogin tunanin hanyar da za ta bi ta karkato hankalin Irfan akanta. Allah Ya gani a irin wannan lokacin ba abin da take buƙata sama da aure, rayuwar barikanci ta daina burge ta, musamman da ta gano cewa ɓatan basira ne kawai wai roƙon Allah da goge. Don haka ta ajiye a ranta za ta tuba tun kafin ta yi fargar jaji irin na yayarta Hanifa.
Wata rana da misalin ƙarfe 10:30 na safe Irfan ya shigo ma'aikatarsu cikin shigar ƙananun kaya, ya tsuke ƙugu da bel, kyakkyawar doguwar fuskar nan tasa a washe, ya yi wa idanunsa ado da tabarau mai duhu. Kansa ba ya sanye da hula saboda haka zaka iya ganin yadda lallausar sumar kansa take sheƙi. Kallo ɗaya zaka yi masa ka fuskanci jinin Fulani ke yawo a jikinsa, duk da a zahirance zai fi yi maka kama da Bature ko kuma ba'indiye.
Cikin takunsa na nutsuwa ya ƙarasa ofishinsa bayan ya gama karɓar gaisuwa ga ƙananan ma'aikatan da ke ƙasansa.
Shigarsa ofishin ke da wuya ya ci burki saboda abin da idanunsa suka yi tozali da shi.
Da hanzari ya matsa gaban teburinsa, ya saka hannu ya ɗauki farar takardar da idanunsa suka yi tozali da ita. Ya ɗauki takardar kafin ya shiga jujjuyata a hannunsa, kafin ya kai ga buɗe takardar ya shiga kallon haɗaɗɗin kulolin da ke ajiye a gefe ɗaya na teburin.
'Me duk wannan ke nufi? Wa ya aiko da su?' zuciyarsa ta jefo masa waɗannan tambayoyin.
Ya tsaya jim, a take zuciyarsa ta shawarce shi da ya fara karanta takardar, mai yiwuwa ya samu amsar tambayoyinsa a ciki. Don haka Ya warware takardar ya fara karantawa a bayyane kamar haka;
Ina nema mana amincin mahalicci makaɗaicin bayi, wannan saƙo ne na musamman daga zuciyar da ke shirin mayar da martanin soyayyar da ake yi mata. Lokacin da kake karanta wannan saƙon na jima da yin nisa tare da ɓacewa ganinka. Sai dai na fahimci raunin da zuciyarka take da game da soyayyata, haka ina maka albishir cewa na kusa dawowa gare ka, cikin izinin Ubangiji zamu rayu da juna, zan cike maka guraben da suka rage a zuciyarka. Ga ɗayan saƙona nan a tare da wannan, ka ci wannan abincin don tabbatar mini kana maraba da dawowata a cikin rayuwarka.
Ina matuƙar sonka inuwata.
Saƙo daga abar ƙaunarka M.I
Gama karanta saƙon keda wuya yanayin farinciki ya yi dirar mikiya a saman kyakkyawar fuskarsa. Duk da cewa saƙon ya zo da wani irin salo kuma ga shi ba cikakken suna, amma hakan bai saka shi kasa fahimtar mai turo da saƙon ba, tunda ga kalmomin sunanta a ƙarshen saƙon.
Ya isa gaban teburinsa ya zauna tare da janyo kulolin ya fara buɗewa yana zabga murmurshi.
"Allah sarki! Baby Mahee annurin zuciyata, ashe baki manta da ni ba? Ina dakon ranar da zaki dawo gare ni."
Yana tsaka da wannan maganar ya yi tozali da lafiyayyen dambun shinkafa haɗin zogale, sai ƙamshi ke tashi. Ya janyo flate ɗaya ya zuba yana ta zabga murmurshi.
Cokali ɗaya ya yi, ya yi jim kamar wanda ke tunanin wani abin, sai kuma ya ajiye cokalin ya miƙe cikin hanzari ya isa gun sakatariyarsa yana tambayar ta wa ya kawo wannan saƙon. Sai ce masa ta yi, ranka ya daɗe wani matashi ne, kuma bai ba ni wata masaniya akansa ba sai cewa da ya yi shi ɗan aike ne kawai sunan jagorar aiken yana cikin kayan da aka aikon.
BALGORI
Zaune suke akan luntsuma-luntsuman kujerun da aka ƙawata falon da su, kowaccensu tana sanye da ɗamammun kaya riga da wando. Wacce ta fi ƙuruciya a cikinsu ce ta kalli ɗayar
"Sister zaki taimaka mini don aiwatar da plan ɗina?"
Wacce aka kira sister ta yi murmushi kada ki damu sis Mahee, me kike so a yi wa wannan gayen Ja'afar? Me ya aikata miki kike ƙoƙarin ganin bayansa? Me ya saka ba zaki iya yafe masa ba."
Mahee ta miƙe cike da taku irin na gogaggun bariki, ta yi taku biyar daga inda take sannan ta tsaya tana faɗar.
"Na san ban taɓa baki labarina ba, yanzun ma ba baki zan yi ba, sai dai ina son ki sani Jafsee bai cancanci yafiya ba."
Ta juyo tana fuskantar London girl sannan ta ɗora zancen.
"Jafsee ne mafarin lalacewar rayuwata, bayan gurbacewar rayuwar tawa sai kuma ya guje ni, a lokacin da ba ni da wata inuwa da zan fake sai ƙarƙashin lemarsa, ina ji ina gani ya janye lemarsa tare da ɗaba mini kausasan zantuka da ba za su taɓa shuɗewa a ma'adanar taskace abubuwa da ke kwanyata ba."
Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ɗora da faɗar "Na so Ja'afar fiye da tunaninki, na so shi fiye da ƙima ta yadda na iya yin biyayya ga umurninsa na bar umurnin mahaliccina, yau ga yar malam a rayuwar bariki duk silar wannan azzalumin bawa. Shin kina ganin ya cancanci yafiya?"
Sorfina ta girgiza kai tana tausayawa Mahee sannan ta ce "Tabbas Jafsee ya cancanci kowanne irin hukunci da kika yanke masa, yanzu me kike so a masa? Na yi miki alƙawarin haɗa hannu da ke a cikin wannan aikin ko da zan ƙare rayuwata a gidan kaso, saboda na tsani mayaudari, ni ma silar yaudarar nake fuskantar wannan rayuwar ƙasƙancin."
Ta matsa kusa da kunnen Sorfina ta raɗa mata wani abu, suka kwashe da dariya tare da tafawa.
"Cab! Jafsee karyarka ta ƙare."
Ummu Inteesar ce