MAMAYA:Labarin Soyayyar Mutum Da Aljan, Fita Ta Sha Daya

MAMAYA:Labarin Soyayyar Mutum Da Aljan, Fita Ta Sha Daya

 *Shafi na sha ɗaya*

 Kwance yake gaba ɗaya ya rasa me ke damunsa, bai da sauran tunani ko kuzari inba dukan yarinyar yayi ba, ya rasa abin da yasa yake jin tsanar yarinyar aduk sanda yayi ido biyu da ita.

 "Anya kuwa gaskiya kake faɗi?(Furucin wata zuciyarsa kenan).

 Ito idan tantagaryan gaskiya zai bayyana to yarinyar itace babbar damuwarsa matsalaisa a rayuwarsa.

 Ba ƙaramin tashin hankali da firgita yarinyar ke jefa zuciyarsa ba, saboda ba dan ya kasance jan wuya ba, mai jan hali jan ƙwazo ba to da yanzu yarinyar ta gana ɗaiɗaita rayuwarsa a kan titin Allah ta'ala.

 To sauƙin shima ta ɓoye da bayyane mugun jan wuya ne mai dakama maza gumba a hannu yasa ya sha gabanta yake ramuwar gayya gareta, tunda ya gane sirrinta da babu wanda ya gane take wahal dashi da firgita shi da tsoma rayuwarsa cikin halin ƙaƙanikayi. To amma tun randa Allah ya taimake sa ya sake gano wani sirrin nata sai ya fara samun sauƙin lamarinta da iya shegenta.

 Malam Aminu kenan (Ɗan-bahago)kwance yana tunanin abin da babu wanda ya taɓa gayamawa ko da wasa.

 Yana cikin wannan tunanin yaji alamar tafiya cikin ɗakinsa, wuf yayi ya rufe idanunsa dan bai fatar ya kalleta, yasan dai itace domin ba makawa kullum sai ta zo ta razana razanar zuciyarsa, cike da tsoro ya fara karanto addu'ar neman tsari daga sharrinta.

 Wata mahaukaciyar dariya ta bushe da ita, ta dubesa da ƙwala-ƙwalan idanuwanta masu zubar da baƙin ruwa mai wani mugun wari tace..

 "Malam kana ban dariya aduk lokacin da kalleka, domin kai ɗin kaci sunanka ɗan-bahagon saboda komi naka a haguncen yake tafiya."

 Jikinsa ya fara kyarma, ko da wasa bai alamar buɗe idonsa ba da zummar ganinta ba.

 Taci gaba da magana, ɗakin na amsa amo da kuwwa tamkar aradu ce ke faɗowa cikinsa.

"Kana ƙara karyamin karfin gwiwa duk sanda ka  hukunta ni a islamiyya domin kasan sirrina na biyu ko? To ka san cewa ina gab da ɗaukar matakan da zasu iya samun kai a komata cikin sauƙi da sauƙaƙawa Malam."

 Banda salati babu abin da yake a zuciyarsa da tunanin yanda gobe zai amfani da sirri na biyu da ya gano daga ɗalibai tasa ya hukunta ta .

 "Kai Malam !

A razane ya buɗe ido ya sauke su a kanta.

Ya salam! Ganinta yayi a wata irin ƙazamar halitta bakinta wage yana hango wasu tarin tsutsoci sai motsi suke cikin bakinta, ga wasu ƙwala-ƙwalan idanuwa masu ban tsoro sai wurwura mai su take , hannuwanta sak na ƙwarangwal ne ga wani baƙin hayaƙi da ke fita daga bakinta mai warin tsiya.

 Cikin kyarma ya dube ta yace "Don Allah Bilkisu kiyi haƙuri ki rabu da ni ki daina bibiyar rayuwata haka nan dan Allah kina tsorata ni da yawa."

 Wata mahaukaciyar dariya ta kwashe da ita, kafin ta turbune fuska tace...

 "Malam kayi kuskure da ka bankaɗo sirrina dan haka naci alwashin bibiyar rayuwarka har ƙarshen rayuwar ka cikin tsananin tsoratar da kai da firgita ka ainun, sai kai katarin burkito sirrina na biyu wanda shine samun sauƙin ka gareni."

 "Bilkisu ki taimaka ki ƙyaleni haka ba zan sake shiga sabgarki ba kwata-kwata na rantse maki."

 Wata mayyar shewa tayi mai saka dodon kunnuwa rushewa tace.

 "Ba zan taɓa sassauta ma ba Malam har ƙarshen rayuwar ka."

 Tana kaiwa nan ta fasa uban ihun da yasa shi doɗe kunnuwansa ya sulale sume a kan katifarsa.

 "Wayyo Malam!

 "Na bani na lalace zo kaga abin da nake gani ni Huraira."

 Matar da Inna ta watsama ruwa ta sake kallon Innar rai ɓace idanunta na yoyon jini, tace cikin muryai fusata.

"Huraira dan tsabar tujara da masifa ina zaune abuna ina tunanin hukuncin da zan yanke ma masoyina yayi mun kishiya shine ke kuma zaki d

zuba min ruwa dan tsabar iskanci da raini? Tana magana bakinta na kumfa kamar an kaɗa sabulu haka yake fitowa alamar tana cikin tsananin ɓacin rai da bala'i mai firgitarwa.

 Ai Inna sai ta ɗora hannu akai ta fara zunduma ihu tana kiran, "Malam kazo nace karta sabauta ni a banza."

 Maganar da ita yi ce ta sake tunzura mummunar Aljanar dan haka bata tsaya ɓata lokaci ba sai jin ƙarar mari kake tas, tas, tas, a fuskar Inna Huraira.

 Ai kuwa Inna ta ɗimauce ta ƙara ƙaimi wajen kiran Malam da ihunta.

 Ganin marukan sunƙi ƙarewa yasa Inna fara addu'ar korai fusatattun Aljanu da karfin tsiya.....

 "Bisimillah walhamdu anci zalina da fusata, kuzo mala'ikun Allah ku kawo ɗaukin sama da fusatattu walau mutum walau aljan iyayen mutunta." Ai tana kaiwa karshen addu'ar ta ta taji wani uban kulli a gadon bayanta wanda yasata kwallama Bilkisu kira ba shiri ta zube gun a sume.

 Dan bala'i sai Aljanar ta ɗebo ruwa ta watsa mata, sai ga Inna kwance ƙasa tana nishi kamar wadda zata haihu.

 Tana daga kwancen taga Aljanar ta yi girgiza sai ga wasu hirɗa-hirɗan kawunan macizai sun bayyana daga kowane kusurwa na jikinta, cike da tsoro Inna ta fara yunƙurin tashi ta ruga ɗakinta amma tashin ya gagara.

 Wata uwar tsawa Aljanar ta daka mata, tace a fusace "maza ki tashi kimun rawa da waƙa saboda in samu sauƙin damuwar dake cin zuciyata na kishin masoyina da nake."

 Idanuwa waje ta dubi Aljanar, wace irin rawa kuma ita yanzu zata yi ? Ai ko zamanin da can da sukai ƴan matanci kowa yasan Huraira bata rawa a dandali saboda bata itaba balle waƙa, ita dai barta da tarin masifarta kawai sai zafin tallar goro da kokon safe kawai da dare ta kai gyaɗa talla dandali.

 Tana cikin wannan tunanin taji saukar wani dundun a gadon bayanta, ai ba shiri sai ga Inna tsaye tana zare idanuwa tana ƙyabƙyabtasu kamar wadda taima sarki ƙarya.

 Ba zato taji wani kiɗa na tashi irin na ƴan borin nan ai kuwa Inna ta dage iyakar karfinta ta fara tiƙar rawa tana juyi tsakar gidan, Aljanar na tsaye gabanta fuska ba alamar fara'a balle ta saka ran ganin dariyarta.

 Inna ansha rawa kala daban-daban wadda tunda uwar data haifeta bata taɓa yin irinta ba , ga Aljanar ga alama rawar Innar sake fusata zuciyarta take yima .

 Inna kuwa numfashinta ya fara alamar shiɗewa saboda tsabar rawar da ke tiƙa ba ƙauƙautawa.

 Ganin zata mace kai tsaye yasata saurin bajewa ƙasa tana maida numfashi abin da yasa Aljanar hawayen takaici kenan ta nuna Inna da yatsanta dake ci da wuta tace..

" Idan zamu shekara dubu ɗari biyar dake kina mun rawa indai ban dariya ba to bazaki dakata ba, dan haka tun kafin na fara fincike maki akaifar yatsanki ki miƙe tsaye kici gaba da yimun rawa irinta India tana burgeni duk sanda suke shooting na waƙoƙin su da rawa ina gun Ina kallo dan haka maza ki fara mun irin tasu."

 To fa ya ya Inna Huraira zata yi rawar India da waƙar su kenan?

 Shin wane sirrine har biyu Malam Aminu ya bankaɗo na Bilkisu ?

 Ya ya soyayyar Nasir da Bilkisu zata kaya ?

 *Taku ce Haupha*