HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta 23

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta 23
HAƊIN ALLAH
 
   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 
 
 
 
*Sosai nake jin farin cikin yadda littafin nan ya samu karɓuwa ga mutane maza da mata kowa bibiyar labarin nan  yake yana tofa albarkacin bakinsa, ga addu'a da kuke min da iyayena gaskiya abin na mun daɗi sai ince Allah Ya bar zumunci da ƙauna*.
 
Haupha.
 
 
 
        Page 23
 
 
 
Na sulale kusa da Hajjo na zauna, idanuwa na son ganin waye ya rasu amma sun kasa gane waye, don haka na buɗe baki da ƙyar na dafa Hajjo nace, "Hajjo don Allah waye ya rasu ne? Ba wanda ya gayamin wanda ya rasu Ni, ance dai na taho Kano anyi rasuwa amma ban san waye ya rasu ba, ina Uncle Salim ban ganshi ba ko a waje?"  Hajjo ta miƙe tsaye ta ja hannuna muka shiga ɗakin Uncle Salim na zauna ina son jin waye ya rasu. Hajjo ta dube ni sosai tace, "Jiddah duk wani Bawa da kika sani yana tare da jarabawa mai daɗi ko akasinta, sannan duk yadda kake son mutum baka kai Ubangiji son shi ba, Jiddah Allah Ya amshi ran Uncle Salim ɗazun nan ya tashi lafiya lau har ya fita ya dawo ya kawo min kaya da takalma ya ce min naki ne domin yanzu kina makaranta kuma dole irin makarantar taku sai da sutura, ya aje kayan ya fita da aka kira sallah ya ce min bari na je sallah na dawo na baki wani labari, to dawowar da bai ba kenan yana sujjada Allah ya amshi ransa."
 
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un!
Uncle Salim fa kika ce Hajjo? Ya zai min haka Ni Jiddah? Hajjo idan na rasa Uncle Salim na rasa duk sauran gatana kenan... Kuka ya ƙwace min sosai, Hajjo ta kama hannuna, "Share hawayenki Jiddah mu je kiyi sallama da Uncle Salim ɗinki, nace a jira ki zo ku yi bankwana, duk da an jima da haɗa shi, amma ban san a kai shi kafin ki zo, nasan idan ba gawar kika gani ba tabbas ba za ki amince da rasuwar shi ba za ki dinga ganin tamkar zai dawo, tamkar wani waje ya je ne." Haka muka nufi ɗakin dana zauna a lokacin da nayi zaman gidan. 
 
Allahu Akbar! Uncle Salim na shimfiɗe ɗakin sai ƙamshin turarensa yake.
Cikin rawar jiki na tsugunna gaban gawarsa, cike da ƙyarmar baki na fara yin magana, maganar da nasan ba zai amsa min ba, maganar da nasan yana ji na amma amsar ce ba zan ji ba, maganar da nasan ita ce ta ƙarshe da zan yi a gabansa.
 
"Uncle Salim! Allah Ya jiƙanka ya gafarta maka, Yasa ka huta. Ina addu'ar Allah Yasa halayenka na kirki su bika Uncle Salim, tabbas ka tafi ka barni a gaɓar da nake cike da neman taimako, nasan Allah ne gatana amma ta hanyar ka nake samun ɗauki.
Uncle Salim nayi rashinka!
Tabbas Uncle Salim nayi rashinka!
Nayi rashinka Uncle Salim a lokacin da Deeni ya sake Ni, ya yi min saki biyu daidai lokacin da na zo garin nan cikin gidan nan naga saƙonsa, amma kuma Uncle Salim waye ka gwada min a mafarkina Yau? Tabbas nayi mafarkinka kuma ka gwada min wani kace na bishi zai zame min madadinka amma ina zan ganshi? Uncle Salim ban san shi ba, shi ɗin ya Sanni ne?" 
 
Hajjo ko ɗauka tai na sauka layi sai ta kamani muka fice daga ɗakin, muna fita aka zo ina ji ina gani aka ɗauki gawar Uncle Salim aka tafi da shi waje ai mai sallah a kai shi maƙwabcinsa na gaskiya.
 
Sulalewa nayi dafe da kaina ban sake sanin abin da ke faruwa ba sai bayan wani dogon lokaci. Hajjo na tare da ni tana ta tofa min addu'a na tashi a firgice ina waige-waigen neman inda zan ga Uncle Salim domin sai naji tamkar yana kirana a kunne na.
 
Hajjo ta rungume Ni ta cigaba da tofa min addu'a, sai kuma barci ya kwashe Ni. A barcin na sake ganin Uncle Salim ya dube ni ya yi murmushi ya ce, "Jiddah kar ki yi baƙin ciki, ko da yaushe ki kasance cikin farin ciki, tabbas Allah zai saka maki ga duk wanda ya cuce ki sannan ki dage da karatunki ki riƙe yaranki amma kar ki bar wannan ya sake nuna min mutumin wancan karon ya juya baya ban ga fuskarsa ba. Na buɗe baki da nufin tambayar Uncle Salim sai naga ya juya ya tafi yana cewa Jiddah ki yi haƙuri nayi tafiya mai nisan gaske Ni...
"Ke Jiddah tashi haka nan ba kyau barcin yamma, mugayen mafarki ake yi ko ma a tashi ba lafiya." Cewar Hajjo kenan. Ina buɗe ido na sauke su kan yarana suna zaune sun zagaye Ni Haidar hawaye yake su Afnah sun yi zugudum da su. Sai tausansu ya kamani ko da yaushe mu kai waya da Uncle Salim sai ya ce min Jiddah ki kula da yaranki naki ne ba na kowa ba, ki yi haƙuri ki jajirce masu, ki zama Uwa ta gari a gare su ,kar da ki bari su yi kukan rashin Uwa idan har kina da numfashi Jiddah. Allah Sarki Uncle Salim Yau ya tafi ya barni da yarana a tsaka mai wuya, domin ban san ina zan nufa ba tunda Deeni ya sake Ni,ga yarana ban san wa zai taimake Ni gun riƙe su ba sam. Janyo su nayi jikina na fashe da kuka, kamar jira suke suma suka fashe da kuka. Akai ta lallashina ana cewa na sa yara kuka, to ya zan lokacin yin kukan mu ne ya zo, mun yi marar dalili ma ina ga mai dalilin ya samu? Mutane nata tambayar wacece ni,ya nake da shi ne saboda kowa ya fahimci yadda mutuwar tai matuƙar girgiza ni na fita hayyacina na zama abar tausayi lokaci guda.
 
                   BAYAN SATI 
 
 
Bayan sati da rasuwar Uncle Salim kowa ya kama shirin tafiya garinsu na nesa dana kusa, Mama daman kwana uku ta yi ta tafi da Haidar tabar min su Afnah.
Da dare Hajjo ta dube ni tace, "Jiddah naji kina cewa Deeni ya sake ki, yaushe?" Na ciro wayata na nuna mata saƙon daya turomin. Ta karanta ta yi jim sai ta yi ajiyar zuciya tace, "Jiddah ki yi haƙuri haka Allah Ya nufa amma shawarar da zan baki ita ce, wannan karon kin girma kin mallaki hankalin kanki don haka ki koma gidan mahaifinki da zama da yaranki duk rintsi kar da ki sake ki ce ɓacin rai zai sa ki bar gidan, domin nan ne gatanki so nake Babanki ya saba da ke ya ɗauke ki matsayin ɗiya haka yaranki ya kallesu matsayin jikokin sa. Jiddah kin ga karatu kike ban so ko da wasa ki dakatar da karatunki don haka ki koma gidanku da zama idan ya so yaranki sai ki barsu nan ki tafi makarantar hakan zai fi maki natsuwa da kwanciyar hankali Jiddah, ba wai don ban iya riƙe ki ba da yaranki ba nace hakan sai don ina son ki sani DA UBA AKE ADO BA UWA BA.  Insha Allah watarana sai komai ya zama tarihi a gareki Jiddah.
 
Washegari ina zaune Zainab ta kirani a waya na je naga wani abu, kamar kar da na fita don tunda na zo ban sake bi ko ta hanyar zauren gidan ba. Hajjo ce tace na je mana ba daɗi mutum yai ta binka kana guje ma shi. Hakan yasa na tashi na ɗauki hijabina na fice. Baƙin ƙofar shiga gidan Zainab na ganshi Yah Mustapha ne, yana zaune ya yi shiru ga alama tunani yake yi nasan bai wuce tunanin abokinsa Uncle Salim domin nasan tare su ke daman can kuma ƴan uwane ta ɓangaren Babansu Uncle Salim ɗin, na dakata na dube shi sai na ɗan saki fuskata nace, "Ina kwana... Ya muka ji da ƙarin haƙuri? Allah Ya jiƙansa Ya gafarta masa Yasa ya huta."
 
Kallona yake kawai ya kasa amsa  gaisuwar da nake mai, nasan ba komai bane yasa hakan illa yadda suke tare da juna tun suna yara dole ne mutuwar ta dake shi, don ma shi Uncle Salim ɗin bai aure ba, shi kau ya yi aure har sau biyu ban sani ba koma ya yi na uku yanzu.
Ganin ya kasa tankawa na wuce shi ina goge hawayen tuna Uncle Salim da nayi.
 
Ko da na shiga cikin gidan tunanin Uncle Salim ya tsaya min a raina sosai duk yadda na so na kauda shi a raina amma ya ƙi kauduwa saboda Uncle Salim shi ne gatana gaba da baya.
 
Zainab tai ta tsokana ta da ban dariya dole na ware na biye mata muna ta tuna baya har na ware na koma cikin kwanciyar hankali.
 
Mustapha kau tunda Jiddah ta fito ya tsira mata ido yana kallonta, yarinyar tana kwance a cikin zuciyarsa tun tana yarinya ƙarama, ko ya manta ta yana ganinta yake jin sabuwar ƙaunarta na yawo cikin jikinsa.  Amma abin mamaki sai ga shi Yau ta zo har gabansa tai mai magana amma ya kasa bata amsa, domin ji ya yi tamkar ba shi ba, ji ya yi ya tafi wata duniyar ta daban.
Tsoronsa guda kada ace tana da aure yarinyar, hakan kawai ke sashi cikin zullumi ya ji ya sake shiga cikin mugun damuwa fiye da wadda yake cikinta.
Yana ji a jikinsa ita ce warakar damuwarsa, ita ce zata kawo mai sauyi a rayuwarsa tabbas yana ji a jikinsa ita ce macen da yake nema ruwa a jallo ita ce wadda zata sashi farin ciki ta kauda mai damuwa idan yana cikinta.
 
Amma taya kenan zai same ta ? Yarinyar na da abubuwan da yake so ba ƙarya ita ce daidai da zaɓin sa amma bai sani ba ko tana da ra'ayi irin nasa? Shi kam yana son macen wayayya , wadda zata nuna mai so da kulawa ta aje kunya da girman kai ta nuna mai ƙauna, ta ɗauke shi tamkar yaron goge, ta tsaya kan lamurranshi, ta dinga tausaya mai ta dinga ba shi duk wata amanarta kamar yadda zai bata tashi amanar, matar da zasu rayu cikin farin ciki su dinga rayuwa mai cike da inganci wadda ke cike da girmama juna yake buƙata.
 
Ya sha mafarkin yana tare da wata yarinya matsayin matarsa suna rayuwa cike da nishaɗi, ya dawo gida daga aiki ta rugo ta tarbe shi, ko da yaushe cikin faɗa mai kyawawan kalamai take masu kwantar da zuciya, bai taɓa ganin fuskarta ba amma Yau da ya ji muryar Jiddah sai ya tabbatar da cewa ita ce a mafarkinsa.
"Ya Allah ka zaɓa min mafi alheri kasa mu zama HAƊIN ALLAH Ni da Jiddah don girman zatinka." 
 
Haka Mustapha ya dinga tunani yana saƙawa da kwancewa, ya rasa wa zai tambaya ya gaya mai tana da aure ko bata da aure, yana zaune yaga sun fito daga gidan dake jikin gidansa sun shiga gidansa. Wani sanyi ya ji daya ga ta shiga gidansa sai ya yi sauri ya bisu shima ya faɗa ɗakinsa, ya buɗe taga yana kallon tsakar gidan ko Allah zai sa ya dinga hango ko da wulgin yarinyar ne ya ji dama-dama.
 
Zainab ta dubi Maryam tace "Kin ganta nan wai tafiya za tai gobe don Allah ba ta bari ba sai an yi arba'in ba sai ta tafi ba?" Jiddah tai murmushi tana kallon tsakar gidan kamar mai nazarin wani abu a ranta sai kuma tace, "Mama ta tafi da Haidar kada yai ta mata kuka ne." 
Maryam ta saka baki tace, "To ba ya saba da ita ba? Ai ba zai damu ba tunda yana ganinki ya amince ya bita."
 
Ni dai ban wani jin daɗin zaman gidan saboda duk sai naji tamkar wani na kallona, haka ma dai tsarin zaman gidan bai min ba, don haka na tashi tsam nace ma Zainab zan koma gida sai na sake fitowa.
Ta tashi ita ma ta biyoni tace mu je tare ba za ki tafi ki barni ba muna firar arziƙi.
 
Yana kallonsu suka fice daga gidan ya yi ajiyar zuciya yana jin wani nauyi na sauka daga cikin zuciyarsa yana ƙasa sai ya ji wasai tamkar bai da damuwar komai a gidansa.
 
Ko da muka koma gidan Zainab kasa natsuwa nai kawai sai na dinga tunano mafarkina da wannan bawan Allah wanda duk lokacin da zan mafarkinsa yana nuna min ƙauna yana lallashina yana sunsunar jikina tamkar wasu indiyawa. Ganin Zainab ba zata barni nayi tunanin dake yawo a zuciyata ba na tashi nace mata zan je gida na dawo wanka zan yi, ba don ta so ba haka na fice ina cewa yanzu zan dawo na samu na kubce na fice.
 
Yana inda na barshi ɗazun bai tashi ba kenan? Haka na raya a raina na raɓa ta gefensa na wuce ina jin sansanyar ƙamshin turarensa, ina son ƙamshi hakan yasa na jima zauren hajjo ina shaƙar ƙamshin turaren yana ratsa zuciyata sosai nake jin daɗin sa.
 
Tunda suka fito ya sake fitowa yana addu'ar Allah Yasa ya sake ganinta shi dai birge shi kawai take yarinyar idan ya ganta yana samun natsuwa sosai a zuciyarsa. "Jiddah!!! Ya ja sunanta a cikin bakinsa yana jin farin ciki na ratsa shi kawai na ambatar sunan da ya yi.
 
Jiddah kuwa abin duniya ya ishe ta, so take ta koma gidan mahaifinta kamar yadda Hajjo ta bata shawara, so take ta ga mahaifinta tai mai wasu tambayoyin da ke yawo a zuciyarta tun tana Lagos har yanzu ta kasa sanin amsar su haka ta kasa daina tunaninsu, don haka take son ta ganta idonta idonshi don kawai tai mai tambayar ko da ba zai bata amsa ba tana son yasan tasan tambayoyin kuma daga lokacin ne zata ba kanta amsa idan bai bata amsar tambayoyinta ba.
 
 
Sai da akai arba'in sannan Mama ta zo muka shirya tare don komawa gida, sannan hutun semester ya ƙare don haka Hajjo taban kuɗin da zan siyayyar makaranta, har mun haɗa kaya nace bari na je nayi ma Zainab sallama.
Bata gidanta tana gidan Maryam don haka can na iske ta na gaya mata yanzu za mu tafi sai wani karon idan Allah Ya nufa.
 
Yana ɗakinsa ya ji sallamarta don haka ya dawo saitin da zai dinga kallonta, yarinyar tamkar wata ƴar budurwa haka yake ganinta a idanunsa komai nata ya yi cif daidai ra'ayinsa.
 
Waje ya fita ganin tana niyyar fita so yake ya ga tafiyarsu tunda ya ji tace tafiya za su yi yanzu.
 
Haka kau akai ta fito da Zainab suka wuce ta gabansa yasan ba lallai bane idan ta ganshi suka faɗa gidan Zainab basu jima ba suka fito tare suka shiga gidan Hajjo.
 
Sai ya ji tamkar ya bita ya tambaye ta tana da aure ko bata da aure? 
Sai ya ji tamkar ya tambayi Zainab ƙawar matarsa kuma maƙwabciyarta idan yarinyar na da aure. Sai kuma ya fasa ba wai don gudun tsogumi ko wani abu ba sai don gudun kada ace mai tana da aure kawai ne ba zai tambayar ba.
 
Yana cikin tunanin yaga sun fito sun tafi yasan ta tafi kenan sai bayan wani dogon lokacin kafin kuma su sake ganin juna.
 
Wayarsa tai ƙara yana ɗagawa ta fara halin nata kamar yadda ta saba na magana kai tsaye ba wani kulawa balle taushi a Muryar, abin da tace ne yasa ya ji tamkar zuciyarsa zata fito don fargaba da ɓacin rai.  "Na gaya ma kai gaggawar sakina kafin nayi maka abin da baka zata ba wallahi."   
Kashe wayar kawai ya yi ba tare da yace ko ƙala ba.
 
 
Mu haɗu a kashi na gaba.
Taku a kullum Haupha!!!!