DUHU DA HASKE: Fita Ta 20
DUHU DA HASKE
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 20*
~Gidan marayu aka kaita, a hankali ta fito da akwatin tana ja tana kallon babban gidan, sallama tayi ta samu me gadi tace "nazo ne na zauna anan"
yace "ke marainiya ce?"
gyaɗa kai tayi sannan tace "sabida banida inda zanje shiyasa na zaɓi na zauna anan, amma ni mamana tana raye nazo ne sabida na nemi aiki nayi karatu amma anan ɗin shine zaifi min kwanciyan hankali harma nayi bacci babu wani fargaba"
yace "to shikenan bari muje ayi miki register"
shiga ciki sukayi tana tafiya a hankali har ya kaita wani office, sukace "suna?"
a hankali tace "ameesha Ibrahim"
da sunan gari da sauran tambayoyin suka mata, ɗaki suka nuna mata sannan suka bata dokokin zama a gidan, jan akwatin take a hankali tana kallon ɗakin, ba laifi yana da kyau, mutanen gidan suna zaune wasu suna aikin gabansu, sallama tayi musu, kaɗan ne suka amsa ta durkusa ta gaishesu suka amsa a takaice, ɗakin da aka bata ta shiga da sallama, wata kyakkyawar budurwa ce ta amsa tareda tashi daga kan katifan da take, murmushi tayi mata ganin akwati a hanunta tace "sannu da zuwa"
kallon cikin ɗakin tayi babu komai sai varanda daya farfashe ga sanyi sai katifa a kasa, a nitse tace "yawwa"
komawa tayi ta kwanta ameesha kuwa ta aje akwatin ta zauna a bakin katifan tayi shiru, gani tayi yarinyar tana kuka, cikin sanyin murya tace "kiyi hakuri ki daina kuka"
share hawaye tayi tace "to"
ameesha tace "ya sunanki?"
cikin sanyin murya tace "sunana hanan"
"ni kuma ameesha"
tace "kin jima da zama anan?"
tace "eh tunda na gama primary a kaduna kakata ta rasu na dawo nan da zama"
tace "Allah sarki"
shiru sukayi kowa da tunanin da yake, ameesha tunawa take da Imran wanda yake kuka yana cewa kada ta tafi, share hawaye tayi, hanan tace "kince na daina kuka ke kuka kinayi"
daina kukan tayi hanan tace "bari na baki biscuit kici"
bata tayi, tace "a,a bana jin yunwa"
tace "a,a kici dan Allah"
ci tayi, tace "kiyi wanka saiki huta"
tace "to"
wanka tayi ta kwanta tana bacci, cikin bacci ta fara juyi tana girgiza kai a mugun firgice ta tashi da ihu tace "no"
hanan wacce take zaune a gefenta tana karatu ta aje takaddan tace "mummunan mafarki kikayi kiyi addu'a"
zufan goshinta ta share sannan tayi addu'a ta zauna tana kallon hanan ɗin a ranta tace "insha Allah nayi alkawarin mantawa da komai da kowa, ba zan kara tuna kowa a cikinsu ba, na rabu da komai daya shafi can anan zan fara sabon rayuwata, zansa a raina kowa nawa ya mutu ni kaɗai na rage a duniya ina fatan Allah ya kula da mama da Imran da kuma fahad.
Abdool yana zaune a falo daram a kasa kan tiles yayi shiru ya ɗaura kanshi a jikin sofa, Ammi ta fito tana tura wheelchair ɗinta, kallonshi ta tsaya tana yi idonta yana cika da hawaye, remote ɗin ta danna yayi kara "ɗit ɗit"
a hankali ya ɗago kanshi ya kalleta, murmushi tayi mishi, tashi yayi yana sanye da wando marar tsayi sosai da riga fari yana showing kirjinshi, ya ɗan faɗa idonshi ya koma ciki ciki, hancinshi ya kara tsayi yayinda lips nashi suka koma jajur, a gabanta ya durkusa yana kallonta yace "ammi akwai abinda kike buƙata?"
girgiza kai tayi, murmushi yayi mata kyawawan hakoranshi suka bayyana, cikin sanyin murya yace "to shikenan na maidaki ɗakinki?"
girgiza kai tayi tana kallonshi, a hankali ya zauna daram a gabanta, kanshi ya ɗaura akan cinyanta yayi shiru yana kallon kofa, itama shiru tayi, hanunta tasa a kanshi tana shafawa, hawaye masu zafi suna wanke mishi fuska cikin raunin murya yace "na rasa yadda zanyi ammi"
shafa kanshi take tana hawaye, inama ace zata iya magana data faɗa mishi gaskiya, da ta faɗa mishi yaje ya kula da kaninshi da Ameesha data faɗa mishi halin ƴarta, amma bata magana a kullum tana ganin rayuwar ɗaci da yake yi duk dan ya taimaki manal"
ɗago kanshi yayi jin hawayenta yana sauka a jikinshi, share hawaye yayi da sauri ya share mata nata yace "kiyi hakuri na saki kuka"
a hankali ya fara turata zuwa cikin tsakiyan falon, tv ya kunna mata sannan ya juya zai tafi, hanunshi ta rike ta girgiza mishi kai alaman kada ya tafi, zama yayi akan sofa yana kallonta tana kallon tv, manal a hankali take tafiya itama ta rame ta zama fara sosai, guntun wando ne a jikinta da armless, ta saki gashinta ya sauko bayanta, tayi kyau sosai da fuskanta daya koma fayau, tun daga nesa yake kallonta tana mishi kyakkyawan murmushi, batada rama sam a cike take ɓulɓul kuma batada jiki sosai, duk inda mace ta kai ga kyau idan ta kalli manal saita raina kanta, gashi ko tafiya take cike da class take tafiya, a hankali ta karaso, akan cinyarshi ta zauna ta raba kafanta ta sashi a tsakiyanta, rungume kanshi tayi cikin sanyin murya tace "ka rame ka fita a hayyacinka"
a hankali ya ɗan tureta yace "Ammi na nan sauka"
kankameshi tayi murya ƙasa ƙasa ta yadda shi kaɗai zai jita tace "so nake ka samu nutsuwa dani Abdool duk ka fita a hayyacinka bakaga yadda ka rame bane?"
yace "to sauka mu tafi ɗaki"
yatsa tasa tana shafa lip nashi na kasa a hankali ta fara kai bakinta zata tsotsa janyewa yayi yace "ammi na nan mu tafi ɗaki"
girgiza kai tayi tana kara shigewa jikinshi tace "kiss kawai"
barinta yayi tana kissing nashi, a hankali take shafa jininshi, tace "i miss you"
ammi tura wheelchair tayi ta bar falon, yana ganin ta tafi ya fara ɓalle boturan gaban riganta ganin baya ɓalluwa da sauri ya yage rigan itama cikin creazeness ta cire rigan dake jikinshi cikin sauri sauri suke romancing juna, man nema yake yaga ya samu nutsuwa ko zai dawo hankalinshi, zame wandon yayi kasa tare da nashi, a hankali ya lumshe ido lokacin daya shiga jikinta daga zaunen ya kura mata idanunshi da suka kara kankancewa, itama kallonshi take ganin bai fara komai ba ta fara tashi a hankali tana komawa, runtse ido yayi yana jin wani irin pleasure, a yadda ya fahimci kanshi shi mabuƙaci ne amma tashin hankali yasa baya kula hakan sosai, ganin bata mishi yadda yake so ya rike waist nata yana cigaba da kallonta da tsumammun idanunshi, a ranta tace "Abdool yafi kama da mazannan wanda ake kira da model, yawanci sunfi zama samarin celebrity ko kuma suyi dating yaran shugaban kasa, duk wani abinda mace take so a jikin namiji Abdool yana dashi ×3, gashinshi yanayin jikinshi muryanshi magananshi kyawunshi da komai da komai oh my god he's hot
ganin tana kallonshi ya rufe ido yana cigaba da abinda yake, tun tana dauriya har ta fara numfashin gajiya, a hankali ta fara zamewa zata sauka, riketa yayi gam cikin muryanshi dake cike da damuwa da kuma yace "please"
kallonshi tayi yana bata tausayi amma babu yadda ta iya sanshi take kamar zata mutu, saida yayi good 2hours kafin ta kai bakinta kunnenshi a wahale tace "my abdool please am tired"
a hankali muryanshi baya fita sosai yace "saura kaɗan"
kuka ta fara, abinda bayaso yaji tana yi kenan shine kuka, da kyar ya iya control na kanshi a kankameta yana sauke numfashi da sauri sauri, shiru tayi a jikinshi shima yayi shiru yana lumshe ido, a hankali ya tashi yana jan trouzer ɗinshi sama, itama mayar mata yayi ya rike hanunta zuwa cikin ɗakinsu, toilet ya shiga sukayi wanka kana ya fito ya shimfiɗa sallaya yayi sallan mangrib da Isha daya wuce shi, itama salla tayi, tashi yayi yace "zan kawo mana abinci"
abincin ya kawo tana zaune akan gado ta lankwashe kafa kanta a kasa hawaye masu zafi suna wanke mata fuska, zama yayi a kusa da ita yace "baby kukan me kike?"
tace "ba kuka nake ba"
yace "okay kin san me?"
tace "no"
yace "zamu fara zuwa company"
tace "bazan iya zuwa ba bazan iya ba na bar maka komai"
yace "shikenan kiyi zamanki a gida ki kula da ammi ni zan fara zuwa"
tace "to"
abincin ya bata, itama ta fara bashi, a hankali yake ci sabida kada tayi mishi kuka.
mama da safe ta tashi domin yin alwala taga babu ameesha, dubawa ta fara taga bata nan, tashin fahad tayi tace "banga ameesha ba"
da sauri ya tashi yace "ina taje?"
saida suka idar da salla suka fara dubata, duk inda suka san tana zuwa sunje basu ganta ba, cikin tashin hankali mama ta shiga ɗaki domin ɗauko hijabi, idonta ya sauƙa akan takaddan dake saman gadon, kallo tayi jikinta yana rawa ta ɗauka ta fara karantawa, tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un na shiga uku, fahad!!! fahad!!! fahad!!!"
shigowa yayi yace "na'am mama"
jikinta yana rawa tace "ka gani?"
karɓa yayi yana karantawa
_salam alaikum mama da kanina fahad ina baku hakuri ku yafemin akan abinda nayi, bazan iya cigaba da zama a wannan garin ba, zuciyata tana zafi ina rokonku dan Allah ku rinƙa kaiwa Imran abinci kullum kuje ku dubashi ga mashin ɗina na bar maka kana zuwa dashi ni nayi nesa daku kuyi hakuri, bazan kara dawowa ba ina muku fatan alkhairi_
hawaye yake sauka a idon fahad takaddan ya rungume cikin kuka yace "Anty ameesha ina kikaje kika bar kaninki?"
mama ta rikeshi suna kuka sosai, saida suka gaji da kuka kafin mama taje ta fara girki, saida ta gama ta zuba a flask ta kawowa fahad nashi, yaki cin nashi ya ɗau na Imran ɗin ya tafi yana share hawaye, mashin ɗinta ya kalla ya hau yana kuka ya fita, prison yaje suka sashi ɗana abincin kafin suka barshi ya shiga, Imran yana zaune ya haɗa kai da gwiwa yayi shiru, sallama yayi ya zauna a gefenshi, Imran bai ɗago ba yace "ina ameesha?"
muryanshi yana rawa yace "ta tafi"
ɗago kai yayi yace "kenan ta barni ni kaɗai?"
fahad kuka ya fara, shima Imran kukan yake yi da kyar suka lallashi kansu, abincin ya mika mishi yace "kaci"
girgiza kai yayi yace "dan Allah ka barni da yunwa nama fi jin daɗin zama anan ka barni da yunwan na mutu, koda na fita ba zanji daɗin rayuwa ba"
fahad yace "tun yanzu zaka fara karya alkawarin unty ameesha? ko ka manta tace kaci abinci?"
ya lallasheshi da kyar yaci, yace "nayi alkawarin kula da kai"
yace "na gode"
akace ya fito lokaci yayi, fita yayi ya hau mashin ɗin, gidansu manal ya nufa zuciyanshi kamar wuta, a kofan gidan ya tsaya ya sauko daga mashin ɗin ya ɗibo duwatsu dayawa, tun daga kofa ya fara harbi yana cewa "Abdool? ka fito"
abdool dake shirin fita yaji ana kiranshi kuma muryan fahad ne, me gadi yace "yaro ka daina harbi"
yace "baba matsa zanci gaba da harbi har sai ya fito"
kara harbin yayi yaje kofan yana bubbugawa da karfi yana cewa "Abdool Abdool"
da driver ɗin gidan da megadi da sauran masu aiki suka rirrikeshi, kwacewa yake yana cewa "Abdool"
cikin farin shadda ya fito yayi kyau sosai sajenshi a kwance luf sai kamshi yake saide ya rame sosai, ganin an rirrike fahad ya tsaya yana kallonshi, fahad yana ganinshi ya fara kwacewa yana cewa "wato kana nan kana rayuwa cikin jin daɗi bayan ka tarwatsa namu jin daɗin? kasa Imran yana zaune a gidan yari mugu kawai banso ace na taɓa saninka ba a rayuwa"
Abdool juya baya yayi,
fita sukeyi dashi yace "wallahi in dai anty ameesha bata dawo ba saina kashe ka, kasa yayata ta tafi ta barmu, ta gudu ta bar garinnan ka karya mata zuciya duk yadda take sonka ka kasa ganewa saida soyayyan ya dawo zazzafan kiyayya dan nasan a yanzu babu wanda ameesha ta taɓa tsana kamar kai, har zobe ta kai maka sabida kasa mata kuyi aure, ta nemi aiki sabida rayuwarmu yayi kyau, shine ka karya mata zuciya mugu mara imani"
cak ya tsaya tsaban yadda jikinshi yake rawa ya kasa buɗe motan, har Imran ya hau mashin ya tafi bai iya koda kara motsi ba, manal dake tsaye akan stair tana kallonsu, sanye take da wani arnen bakin riga, kafanta dogon takalmi ne kamar kullum, hanunta rike da glass cup cike da wine tana sipping a hankali, tayi bala'in yin kyau a cikin rigan me hanu ɗaya, ɗayan hanunta a waje, gani tayi ya kasa shiga motan a hankali ya fara dawowa, aje cup ɗin tayi a kasa yana karasowa zai shiga ɗaki taje gabanshi kamar bata san komai ba, ta shafa sajenshi dake kara mishi kyau, wani irin hug tayi mishi bata manna jikinta duka a nashi ba amma tayi mishi hug me kyau, fuskanta ta fara shafawa a sajenshi, bakinta ta kai kunnenshi cikin wani irin voice da yasa yaji tsikan jikinshi yana tashi tace "ka fasa tafiyan ne? ka dawo sabida na zauna da kai kamar yadda na rokeka na rinƙa jinka a jikina a koda yaushe?"
a hankali ya lumshe ido, hamdala yayi a ranshi da bataji abinda ya faru ba, zameta yayi daga jikinshi ya ɗaura hanunshi a waist nata ya matso da ita kusa dashi sosai yace "na dawo na kara kallon kyakkyawar matata me kama da larabawa"
murmushi tayi, yaja dogon karan hancinta yace "me zaki bani?"
cikin kasa da murya da yanayin farin ciki da take ciki tace "me kake so?"
a hankali ya raɗa mata a kunne yace "ke"
tace "bakayi breakfast ba ka fara yin breakfast first"
ya kara janyota jikinshi yana shinshina wuyanta dake kamshi yayi mata neck kiss ta lumshe ido, bakinshi ya kai kunnenta yace "i want to have you for breakfast"
tureshi ta fara yace "please"
tana dariyanta da yake kara mata kyau tace "let's go in"
yace "no"
yayi maganan yana rufe kofan falon, waro manyan idanunta tayi tace "me kake nufi?"
cikin erotic voice nashi yace "anan nakeso"
yayi maganan yana mannata da jikin bango, ɗan waro idanu tayi tace "my Abdool kowa fa zai iya shigowa falo"
kasa yayi da murya yace "zan kashe wuta, my crazy wife"
cikin crazeness nata tace "okay my naughty husband"
kashe wutan yayi ɗakin yayi duhu ya mannata da jikin bangon a hankali yake hawaye yana rabata da arnen dogon rigan dake jikinta, bata iya ganin hawayenshi hakan ne dama yasa ya kashe wutan, bakinta ya haɗa da nashi yana cigaba da hawaye masu zafi, a yadda yayi lissafi saura mata shekara huɗu da wata huɗu a duniya.
a kullum sai fahad ya kaiwa Imran abinci baya yadda yaci sai kuka, tunda ameesha ta tafi rayuwa tayi musu ɗaci, da mama da fahad da Imran suna rayuwa kamar matattu, duk ranan da yaje saiya tambayeshi ameesha ta dawo? cewa yake "a,a bata dawo ba"
ya ɓaci sosai kasumba ya cika mishi fuska yayi baƙi kamar ba Imran kyakkyawa ba, shi kanshi fahad ya ɓaci duk sun zama shiru shiru.
***********************
*bayan shekara huɗu*
a yau ne kamar yadda alkali ya faɗa zasu shiga kotu domin ayi shari'a na ƙarshe daga wannan sai a yankewa Imran hukunci dai dai da abinda ya aikata, tun safe fahad yake zaune a wajen yayi tagumi ya gama ramewa yayi baƙi ƙirin da alama ma da yunwa yake zaune, Imran aka fito dashi yana sanye da kayan prisoners kayan yayi baƙi a jikinshi ga wanda bai sanshi sosai ba idan ya ganshi ba zaice shine Imran ba, fuskanshi yayi buzu buzu da gashi, kanshi ma gashi ne ya cika har ya sauka wuyanshi, hanunshi da kafanshi ɗaure da kaca sun sashi a gaba suna biye dashi a baya, yana ganin fahad yace "ina mama?"
bakinshi ya fara rawa ya kasa magana, hawaye masu zafi suka zubo yace "tunda taje neman lauya kwana uku da suka wuce wanda zai kareka, ta tafi da kuɗi masu yawa domin ta biya lauya ta siyar da gidanmu har yau bata dawo ba, ni kaɗai nake kwana a gidan mama bata dawo ba..."
ya karasa maganan yana kuka, shiru Imran yayi suka rikeshi suna tafiya dashi, shima fahad ya tashi yana binsu a baya har aka fita dashi aka sashi a mota zuwa kotu, fahad ya hau mashin ya bisu a baya,
man yana gyarawa ammi hijabinta tana zaune akan wheelchair yayi murmushi ya rike fuskanta da hanu biyu yace "yau za'a yankewa wanda ya saki a wannan halin hukunci kinji ammi?"
tana iya ganin yadda yake jin ɗaci a kasan ranshi, tana iya ganin tashin hankalin da yake ɓoyewa a kullum, hawaye masu zafi suka fara wanke mata fuska inama tanada baki da tace mishi ya ɗauketa su gudu su bar gidannan, data faɗa mishi gaskiya, tun daga kan mutuwan dady har zuwa yanzu ta gama gane komai akan manal saide bakinta ba zai iya magana ba, kallonta yayi duk yadda yaso ya daure ya kasa kifa kanshi yayi a cinyarta ya fashe da wani ɗan marayan kuka, a hankali take shafa bayanshi alaman lallashi, karan takalmin manal yasashi tashi da sauri ya share hawayen sannan ya sharewa ammi, cikin rashin dariya na asalinta manal ta fito sanye da abaya baƙi tasa siririn mayafi a kanta, idonta ta rufe da baƙin glass sannan tasa flat shoe hanunta rike da waya, kallon Abdool tayi wanda yake kallonta yana murmushi, karasowa tayi ta zuba hannayenta akan wuyanshi tana kallon cikin idonshi bayan ta ɗaga glass ɗin tasa a saman mayafin tace "my abdool na yafewa Imran ina ganin mu janye wannan case ɗin sabida yana cikin wani hali"
waya ta ɗaga zatayi kira ya rike wayan, yace "idan kin yafe ammi bata yafe ba, ki duba kiga ba zata kara tafiya ba har karshen rayuwarta, duk wanda ya saka a wannan halin dolene a kullum sai kaji ka tsaneshi a cikin ranka, koda kin yafe dole a yiwa ammi adalci"
tace "nasan ammi zata ya..."
yatsanta yasa a bakinta hakan yasa tayi shiru, cikin son kawar da maganan yace "sha"
tsotsan yatsan tayi tana kallonshi, murmushi yayi yace "to ya isa"
tsayawa tayi ya cire yatsan daga bakinta yace "haka nakeso a kullum idan na faɗa miki abu kiji"
har cikin ranshi yana jin daɗin yadda idan ya faɗa mata abu bata musu zatabi umarninshi yasan tana yin hakan ne sabida tsananin sonshi da take, a hankali tace "my abdool ina sanka zan iya mutuwa a kanka"
idonta cike da hawaye tayi maganan, yana kokarin fara tura ammi yace "na sani, manal soyayyan da kikemin yayi yawa ya kamata ki ɗan rage"
tsayawa tayi tace "kalleni my abdool"
kallonta yayi, ta rufe ido tace "na rantse da ubangijin daya halicci rana kuma ya halicci wata, ubangijin da yayi mutum kuma yayi aljani, ubangijin da yake bawa wanda yaso ya kuma hana wanda yaso, na rantse da ubangijin Annabi muhammad s.a.w bazan daina sonka ko kuma na rage sonka ba till the end of time"
da sauri yazo ya rike ta yace "dan Allah manal ki daina wannan maganan"
zatayi magana yace "karfe ɗaya da minti goma yanzu karfe biyu za'a shiga kotu"
tura ammi yayi har zuwa wajen mota, shi ya ɗagata ya sata a motan sannan ya shiga itama manal ta shiga, driving zai fara ammi ta ɗan taɓashi, juyowa yayi yace "na'am ammi akwai abinda kikeso ne?"
kallonshi takeyi sosai da alama akwai abinda take so ta faɗa mishi, yace "kina buƙatan wani abu?"
ta cikin madubi ta kalli manal wacce take aika mata kallo da idanunta masu rikita mutum, a hankali ta girgiza kai alaman babu, killer smile manal tayi, yaja motan suka tafi.
a cikin kotu sukayi parking da kanshi ya cire ammi yana turata ita kuma manal ta rufe idonta da glass ɗin suka jera tare suna tafiya, a daidai lokacin aka shigo da Imran cikin kotun, shima fahad ya karaso ya aje mashin nashi a gefe, yana gaba suna biye dashi an ɗaure hanunshi an kwance na kafanshi domin yayi tafiya, ido huɗu sukayi da man wanda hanunshi yake kan keken ammi, ɗauke kai yayi yaci gaba da kallon gabanshi, fahad kallo ɗaya ya yiwa su man ya wuce yana binsu Imran, man jikinshi ya fara rawa ganin yadda Imran ya koma, da kuma fahad kuma baiga mama ba baiga ameesha ba, yasan ita bata nan tunda ta tafi yau shekara huɗu kenan bai kara ganinta koda a hanya bane, ammi ta ɗaura hanunta akan nashi cikin tausayi, murmushi yayi mata ya turata suka shiga ciki, dashi da manal da ammi suna gaba gaba, fahad yana nesa dasu shima layin gaba ya sunkuyar da kanshi yaki kallon Imran dake tsaye a gaban kotu, yau kam kotu har yafi na koda yaushe cika, fal yake da mutane har wasu suna tsaye akan kafarsu, alkali ya shigo kowa ya tashi domin bashi girma saida ya zauna kowa ya zauna akayi shiru, alkali yace "ina lauyan wanda yake kara da wanda ake kara"
lauyan manal ne ya tashi yace "sunana barrister fadeel lauyan wanda yake kara"
komawa yayi ya zauna, Alkali yace "ina lauyan wanda ake kara?"
shiru babu amsa, ya kara maimaitawa, har yanzu shiru babu amsa, alkali yace "za'a fara gudanar da shari'a yaune karshe yau za'a yanke hukunci, barrister fadeel bismilla"
fitowa barrister fadeel yayi ya tsaya a gaban Imran ya fara mishi tambayoyi amsawa yake a hankali cikin karaya, barrister fadeel yace "ina neman kotu nan me alfarma ta taimaka ta yiwa waɗanda aka zalinta adalci tunda ya fara karaya da alama zai amsa laifinshi"
alkali ya kalli Imran wanda ya sunkuyar da kai yace "malam Imran shin ka amsa laifin da ake tuhumanka dashi?"
a hankali yace "eh na amsa"
a firgice Abdool ya kalleshi jin abinda ya faɗa, Alkali ya kara cewa "shin ka amsa laifin da ake zarginka dashi?"
yace "kwarai na amsa"
yace "kaine ka yiwa matar yayanka fyaɗe kayi niyan kashe mahaifiyarta har ta samu rauni me muni?"
a hankali yace "eh nine"
kanshi a kasa yake amsawa, alkali yace "ɗago kai ka kalli kotu ka faɗa laifinka a gaban kowa"
a hankali ya ɗago kai ya kalli duk mutanen ciki kafin yace "na amsa laifina na zuwa gidan yayana wanda muke uwa ɗaya uba ɗaya na yiwa matarshi fyaɗe sannan da zan gudu mahaifiyarta tana kokarin hanani gudun na tureta daga stair ta faɗi taji ciwo"
duk kotu yayi shiru harda alkali, sai bayan wasu mintuna alkali ya kalli mutanen kotu yace "bayan Imran ya amsa laifukan daya aikata da kanshi kotu ta yanke mishi hukuncin kisa, sabida yayi niyan yin kisa sannan ya aikata mummunan laifi wato fyaɗe"
alkali ya kalli Imran wanda kanshi a kasa yace "ka amince da hukuncin da akayi maka? ka yadda kotu bata zalinceka ba?"
jijjiga kai yayi yace "kwarai na amince"
fahad wanda babu abinda yake sai kuka ya kasa daurewa ya ɗaga murya yace "dan girman Allah alkali kuyi hakuri wallahi bashi ya aikata ba, na rantse da Allah bashi bane"
manal kanta a kasa man yaki yadda ya kalli inda Imran yake, ammi banda hawaye babu abinda take yi, alkali yace "yaro shifa da bakinshi ya amsa laifinshi kuma ya maimaita a gaban kotu, idan kana ganin anyi mishi rashin adalci yanada lauya ne?"
shiru yayi, alkali yace "yanada lauya?"
"Eh yana dashi"
muryan ameesha ne ya karaɗe cikin kotun, daga bakin kofa take tsaye, duk suka juyo atare harda manal, murmushi ne ya suɓucewa Imran tareda hawaye, fahad ganin ameesha tsaye a bakin kofa cikin uniform na lauya baƙi da hula akanta, tasa bakin takalmi me tsayi tayi parking na tulin gashinta tasa ribbon baƙi kafin ta ɗaura hulan lawyer a sama, tayi wani irin masifan kyau ta kara zama fara fatarta yana wani glowing ta zama kamar balarabiya, cikin kukan ya fara dariya har yanzu hawaye bai tsaya ba, saide babu murmushi akan fuskanta ko kaɗan, tayi wani kwarjini na musamman, cikin takun nutsuwa da class kamar ba ameesha me sauri ba, ta fara takowa duk mutanen kotu suna kallonta, manal idanunta a waje take kallon ameesha, saida ta karaso a gaban Imran ta tsaya sannan tace "sunana barrister Ameeesha Ibrahim lauya wacce zata kare wanda ake kara"
a hankali taje gaban alkali ta mika mishi takaddunta tace "ina rokon kotu tamin alfarma sabida late ɗin da nayi banzo da wuri ba, amma inada kwakkwaran uzuri"
alkali ya duba takaddunta yaga eh tabbas successful lawyer ce sannan lawyer ce me kokari domin da first class ta fito, gyaɗa kai yayi, tace "idan ba damuwa zanso a maida wannan case ɗin baya sannan idan har case ɗin baimin ba zan ɗaukaka kara"
alkali duba da matsayin da take dashi a fannin karatu yace "na baki dama wannan case ya zama sabo"
kallon mutanen kotu yayi sannan yace "lauyan wanda suke kara zai iya fitowa sannan an baku dama kowane challenge fa zaku kare wanda kuke karewa ku yishi amma banda zagi banda cin mutunci"
cikin girmamawa ta karɓi takaddunta daga hanun alkalli ta rungume a kirjinta, dr fadeel ya fito,
Alkali yace abasu kur'ani suyi rantsuwa zasu faɗi gaskiya, dr fadeel yayi sabon rantsuwa sannan ameesha ta karbi kur'ani tace "na rantse da ubangijin daya aiko mala'ika jibril a cikin kogo ya cewa Annabi muhammad s.a.w kayi karatu da sunan ubangijinka wanda ya halicceka (ikra bismi rabbikallazi khalaka)
ba zan kare me laifi ba, mika kur'ani tayi cikin girmamawa alkali ya karɓa ya aje, kallon manal tayi tace "zanso abani dama na kira wacce ta kawo kara domin akwai wasu tambayoyi da nakeso nayi mata"
alkali yace "an baki dama, wacce tayi kara bismilla"
a hankali manal ta tashi daga inda take taje ta tsaya tana kallon kotu, zuciyanta yana dukan ɗari ɗari.
cikin confidence Ameesha ta tako zuwa gabanta tace "manal umar maidawa"
kallonta manal tayi tace "manal Abdulrahman lamiɗo kamar kin manta inada aure"
murmushi tayi me sauti sannan tace "sanin darajan mahaifi yasa na kiraki da sunan mahaifinki, ko dai bakisan darajan naki bane?
sannan ko a addini babu inda akace ki cire sunan mahaifi kisa sunan miji ko dai bakije islamiya bane? okay na manta mahaifinki ya mutu oh sorry an kashe shi ina nufin wata ta tura motarta ta bige motarshi tana gani yana ɗaga hanu a cikin motar yana neman taimako bata taimaka mishi ba har saida ya zama toka, sannan tabi wacce suke tare a hotel ta sata rataye kanta sabida kada ma zargi ya hau kanta"
kallonta manal tayi jikinta ya fara rawa, itama ameesha kallonta take tana wani irin smiling da alama a shirye tazo.
ameesha tace "koda shike ba case nashi muke yi ba kawai ina tayaki alhinin mutuwan mahaifinki ne"
kallon mutanen kotu tayi sannan ta kara maida hankali kan manal tace "manal zanso na faɗawa kotu wani abinda kika taɓa yinshi lokacin da kike yarinya hakan zaisa kowa ya fahimci abinda zaki iya aikatawa da wanda ba zaki iya ba, a lokacin da kike school kin taɓa kwace teddy ɗin wata yarinya me suna hanan kika kona a cewarki duk abinda kikeso daki rasashi gara kowa ya rasa"
da mugun mamaki manal ta kalleta aina tasan wannan labarin?"
murmushi tayi tace "kin girma da wannan abin a ranki hakan yasa a lokacin da kika haɗu da abdool ko kuma ince kika kwace Abdool kinga cewar mahaifiyarshi da kaninshi basa sanki hakan yasa kika fara kulla sharruka har saida kika janye Abdool zuwa gidanku, sannan bayan kunje gidanku bakyaso kowa ya raɓeshi kika yiwa kaninshi sharri, ta yaya akayi Imran yasan inda makullin ɗakinki yake?"
tana mata wani irin kallo tace "makullin yana jikin kofa"
girgiza kai tayi tace "gidanku basa barin makulli a jikin kofa kuma kece kika hana hakan, idan baki yadda ba inada shaida"
buɗe murya tayi tace "Atika"
wata me aikin gidansu manal me suna Atika ce ta shigo, ameesha ta nuna mata waje ta tsaya tace "sannunki"
a hankali tace "yawwa"
tace "zaki iya gayawa kotu wacece ke?"
tace "sunana Atika nice me kula da shara da goge na gidansu manal"
tace "sannu malam Atika shin zaki iya faɗa mana yaushe rabon da abar makulli a jikin kofan gidansu manal?"
tace "gaskiya ya jima domin manal ta hana hakan"
murmushi tayi tace "mun gode zaki iya tafiya"
fita tayi, ameesha tace "to manal ta yaya akayi Imran yaga makulli shida ba shiga gidan yake ba har ya rufe ɗaki?"
tayi shiru, ameesha tace "tambaya na gaba, shin Imran ne ya yaga rigan jikinki ko kece kika yaga nashi?"
tana huci kanta a kasa tace "shine"
girgiza kai ameesha tayi tace "no kece kika yaga riganshi dogon domin yagun ta gaba ne, da ace fyaɗe zaiyi miki da ta baya zaki yaga riganshi domin ceton kanki, amma ta gaba ya nuna kinason abinda zai yi miki"
dunƙule hanu manal tayi, ameesha tace "sai tambaya ta gaba shin minti nawa yayi yana amfani dake?"
a fusace ta kalleta tace "taya za'ayi nasan minti nawa ne?"
tace "ta yadda akayi kikasan fyaɗe ya miki, a ganina duk macen da miji ya kusanceta dole tasan daɗewanshi ko akasin haka a yadda nasan Imran ko s*x bai sani ba, baisan yadda ake yinshi ba ta yaya wanda baisan komai ba akan abu zai aikata?"
manal tace "ta yaya kikasan bai sani ba?"
tace "na tashi tare dashi tun muna yara kanana, Imran tun yana ɗan kankanin yaro nake tare dashi ki sani duk wanda na zauna dashi nasan abinda zai iya kuma nasan wanda ba zai iya ba, sabida ni ba dabba bace me manta komai"
manal tace "to waye dabba?"
ameesha tace "duk me manta Alkhairi dabba ne kamar mijinki"
a fusace manal ta fito daga inda take tsaye ta shaƙe wuyan ameesha, murmushi ameesha tayi dama haka takeso shiyasa tayi hakan sabida tanaso asalin halin manal ya bayyana a gaban alkali sannan hakan zaisa a ɗaga kara zuwa gaba daga nan zatayi duk yadda zatayi ta fitar da Imran daga wannan zargin, rike manal aka fara, man ne yazo da gudu yana janta, manal tace "saina kasheki"
murmushi tayi tace "dama kin iya kisa ne?"
da kyar man ya janyeta, tsayawa tayi da faɗan, idonta ya gani yana rufewa atake ta fara aman jini a cikin kotun, zaro ido man yayi yana kallonta yace "manal manal open your eye's manal"
alkali yace "an ɗaga wannan case ɗin zuwa nan da sati ɗaya"
duk mutane suka fara fita, man ya kalli ameesha wacce Imran yazo da gudu ya kankameta yana kuka, itama hawaye take, cikin kuka yace "baki karya alkawari ba kinzo banyi zaton zaki dawo ba Anty ameesha nayi kewarki i miss you so much, I miss you..." kuka yake yi sosai
tana rungume dashi tace "to me na kuka ba gashi na dawo ba? sai butulu ne yake manta baya Imran koda me na zama a rayuwa ba zan taɓa mantawa daku ba"
police sukazo suna janyeshi zasu tafi dashi yace "Ameesha zasu koma dani wajen babu daɗi babu komai sai sauro da sanyi, nasan zaki fitar dani"
juya baya tayi da zasu fita dashi tace "Imran nayi alkawarin kota wuya kota daɗi saina fitar da kai"
man ya kwantar da manal wacce idonta ya juya ta bushe a wajen, cikin wani irin zafin rai ya fuskanci ameesha ya nunata da yatsa yace "meesha"
tana kallon cikin idonshi tazo dab dashi tana wani irin smiling na rainin hankali tace "barrister Ameesha Ibrahim zakace"
yace "idan wani abu ya samu manal"
cikin bushewan zuciya tace "me zakayi? kasheni zakayi? ko nima sharri zakumin a kulleni kamar yadda kuka yiwa kaninka? to amma Inaso ka sani malam Abdulrahman ameesha tafi ƙarfin ɗauri, da wannan maganan da tada jijiyan wuya da kake da matarka ka ɗauka ka kai asibiti watakila yau ta cika shekara huɗu daya rage mata a duniya ko ka manta shekara huɗu dr yace zatayi? ko dai har yanzu ƙwaƙwalwan naka irin na dabbobi ne baka daina mantuwa ba?"
cikin wani irin yanayi yake kallonta yace "idan wani abu ya sameta ba zan kyaleki ba"
tace "idan ka fasa Abdulrahman"
hannu ya ɗaga zai mareta sai kuma ya dunƙule hanun yana huci yana kallonta, murmushin gefen baki tayi tana kallon hanunshi tace "zanso kayi wannan kuskuren koda sau ɗaya ne na marina"
bai kara kulata ba ya juya manal ya ɗaga tana tari yasa hanu a bayan wheelchair ɗin ammi wacce idanunta akan ameesha tana murmushi ya fara tafiya dasu, fahad yace "anty ameesha mama yau kwana uku kenan da ɓatanta babu ita bata kara dawowa ba"
a ruɗe tace "ina taje?"
yace "tunda taje nemawa Imran lauya har yau babu ita, kuma ta siyar da gidanmu"
shafa kanshi tayi tace "karka damu"
man yana jinsu har suka fita, asibiti ya kai manal aka kaita emergency, zama yayi kusa da ammi yayi shiru, jim kaɗan aka fito da ita, shi ya kaita gadon asibitin ya kwantar da ita, juyawa yayi zai fita manal ta buɗe ido, murmushi tayi a hankali ta rike hanunshi, juyowa yayi ya zauna akan kujera yana facing nata, lumshe ido tayi ta buɗe kana cikin muryanta da baya fita sosai tace "ina sanka my abdool"
shiru yayi ya sunkuyar da kai, a hankali tace "ko sau ɗaya ban taɓa ji kace kana sona ba, yau zanso naji wannan kalman daga bakinka"
a hankali ya kalleta, tausayi take bashi, a yadda dr ya faɗa zata mutu nan bada jimawa ba, kuma duk wani sign ɗin da dr ya faɗa na cutan idan ya gama cin karfinta duk ya bayyana domin yaga idanunta suna canja kala suna komawa ɗan jaja, hanunta ya rike a cikin nashi yana murzawa, ta kalli karamin bakinshi tace "ka faɗamin"
a hankali ya matso sosai ya manna fuskanshi a nata yace "i love you manal"
murmushi tayi zatayi magana jini ya fara fita daga bakinta, da sauri ya ɗauko tissue ya goge mata, hanunta cikin nashi tace "kiss"
murmushi tayi dan ya lura tana son kiss koda yaushe idan suna zaune bata rabo dayi mishi, bakinshi ya manna a kumatunta, a hankali ya zame ya fara manna mata kiss a duk inda yaci karo dashi a jikinta, hanunta da babu drip ɗin tasa a gashin kanshi, matso dashi tayi kusa da ita ta manna bakinta akan nashi tayi shiru tana kallon cikin idonshi shima yana kallonta, zamewa tayi a hankali cikin kunnenshi muryanta kasa tace "i love you too my abdool"
hanun fahad ta rike tana tafiya a hankali kamar babu jini a jikinta, ba abinda yake sai kallonta, shekara huɗu kenan baisa yayarshi a ido ba sai yau, gani yayi ta zama kamar ba ita ba, tayi kyau amma yanzu babu fara'a kamar da, wani zazzafan mota ta buɗe mishi tace "shiga muje"
buɗe baki yayi zaiyi magana
cikin rashin fara'a tace "shiga mana"
shiga yayi itama ta shiga, da mugun gudu ta bar kotun, gani yayi ta nufi hanyan wani gida ba nasu ba, sunyi tafiya da nisa kafin suka isa wani unguwa me kyawun gaske, a kofan wani maƙeƙen tsararren gate suka tsaya tana hon, buɗe musu gate ɗin akayi da mamaki fahad yake kallonta yana kallon gidan, a babban compound ɗin tayi parking me ɗauke da wasu zafafan motoci sannan ta fito ta buɗe mishi marfin motan tana tafiya da hanunshi a sarƙe cikin nata, sunyi tafiya me nisa da mamakinshi yaga kowa idan sun haɗu masu aikin sai sun durkusa kasa sun gaisheta, da sauri take cewa su tashi kada su durkusa mata, a kofan dake ɗauke da glass suka tsaya knocking tayi kafin ta buɗe, hanan dake zaune akan sofa tayi kyau cikin riga da wando fatar jikinta kaɗai ya isa ya nuna dukiyan da take ciki, da sauri tazo ta rungume ameesha tace "my sweet sis anyi nasara?"
girgiza kai tayi tace "ba'ayi ba amma za'ayi"
kallon fahad tayi ta buɗe mishi hanu alaman ya rungumeta, shiru yayi ya tsaya yana kallonta, ameesha tace "itama yayarka ce"
a hankali ya rungumeta, tace "welcome home my handsome bro"
rike hanunsu tayi suka shiga tare, a hankali ameesha ta zauna tace "akwai wani abu da yake raina"
hanan tace "menene faɗamin?"
ganin ba zatayi magana ba tazo ta zauna a gefenta ta rungume ta tana turo baki a shagwaɓe tace "me kuma sis? ba zaki rabu da damuwa ba kullum?"
tace "hanan ina ganin tsananin kama tsakanin manal da momy"
dafe kirji tayi tace "subhanallah dan Allah ki raba momy da wannan muguwar yarinyar momy babu ruwanta yanzu ma ta kirani tana tambayata ya aka kare da case ɗin kinyi nasara ne? nace mata kin hanani zuwa kince sai zama na biyu zanje, momy tace Allah ya baki nasara yasa kici galaba akan manal, kuma kin san me? yau ma ya yazeed zai zo yana hanya, jirginsu ya kusa landing kuma ta nan zai biyo sabida yasan Abba yana nan"
murmushi tayi ta kalli fahad tace "nasan kanada tarin tambayoyi a ranka amma yanzu zan amsa mata"
tashi tayi ta shiga cikin tsararren ɗakinsu da hanan ta ɗauko wani hoto tazo ta zauna kusa dashi tace "wannan shine Alhaji Abdullahi wato mahaifin hanan shine me gidan marayun da wata mata tamin kwatance a lokacin dana tafi abuja, bayan naje gidan na haɗu da kawa itace hanan, komai tare muke yi da hanan mun shaƙu sosai, kullum hanan tana tambayata me yasa nake yawan kuka ina damuwa? sai na faɗa mata duk abinda ya faru na bata labari, nan take naga ta shiga damuwa, abinda ban sani ba shine hanan itace ƴar me wannan gidan marayun tazo hutu ne tace ita a gidan zatayi hutu sabida babu wanda suke zama dashi a gida sai yayanta yazeed shi kuma a yadda tace baya magana baya shiga harkan kowa, nayi mamaki sosai da naji haka, koda zata koma gida sai tace sai mun koma tare, da kyar na yadda ina tunanin ko abbanta zaiki karɓana sai kuma nayi mamaki naga ya karɓeni hanu bibbiyu bayan ta bashi labarin duk abinda ya faru.
abba yace me nakeso yamin a rayuwa tunda ƴarshi take sona haka? nace Inaso ya sani a makaranta zan karanci law, hakan kuwa akayi na karanci law ita kuma hanan tana karantan theatre art, na samu rayuwa me kyau a gidansu mahaifiyarsu hanan ta mutu tun lokacin da hanan take karama, son da abba yake yiwa momynsu hanan ya hanashi kara aure, da kyar suka sashi yayi aure saide bai dace ba ya auro wata wacce take neman ta kasheshi ta kwashe dukiyanshi ta gudu, bayan ya gano haka ya saketa, ya kara wani aure nan ma ya auro muguwa hakan yasa ya hakura da aure suna zaune haka, watarana muna zaune muna karatu a cikin laptop ɗin da Abba ya siya mana saiga abba ya shigo da wata mahaukaciya amma balarabiya, duk muka tashi zamu gudu saide mukaji tace karku gudu ku tsaya da hankalina yanzu, abin ya bamu mamaki hanan tace Abba ina ka samo mahaukaciya? Abba ya bamu amsa da cewar yaga wasu mutane suna niyan cutar da ita shiyasa ya taimaketa ya zaci tanada haukan ya bata kuɗi sai yaji tace mishi lafiya ƙalau take yanzu abinci takeso"
cikin tausayi ya ɗauketa ya kawota gidan, dani da hanan muka riketa muka kaita ciki saide har yanzu a tsoracen muke, toilet muka fara kaita tayi wanka kafin na kwashe kayan dattin na kai waje na bata sabon kaya tasa sannan nida hanan muka kawo mata abinci taci, bayan ta nutsu muka tambayeta daga ina take?
tace mana itama bata sani ba domin tun tana karama mamanta ta mutu, babanta balarabe ne ya auri bakar fata yaje can yana wulakanta da kyar mamanta ta gudu daga gidan da ita, koda sukazo nigeria mamanta ta wurgar da ita sabida yunwa da bakar azaba, tazo taga gawan mamanta a gefen titi, tace a haka take rayuwa har watarana ta haɗu da wani mutum ya ɗauketa ya kaita gidanshi amma bai aureta ba, ya girmar da ita ya fara zina da ita yana bata manyan kuɗaɗe da kuma duk abinda take so a rayuwa, a ranan da tace ya aureta yace ya rabu da ita ba zai iya aurenta ba, ita kuma da ranta ya ɓaci tace saita tona mishi asiri ganin haka yasa ya fara dukanta har saida ya taɓa mata ƙwaƙwalwa ta zama mahaukaciya, tace batasan shekara nawa tayi da hauka ba amma na kamu da haukan tanada shekara 20, ranan data fara gane hankalinta shine ranan da wasu mutane suka bigeta suka kaita asibiti, bayan an kwantar da ita ta tashi taga inda take kawai ta gudu, daga nan saita shiga mota batasan ina za'aje ba, tsintsan kanta tayi a wannan garin har suka haɗu da Abba, bayan ta gama bamu labari tace zata tafi, nida hanan muna kuka mukace ta zauna damu, ganin babu inda zataje yasa ta zauna, muka fara kulawa da ita muna bata duk abinda take so, wani lokaci ina iya fasa zuwa school sabida naga tana zama tayi tagumi tana yawan tunani da kuka, hakan yasa nake yawan zama kusa da ita ina bata labari, dani da hanan muka roki Abba ya aureta, Abba ya amince sabida labarinta da yaji, ranan aure muka yi mata kwalliya ba dan taso ba tasa sabbin kaya, nayi iya kokarina dan ganin ta samu rayuwa me kyau ta sake tana rayuwa kamar kowa, to amma bayan na zauna da momy sai naga tana min kama ko yanayi da wata, na rasa dawa take min kaman saida na dawo nan naga tana kama da manal"
hanan a shagwaɓe tace "haba mana sweet meyasa kike haka ki daina wannan maganan manal fa na gaya miki muguwa ce ta karshe, na baki labarin lokacin da Abba ya kawoni karatu a wajen kakata a kafuna kafin ta rasu, munyi class ɗaya ta kona min teddy ɗina tace data rasa saide kowa ya rasa, wannan abin da tamin har yau yana raina, tun tana karama take mugunta bata dariya bata magana, gata da kyau kamar aljana, amma kin fita kyau"
kwaɓe fuska ameesha tayi tace "banfi manal kyau ba, nasan inada kyau amma manal ta fini shiyasa man yaje wajenta ya barni"
kallon fahad tayi tace "karka damu zamu samu mama insha Allah zamu fara nemanta daga yanzu, sannan Imran zai fito daga prison komai zaiyi daidai kaji?"
yace "to"
wayan hanan yayi ringing ta ɗauka da sauri tace "ya yazeed"
cikin rashin son magana a takaice yace "na iso"
tsalle tayi ta fita daga ɗakin taje cikin gida inda mota ya tsaya, da gudu taje ganin ya fito sanye da baƙin suit, subhanallah wani irin kyau ne dashi tsaban farin fatarshi har ya koma yellow, skin nashi kamar na mace yana glowing, hancinshi me tsayi bakinshi ɗan karami, yana sanye da baƙin glass a idonshi hanunshi rike da jaka saide fuskanshi a murtuƙe babu dariya, da gudu ta faɗa jikinshi tace "oyoyo ya yazeed"
a hankali ya rungumeta baiyi magana ba, kuka ta fashe dashi, yana shafa bayanta cikin muryanshi me sanyi da daɗin sauraro yace "kukan me?"
shiru tayi tace "shekara ishirin saide video call da waya? yau naga yayana wanda tunda momynmu ta mutu ya tafi ya barni ya koma kasar india da zama ba dole nayi kuka ba?"
janyeta yayi daga jikinshi ganin tana nema ta sashi kuka yaja karan hancinta yace "to aku sarkin surutu"
murmushi tayi ya rike hanunta yace "Abba yace sai dare zai dawo"
suna tafiya tace "eh haka yace"
shiga ciki sukayi ameesha tana ganinshi tayi kasa tace "ina wuni"
a takaice yace "fine"
shima fahad yace "ina wuni?"
yace "fine"
hanan tace "itace ameesha wacce kullum nake tura maka hotonta da nawa"
yace "okay"
shiga ciki yayi ameesha bata damu ba dan hanan ta gama faɗa mata halinshi mugun miskili ne na karshe, ɗakinshi ta kaishi ya shiga ya zauna yana kallon ɗakin, zama tayi zata fara zuba mishi surutu yace "jeki banson surutu na gaji"
turo baki tayi tace "to ina tsaraba?"
yace "sai anjima jeki zan canja kaya"
tashi tayi ta fita, ya tashi ya cire suit na jikinshi yasa vest da gajeren wando, hawa gado yayi domin ya kwanta ya huta, wayanshi yayi kara a gajiye ya ɗauka yana kara kwanciya rub da ciki, ganin sunan ROHI yana yawo ya ɗaga a hankali cikin muryan bacci yace "Baby"
cikin harshen turanci yace "i missed you"
tace "let's do video call"
yace "okay"
buɗe video call call, ya ganta kwance akan gado rohi wata kyakkyawar budurwashi ce ita kaɗai yake kulawa baya kula kowace mace, ko ita ɗinma wata rana baya kulata, zatazo tayi ta kuka yaki kulata har sai yaga dama amma yana sonta sosai da sosai, hot ce domin ko yanzu wando ne ɗan karami a jikinta na jinx, da riga fari transparent, yana iya ganin shatin nipples nata ta cikin rigan, gashinta a kame da ribbon tanada wani irin masifaffen kyau, murmushi yayi ganin tana rungume pillow cikin harshen turanci suke magana amma ta iya hausa kaɗan kaɗan ya koya mata, yace "you miss me?"
idonta cike da hawaye muryanta yana rawa tace "so much, ba nace ka tafi dani ba kaki"
yace "sorry baby zakizo watarana"
shiru tayi tana kallonshi
lumshe ido yayi ya buɗe yana kallonta da tsumammun idanunshi yace "shirt up"
kallonshi tayi tana dariya tace "i can't"
turo baki yayi yace "i miss them Inaso na gansu"
ɓoye kirjinta tayi da pillow tace "nooo"
da alama tana matukar sanshi, yace "shikenan tunda ba zaki ɗaga ba"
ganin yayi fushi tace "okay"
ya zuba mata ido, tashi tayi ta zauna tana kallonshi, zata ɗaga rigan yace "it's okay"
murmushi tayi ganin shima yana murmushi tace "you sure?"
gyaɗa kai yayi yace "yes, I love you bye"
a hankali tace "love you too bye"
kashe wayan yayi a ranshi yana jin sonta idan har Abba ya amince mishi zai auri rohi idan bai amince bama zai aureta a ɓoye domin ba zai taɓa samun macen da zai rinƙa samun hundred percent pleasure idan yana tare da ita kamar rohi ba, ko muryanta yaji yana iya fara kuncewa bale ya ganta.
Ameesha shiru tayi tana kallon fahad dake cin abinci idonta cike da hawaye, tana tuna yadda man ya shaƙe wuyanta har yanzu tana jin zafi ɓoyewa tayi sabida kar hankalin fahad ya tashi, ga kuma tashin hankalin rashin mama da take ɓoyewa kada ta ɗaga musu hankali, ji take kamar ta aza hanu aka ta ƙwala ihu ko zataji sauƙin abinda yake damunta, ganin idon manal take a cikin nata, da alama zata iya yin komai akan man, dan tana iya hango tsananin soyayyan da take mishi, runtse ido tayi a ranta tace "ya Allah na rasa me nake ciki, ya zanyi?"
hanan tace "dan Allah ki daina wannan damuwan kada ki sawa kanki ciwo"
kukan da take ɓoyewa ta faɗa jikin hanan ta fara yi, hanan sai bubbuga bayanta take tana cewa "ya isa darling sis"
har dare bata samu natsuwa ba, fahad a wani ɗaki me kyau ya kwanta yayi wanka ya canja kaya sabo, har bacci ya ɗaukeshi, hanan tana kwance kusa da ameesha ta rungumeta tana bacci, ameesha kuma idonta biyu ta kasa koda rintsawa, juyi tayi akan runtse ido tayi zuciyanta yana tafasa, komai yana dawo mata sabo tana tuna Imran daya fita daga hayyacinshi ya koma kamar wani mahaukaci, fahad ya rame yayi baƙi ƙirin, gashi babu mama an saceta, toshe baki tayi tana kuka, batasan time ɗin da kukan ya suɓuce mata ba ta fara yi da karfi zuciyanta yana zafi tace "wallahi koda zan rasa raina saina rama duk abinda kikayi manal saina fito da Imran daga wannan kuncin
wsyarta ne ya fara ringing ɗauka tayi tana duba sunan dake yawo a gaban tsadadden screen na wayar, gani tayi SWEET MOM yana yawo a gaban wayar, murmushi tayi ta amsa call ɗin tace "momy na?"
momy wacce take zaune akan sallaya cikin wani tsararren ɗaki ta mike tana ninke sallayan sannan ta cire hijabin jikinta, subhanallah wannan itace asalin balarabiya, tssyawa faɗan kyawun wannan balarabiyan ɓata lokaci ne, cikin sanyin muryanta tace "ƴata Ameesha kada ki karaya a kullum kece kike bani karfin gwiwa kece kike cewa na daina shiga a damuwa, idan yau bakiyi nasara ba gobe zakiyi haka rayuwa take, ina nan ina tayaki da addu'a a matsayina na uwa, da yaddan Allah zakiyi nasara akan wannan manal ɗin, ba zatayi albarka ba ban ganta ba amma na tsaneta, idan har kinga wannan case ɗin zaifi karfinki ni nayi alkawarin shiga kuma zan tabbatar na taimakeki koda mutuwa zanyi, ina tare dake ƴata Ameesha"
cikin muryanta daya dishe tace "momy na gode ki kwanta kiyi bacci zuwa gobe zamuyi waya"
tace "ameesha na saba dake ba zan iya baccin ba idan bana ganinki"
tace "momy ki kwanta mana ko sai nayi fushi?"
da sauri tace "A,a zan kwanta"
murmushi tayi momy ta kwanta, ameesha tace "good night momy"
tace "good night I love you"
tace "love you too momy"
katse wayan tayi ta kwanta tana kallon saman ɗakin ta rasa tunanin mema zata fara tsaban yadda lissafinta ya dagule.
*Laifin daɗi karewa Anan na kawo karshen free pages, duhu da haske naira ₦400 ta account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, sai a turo katin shaidan biya ta nan 08144818849 please idan kinsan baki shirya ba kada kimin magana receipt kawai zaki turamin ni kuma zan tura miki complete*
_Jiddah Ce..._
08144818849
managarciya