MAMAYA:Labarin Soyayya Mai Ban Al'ajabi Tsakanin Mutum Da Aljan

MAMAYA:Labarin Soyayya Mai Ban Al'ajabi Tsakanin Mutum Da Aljan

 

 

 *Shafi na Huɗu*

 

 

Sallamar Babansu Bilkisu ce ta karaɗe gidan baki ɗaya, abin da yasa yaran gidan fitowa da gudu suna "ga Baba ga Baba !

 

Bilkisu na biye dasu ta karbi jakar hannunsa ta shiga ɗakinsa ta a je , shi kuma kai tsaye ya nufi ɗakin Inna dan ganin uzurin da ya hanata fitowa duk da tanajin shigowarshi.

 

Kwance ya iske ta ƙasan leda sai barci take hankalinta kwance ga alama ba ƙaramin daɗin barcin nan ta ke jiba .

A hankali yabi ya ɗauko filo ya ɗora mata kanta samansa ya juya ya fice daga ɗakin.

 

Duk abin da ke faruwa babu wanda Inna bata ji ba , amma ta kasa koda ɗaga bakinta balle yatsanta guda , ji take tamkar an ɗaure mata gaɓɓai ta ko i na .

 

San da Babansu ya shigo ta so kwarai tai ihu ko zai kawo mata ɗauki amma taji bakinta tamkar an datse mata shi gam.

 

Sai daya jima da barin ɗakin sannan taji jikinta ya dawo nata , wuf ta yunƙura tana jinta miƙe zaune ai sai ta kwasa da gudu tai waje .

 

Bilkisu ta zuboma Babansu abinci kenan ta nufi ɗakinsa dan ta kai masa taga fitowar Innarsu daga ɗakinta tamkar wani ya biyota .

Tsaye ta yi jim tana nazari kan Innar tasu a cikin kwana biyu rak ta sauya tamkar ba ita ba , girgiza kai tayi sanda taga Innarsu ta wuce ta fuu ta faɗa cikin ɗakin Babansu .

 

"Ya ilahi ,, itace kalmai da ta ambata tabi bayan Innarsu cikin ɗakin.

 

 

Shima dai Baban kallon mamaki yabi ta dashi dan yaga kamar ta ɗan rame ta fita hayyacinta .

Gyaran murya yayi "Huraira baki jin daɗin jikin ne halan ?

 

Cikin ɗan mamaki da faɗan daya gama bin jikinta tace " Kamar ya ban da lafiya Malam ?

Kaifa tsiyarka ke nan daka motsa sai ka samu wani takaicin ka manna ma mutum yana zaman-zamansa , to lafiya ta lau ni wani sabon a bun kaga ni daga dawowarka guna ne ?

 

Murmushi yake yana cin abincin sa , in da sabo ya saba da wannan halin na matarsa , mace ce mai faɗan tsiya da abin da ya kamata tai magana da wanda ya kamata ta kauda kai duk magantuwa ta ke kanshi .

 

Sai da ya kammala cin abincin san nan ya yi hamdala ya dube ta " Na same ku lafiya ? Ya gidan da hidimar gidan ?

 

Kallonsa tayi zuciyarta na shawartar ta akan ta bashi labarin guntun mutumin da guntayen yaran nan , cikin ƙwarin gwiwa tace " Lafiya lau kowa sai dai abubuwan mamaki sun faru da dama cikin gidan nan da baka nan ,,

Cikin natsuwa ya dube ta a lamar yana sauraren ta .

 

Taci gaba " Ran da kai tafiyar nan tsakar dare na fito yin bowali (fitsari) amma ƙiri_ƙiri na ga gidan nan ya juye min na kasa gane banɗakin sai dai a kwata nayi sa malam ,,

 

Murmushi yayi "Huraira kice ɗimuwa kikai ranai ? Ai da kin taso ɗiyar albarka (Bilkisu) ta nuna maki ,,

Murmushin yaƙe ta yi , har ga Allah ba haka tai niyyar faɗi ba amma sai taji ta faɗi hakan .

 

Yaran kowa ya shigo yayi mashi sannu da zuwa .

 

 

 _Dare mahutar Bawa_

 

 

 

Kamar yanda Bilkisu ta saba kowane dare takan rayashi da karatun Alkur'ani mai girma ne , to yau ma hakan  ya faru .

 

Tana zaune kan darduma tana rero karatun Alkur'ani cikin muryar ta mai daɗin saurare , tana cikin karanto suratul Maryam (khahafi) gaba ɗaya hankalinta yana kan karatun har takai sumuni .

Ta ɗan saurara kenan zataci gaba sai taji wata murya mai taushi tana cigaba da rero karatun Alkur'anin cikin sanyin murya .

 

Juyowa tayi dan a saninta kaf cikin ƙannenta babu mai irin muryar , sannan basu kai hizif talatin ba ai .

 

" Ya kika dakata da karatunne Malama Bilkisu ?

 

Wannan karon wata murya ce marai daɗin saurare tai maganar .

 

Dube-dube ta kamayi tana jin tamkar ta ruga kan gado ta boye ,

 

"Kar ki bari Yah Malam ya riga ki gama surannan idan ya riga ki zamui maki dariya Bilkisu ,,

 

Suman zaune taso yi a inda take bakinta ya datse ta kasa ko jan numfashi mai karfi . Zuciyarta ce kawai ta fara karanto ayatul kursiyyu .

 

" Ai ke kin ji matsalarki da an fara arba dake sai ki toyemu da karatun nan naki , to nidai na tafi saura su Yah malam ,,

 

Wannan karon da karfi take karatun a bayyane , dan ta tsorata iyakar tsorata .

 

Inna da tana kwance ta ji sautin karatun Bilkisun ya cika mata kunne sai abin ya bata haushi , "yarinya ba ta tashi karatu dan gulma sai tsakiyar dare ,,

Babansu dake gefe yana lazimi ya dubeta ya girgiza kai , yana mata fatar ta gane abin da take ba daidai bane.

 

Ganin ta yunƙura zata fice daga ɗakin yasan kuma gun Bilkisun za ta je tai mata faɗan nata na gado ya katse lazimun .

 

" Haba Huraira ke yanzu ba jin daɗin ki bane Allah ya baki yarinya mai hankali da natsuwa irin haka ba ?

 

Yamutsa fuska ta yi ɗan kwalinta a hannu ta nufi ƙofa " Allah malam sai naje naji dalilin wannan karatun daren da take tana hana ni barci ,, ta fice daga ɗakin bata samu damar ɗaure kan nata ba .

 

 

Tana tafe tana sababinta ta ji tayi karo da wani abu , dubawa tai dan ganin ko miye taci karo da shi .

 

Dafe kai tayi ta wage baki iya karfinta ta kwarma ihu

 "wayyo malam !

" Ni Huraira yau na yi baƙin gamo zo ka gani malam,,

 

Kallon abin da yasata ihun nayi nima .

 

Wani murgujejen baƙin ƙadangare ne ta gani jikinsa baki ɗaya kawu nane na wasu ƙadangarun , ga wata ƙatuwar jela wajen bindinsa , bakinsa wasu jajayen haƙora ne kafta-kafta idonsa huɗu kowane sai jujjuyawa yake .

 

Cike da tsoro ta yunƙura da nufin komawa ɗakinta , caraf taji an riƙe ma ta babban yatsan kafarta .

 

A firgice ta kalli yatsan dan ganin abin da ya riƙe mata shi haka ,  ashe kai guda ne daga cikin kawunan ƙadangaren ya riƙe mata yatsan .

 

Babu irin nau'in ihun da Inna ba taiba amma ga alama babu mai jin ihunta a gidan , dan ba wanda ya motsa daga yanda yake kwance kaf ahalin gidan .

 

Iyakar galabaita ta galabaita idanunta sun ƙara girma muryarta harta shaƙe dan azabar ihu da kiran malam .

 

Ƴan yaran ɗazun taga sun fito daga cikin bakinsa suna tuntsura dariya mai amsa kuwwa da amo .

 

"Ke dai baki jin magana ba sai da Samdan yayi maki kashedin tadamu da masifarki ba ?

 

" To yau zamu yi gasar masifa mu dake idan kinci zamu baki kyautar wannan abin namu. (suka nuna ma ta wannan ƙaton ƙadangaren )

"Idan kuma kika faɗi to zamu cire haurenki na ƙurya (haƙori)

 

Ga alama Inna batama san inda kanta yake ba dan tayi tubus ,

 

A cikin ɗakin su Bilkisu kuwa jin komi ya daidaita ta daina jin muryoyin sai ta mike da ƙyal ta nufi waje da nufin sako wata alwala dan ta kabbara sallah nafila .

 

Bakinta bai gushe yana karanto addu'ar neman tsariba daga abin halitta har ta fice daga ɗakin .

 

Ganin ta yasa guntayen da halittar suka bace bat , sai Inna dake kwance ƙasa magashiyan murya bata fita ko kaɗan ga inda ta faɗi ya ɗau fushi ya kumbura fuskar tayi suntum .

 

Cikin sauri Bilkisu ta gama alwala ta koma ɗakinsu bata ga Inna da ke kwance cikin wani yanayi ba.

 

Shigar Bilkisu ɗakinsu ke da wuya , wata mata ta bayyana gaban Innar fuskarta ba kyan gani idanunta sai yoyon nono suke madadin ruwa , bata da hanci ko kaɗan a fuskarta hakama babu kunnuwa ammafa idanunta sun yi kofar ɗaki mai faɗi .

 

Ta dubi Inna ta kwashe da dariya tace " shin zaki bamu waje koko sai nasaka jikokina sun yi wasan ɗanɗare dake ?

Idanuwan Inna gwale-gwale ta dubi matar , ai bata san lokacin data yunƙura ta miƙe tsaye ta kwasa da gudu ta nufi  ɗakinsu ba .tana jin ƙarai dariyarsu kala-kala ta samu dai ta afka jikinta sai rawa yake .

 

Malam na zaune inda ta barshi sai laziminsa yake baiko  ɗago kai ya dube taba , dan yana jiyo faɗan da take ma Bilkisun sama-sama daga nan inda yake .

 

Ai Inna na jinta kan gadon ga malam zaune sai ta nemi fashewa da kuka sabo .

 

Abin da ya harzuƙa Malam kenan ya turniƙeta da faɗan ta raina shi yace kattaje ta je tayi abin da ranta keso shine dan tafi kowa masifa zata dawo ta fasa masa kuka cikin dare , to wallahi ta kiyayi gamuwarsu.

 

Inna dai ba baka sai kunne , ga mamakin yanda malam yai biris da kiran da take kwaɗa mashi ga ihu tana yi wanda tasan ko shakka babu makwabtan su gobe sai sun zo jin abin da ke faruwa .

 

Jin tana ta kukan ya  yunƙura ya isa gaban ta ya haska fuskarta da fitila .

 

"Ya Salam Huraira garin yaya kika faɗi haka ?

 

"Amma yanzu sabida Allah kan wannan faɗuwar kike kukan nan Huraira ?

 

Takaici yasa ta gimtse bakinta tai luf jikinta ba inda bai mata ciwo karma gefen fuskarta yaji .

 

 

 

Washe gari da safe Bilkisu ta kammala komi ta ji shiru Innarsu ba ta fitoba dan haka ta nufi ɗakin Innar kai tsaye ƙannenta na biye da ita dan sun gaisa da Babansu ya fice kasuwa .

 

 

Saboda zullumin abin da zata iske yasa ƙannenta suka shige suka barta tsaye kofar ɗakin .

 

Kawai jiyo yaran tayi sun fashe da dariya su duka , abin da yasa ta faɗa ɗakin ba shiri kenan .

 

Turus tayi ganin yaran sun tasa Innarsu sai dariya suke gaggaɓawa , kallon Innarsu tayi dan ganin yanayinta .

 

Ya Salam !

 

"Inna miya faru daku haka ?

Kinga yanda fuskarki tai kumburi ?

 

 

 

Sai lokacin yaran suka daina dariyar ganin Yayarsu cikin tashin hankali ainun  , amma su da suka ga Innar dariya fuskarta, ta basu ta koma kamar wata halitta mai ban dariya.

 

Inna dai ba baki sai kallonsu take abin da yasa Bilkisun hawaye kenan .

 

Da ƙyal Inna tace ma Bilkisun ta fito da dare ne ta zame ta faɗi bakinta ya bugu .

 

 

Ranai dai haka Bilkisu ta haƙura da zuwa duka makarantun dan Inna ba lafiya .

 

 

 

Wacece Bilkisu ?

 

Bilkisu Ahmad shine cikekken sunanta , suna zaune a cikin garin Funtua a unguwar Barmani coge , mahaifinta mal Ahmad mutum ne mai sanyin hali da neman na kansa yana sana'ar sai da gwanjo , mahaifiyar ta Huraira mace ce mai faɗan tsiya kowa yasan faɗan ta a rukunin layin .

 

Suna da yara ukku duk mata Bilkisu ce babbar su sai Amina, da ;Hafsa Allah bai basu namiji ba . Huraira irin mutanen nan ne da sam basu damu da ibada yanda ya kamata ba sannan kafin ta ambaci Allah sau ɗaya saita ƙunduma zaki kala biyar , ko abin tsoro ta gani bata iya ambatar Allah sai dai ta wage baki ta kurma ihu , mal Ahmad yana yawan yi mata faɗan wannan baƙar tabi'a tata amma har yau ta gaza dainawa ta riga tabi jikinta , saɓanin ƴaƴanta da komi nasu sai sun saka Allah ba kamar Bilkisu da ko da yaushe idan Babansu ya koya masu karatun takan ƙara mai-maitama ƙannen nata, hakan yasa suke da natsuwa da son addini bakin gwargwado , Inna tasha fatattakarsu idan suna bitar karatun Alkur'ani , takance " ku da ba maza ba karatun mi ? Iyakarsa dai ɗakin aurenku ai , koko ni da ban yi na kirki ba na kasa zama lafiya ne a gidan aurena ? Ko wani ɓakin lamari yazo yasha mun kai ne ?

 

Haka zatai ta mita da sababi har sai  sun gama karatun .

 

 

Wannan kenan .

 

 

Yau kwananta uku bata samu damar zuwa Makarantar islamiyya ko bokonba , dan haka yau da yamma ta ga dacewar zuwa islamiyyar dan jikin Innar da sauƙi ainun  harma ta koma kan faɗan ta na gado .

 

 

Tun da ta shiga ajin nasu kawayenta ke binta da kallo , abin da yasa ta taɓa Shema'u kenan , "wai ya naga kowa sai kallona ya ke ne ?

Shema'u tace " tausanki muke dan kullum sai mal. Aminu (Ɗan bahagon) ya kira suna kuma ana cewa baki zo ba ,,

 

Ido waje ta dubi Shema'un " Da gaske kike ko dai jana kike dan Allah ?

"Wallahi sai in koma gida Baba ya rakoni dan kinsan Inna ce ba lafiya ,,

 

Jin hayaniyar ajin tayi tsit yasa ta duban ƙofar ajin .

 

"Innalillahi , shine abin da ta furta cikin zuciyarta , ganin mal. Aminu ya shigo fuska ba annuri sai zare-zaren idanu yake tamkar yana neman wani .

 

 

Zuciyarta ta gama bata shawarai idan zai mata dukan rannan to ko shakka babu rugawa da gudu zatai bazata tsaya ya illatar da ita da dukanshi ba .

 

 

To ya kenan ?

 

Zata kuwa rugan ko ko bazai dake taba ?

 

Haupha.....