DUHU DA HASKE: Fita Ta 25
Ameesha aiki take sosai tana sauri kar dare yayi nisa ta samu taje gidan ammi suci abinci kafin ta tafi gida, da kyar ta gama aikin ta cire uniform nata ta rike a hanu ta fara tafiya tana kallon time lokaci ya tafi gashi an idar da mangrib, cikin sauri ta shiga motar ta tada, gani tayi motar yaki tashi, buga motan tayi cikin ɓacin rai tace "meyasa zakamin haka mota?" fitowa tayi ta rufe da makulli sannan ta samu me gyara ta bashi tace "idan an gyara a kaimin gida kawai zan shiga taxi"
DUHU DA HASKE: Fita Ta 25
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 25*
~Shaƙuwa me karfi ne yake shiga tsakanin ameesha da yazeed, yauma tayi shiri cikin riga da skirt na leshi sky blue, ta ɗaura kanta da siririn mayafi tasa takalmi white me kyau, kamshi take sosai hanunta ɗaya rike da waya tana dannawa kanta da hankalinta duk akan wayar, ɗayan hanunta kuma rike da uniform nata, kamar koda yaushe cikin sauri take zatayi kwana sukayi karo da yazeed wanda ya fito daga ɗakin abba shima yana latsa waya yayi kyau cikin sky blue na shadda, riketa yayi ganin zata faɗi yace "easy"
da sauri ta buɗe ido tana kallonshi ganin bata faɗi ba, tace "yaya munyi anko"
kallon yadda tayi kyau yayi sannan yace "amma nafi yin kyau"
turo baki tayi tace "a,a nikam nafi kyau"
murmushi yayi yace "to na yadda"
wayanta ta ɗaga tace "photo"
murmushi yayi ya tsaya kusa da ita sosai itama tana murmushi tayi musu photo, nuna mishi tayi tace "munyi kyau, tsaya nayi maka kai kaɗai"
yace "meesha ban iya pho..."
gyara mishi hulan tayi tace "shiru"
shiru yayi ya tsaya ta fara mishi hotuna masu kyau, nuna mishi tayi tace "yaka gani?"
yace "sunyi kyau meesha i love you"
ta saba da man suna iya faɗan wannan kalman wa juna a koda yaushe shiyasa bata wani damu ba tace "love you too"
tana faɗa tana dudduba hotunan, kallonta yake yi murmushi ya kasa tafiya daga fuskanshi, saida ta gama dubawa ta ɗago suka haɗa ido, signal tayi mishi tace "ya da kallo haka?"
yace "kinyi kyau"
tace "yau kam ba tare zamu tafi ba, bari na shiga na gaida Abba saimu fita tare kowa ya shiga motarshi"
dariya yayi ganin bataso su tafi daban daban amma ya zama dole dan yau akwai inda zaije, da sauri momy ta saki labulen ɗakin Abba tana kallonsu tana murmushi, shigowa ameesha tayi ta durkusa kasa ta gaida Abba dake zaune akan sofa sanye da jallabiya yana shan tea, yace "barrister har kin fito?"
tace "eh Abba zan wuce"
gaida momy tayi tace "a dawo lafiya ameesha"
tace "Allah yasa"
tashi tayi da sauri ta fita, hanan ce ta fito tana sa rigan uniform nata na dr, gefenta Imran ne da fahad da alama tare zasu tafi yau, ameesha tafe "ya fahad bai shirya school ba?"
Imran yace "zamu je hospital nasu hanan ne"
zatayi magana hanan tace "gobe zai je"
bata musa ba kawai tace "to bari naje ya yazeed yana jirana"
tafiya tayi ta shiga motarta shima ya shiga nashi, tare suka fita tana ɗaga mishi hanu har yayi nisa, hanyan zuwa kotu ta kama, wayarta ta ɗauka ta kira baba megadi tace "ina kwana baba?"
yace "lafiya kalau ƴata ya kike ya gajiyanki?"
tace "alhmdllh, sun dawo?"
yace "basu dawo ba"
tace "to masha Allah anjima zanzo may be ka kira wayata a kashe amma tunda basu dawo yau ba may be ba zasu dawo nan kusa ba"
yace "to ƴata"
katse wayan tayi tana tafiya, waya ta kara kira saide wannan karon jikinta a sanyaye tace "har yanzu babu wani labari ko?"
shiru tayi tana saurara sai kuma tace "kaci gaba da bincike da kuma bibiyan komai na manal, harda company ɗinta na m.u.m ka bincika sosai har sai ka gano wani abin"
yace "to shikenan"
a hankali tace "na gode sosai"
katse wayan tayi tana driving a hankali.
murmushi da murna da farin ciki akan fuskan manal, yanzu ta samu lafiya zatayi rayuwa kamar kowa, kallon Abdool tayi wanda yake shirya kayansu a luggage yana murmushi shima kana ganinshi kasan yana cikin farin ciki mara misaltuwa, tace "my abdool yau zamu koma nigeria?"
gyaɗa mata kai yayi, ta tashi da sauri taje ta rungumeshi tace "daɗi nakeji sosai, yanzu zamu fara zuwa m.u.m fashion designing tare da kai a matsayin couples, my abdool nasan sai soyayyanmu ya birge kowa"
cire hanunta yayi daga cikinshi ya juyo da ita ya mika mata kayan da zata sa yayi mata alaman ta canja domin jirgin yamma zasu bi kuma 4 yayi, karɓa tayi tana kallon kayan ba zata taɓa mantawa ba wannan shine kayan data sa ranan da suka haɗu da abdool, dogo riga ne ja yana da tsayi bayan yana sharan kasa, gaban kuma guntu, murmushinta dake kara mata tsananin kyau tayi sannan tace "ka tuna wannan kayan? dashi muka fara haɗuwa a ranan da kaje neman aiki company ɗina"
murmushi yayi mata yace "na sani"
a gabanshi ta cire zip ɗin gaban riganta dake jikinta ta sauke kasa, kallonta yake harta canja kayan, mayafi siriri yayi mata rolling kanta dashi sannan ya durkusa ya kamo kafanta yasa mata takalminta me tsayi shima red, tashi yayi ya ɗau karamin jakanta red ya ciro kayan kwalliya, ya riko hanunta ya zaunar da ita a bakin gadon ya ɗau powder ya shafa mata sannan ya shafa mata red na janbaki a lips nata, mascara ya shafa mata a zara zaran eyelashes nata, murmushi yayi mata ganin tayi masifaffen kyau, turare ya fesa mata, sannan ya ɗauki kayanshi zai shiga toilet ya canja, hanunshi ta rike ya juyo yana kallonta, girgiza kai tayi cikin crazeness nata ta taso tana wani irin tafiya me kama dana beaches, tazo gabanshi tace "nice zan canja maka my abdool"
cikin wani murya tayi maganan, zaiyi magana tasa yatsa ɗaya a bakinshi tace "shiiii"
shiru yayi ta karɓi rigan ta kalla murmushi tayi bayan ta cire mishi jallabiyan jikinshi tace "wannan kayan bana taɓa mantawa dashi muka fara haɗuwa, dashi kaje company neman aiki, nima ka zaɓomin kayan dana sa a ranan da muka fara haɗuwa, wow abin yamin kyau sosai"
murmushi yayi mata yana ganinta tana rufe mishi bottle na rigan har tasa mishi belt nashi sannan ta fesa mishi turare, luggage ɗinsu ta rike tana turawa hanunshi cikin nata suka jera suka fito daga ɗakin da aka kwantar da ita, juyawa tayi ta kalli ɗakin tace "bye bye Abdool and manal sun tafi"
dariya kaɗan yayi ganin yadda tayi abin kamar wata yarinya, office na dr sukaje yana ganinsu ya tafa hanu yace "congratulations manal Allah ya kara lafiya"
murmushi tayi tace "thank you dr"
wata nurse wacce take kula da manal ɗin ta shigo tana rike a plate na magunguna ta mikawa manal tace "ga wannan ki rinƙa amfani dashi yadda aka rubuta"
murmushi tayi tace "thank you"
hanu nurse ɗin ta mika mata tace "congratulations"
itama sa hanun tayi a cikin na nurse suka gaisa tana murmushi, zame hanunta nurse tayi sannan ta mikawa Abdool tace "congratulations"
zaisa hanunshi a nata manal taji wani abu ya tsaya mata a wuya, wani kallo ta aikawa nurse ɗin sannan tayi sauri ta riga Abdool sa hanunta suka kara gaisawa, wannan karon matsa hanun nurse ɗin tayi da karfi saida tayi kara, da kyar ta samu ta sakar mata hanu tayi murmushi tace "nice ya kamata ki gaisa dani kaɗai ba mijina ba"
Abdool kallonta kawai yake sai kuma ya kalli nurse ɗin, luggage nasu taja sannan ta rike hanunshi tace "thank you Dr"
tafiya sukayi har zuwa wajen motar da tayi musu booking suka shiga, yana ganin farin ciki sosai a tare da ita, tace "yau zanje naga ammi na"
har suka isa airport sai karfe biyar aka fara sanarwa jirginsu zai tashi, zaune suke kusa da juna manal tasa baƙin glass a idonta ta ɗaura kafa ɗaya akan ɗaya, man kuma yana latsa waya yana tauna cingum kaɗan kaɗan.
Ameesha aiki take sosai tana sauri kar dare yayi nisa ta samu taje gidan ammi suci abinci kafin ta tafi gida, da kyar ta gama aikin ta cire uniform nata ta rike a hanu ta fara tafiya tana kallon time lokaci ya tafi gashi an idar da mangrib, cikin sauri ta shiga motar ta tada, gani tayi motar yaki tashi, buga motan tayi cikin ɓacin rai tace "meyasa zakamin haka mota?"
fitowa tayi ta rufe da makulli sannan ta samu me gyara ta bashi tace "idan an gyara a kaimin gida kawai zan shiga taxi"
yace "to hajiya"
taxi ta shiga saida ta tsaya a inda ta saba siyan kaza da sauran kayan abincin sannan ta koma taxi ɗin suka tafi, a kofa ya ajeta ta kira ya yazeed tace "please kazo ka ɗaukeni motata ta lalace"
ya amsa mata da to, shiga ciki tayi ta bawa baba megadi nashi sannan ta shiga ciki, ammi tana ganinta yau harda yin dariya mara sauti, murmushi ameesha tayi tace "ammi barka"
saida tayi mata wanka sannan ta canja mata kaya ta wanke kayanta me dattin ta shanya a toilet ɗin, turare ta fesa mata na dare sannan ta hau gadon ta fara bata abincin ganin ita bataci ammi ta ɗauko naman ta kai bakinta, ci ta fara farin ciki baya ɓuya a fuskan ammi a duk lokacin da Ameesha tazo, a ranta ji take kamar taga ƴar data haifa a cikinta, kwanciya tayi cikin gajiya akan gadon ta ɗaura kanta a cinyar Ammin tace "wayyo yau na gaji sosai ji nake kamar na kwana anan tare dake ammi"
murmushi kawai ammi takeyi tana shafa kanta, rufe ido tayi tana jin baccin gajiya yana shirin ɗaukanta.
babban Airport jirginsu yayi landing, murmushi manal tayi sannan tace "mun dawo gida nigeria"
hanunshi ta rike sannan ta rike luggage suka fito yana goye da jakan baya, tana sanye da bakin glass ɗin shi kuma yana taunan cingum a hankali yana kallon yadda gari ya ɗanyi duhu, can suka hango driver da gudu yazo ya durkusa gabansu yace "barkanku da dawowa"
karɓan kayansu yayi yaje yasa a mota, tare suka shiga motar, manal ta ɗaura kanta a kafaɗanshi tace "i miss my home"
murmushi yayi kawai yana cigaba da taunan cingum, driver ya jasu direct sai gida, har ya shiga dasu ciki baba megadi bai kula dasu ba ya zaci kamar kullum yauma yawo kawai driver ya tafi, saida ya fito da gudu ya buɗe musu motar, kafar manal daya gani sanye da dogon takalmi gashi ƙafan fari sal yasa jikinshi ya fara ɓari, da kyar ya iya ciro wayanshi daga aljihu yayi dialing number ɗin Ameesha, a firgice yake kiranta yanaso yace ta ɓuya sun dawo, hanun man dana manal a haɗe suka fara takawa zuwa cikin gidansu da sukayi mugun missing nashi, ameesha tana bacci akan cinyar Ammi jin wayarta yana kara ta turo karamin bakinta batason damuwa idan tana bacci, ammi ganin haka saita ɗau wayan ta kashe sabida bataso ameesha tana taƙura, kallon fuskan yarinyar take tana murmushi inama ace su zauna haka har karshen rayuwarsu da bazata kara kukan rashin haihuwa ba, muryan manal taji tun daga kasa tace "Ammiiiiiiiii mun dawo"
dum dum dum kirjin ammi ya fara bada wani mugun sauti, take jikinta ya fara rawa, ta kara cewa "Ammiiii nayi kewanki"
manyan idanunta ta waro sannan ta zubawa ameesha dake bacci cikin nutsuwa, jikinta yana mugun rawa ta fara bubbuga ameesha cikin bacci tace "uhum"
ammi tana bubbugata ganin bata tashi ba ta fara bugata da karfi,
a firgice ta buɗe ido tana kallon ammi ganin yadda take zaro ido a mugun tsorace, ji tayi manal tana hayowa tana kiran ammi, da gudu ta dira akan gadon tasa riganta na uniform data cire, wayarta ta ɗauka da jakanta da ledojin ta zuba a cikin jakan, sannan ta ɓuya cikin wardrobe ganin manal ta buɗe kofan ta shigo da gudu cikin kyaun da tayi da red dress ɗin data fara ganinta dashi a ranan da sukaje neman aiki, zuciyan ammi yana bugawa har yanzu tana kallon manal wacce ta tsaya tana kare mata kallo, a tsorace take sosai kana ganinta kasan hakan, turo bakinta tayi a shagwaɓe ta faɗa kan ammin ta rungumeta ta manna fuskanta a nata tace "wai bakiyi farin cikin dawowan babygirl naki bane? naga duk kin ruɗe kin shiga tashin hankali kamar wacce taga dodo"
ammi daurewa tayi tana kallonta tayi murmushi sannan tayi mata alaman tayi farin ciki, sakinta tayi ta kalleta tace "amma kinyi kiɓa kinyi kyau sosai ammi kamar lokacin da dady yake raye, me kikeci ne haka? kuma waye yake wannan kulawan dake?"
shiru tayi tana kallon wardrobe tana iya ganin idon ameesha wacce take kallonsu amma su bazasu ganta ba sai wanda yasan tana wajen, murmushi tayi mata kawai, abdool ne ya turo kofan ya shigo, ameesha zuciyanta ya fara duka da sauri da sauri, ganin yayi kyau cikin kayan da suka fara zuwa neman aiki dashi, wajen ammi yaje wacce take kallonshi tana mishi kyakkyawan murmushi, a hankali ya zauna a gefenta ya rungumeta yace "ammi mun dawo manal ta samu lafiya yanzu babu abinda yake damunta na ciwon zuciya anyi mata aiki komai yazo karshe"
murmushi ammi tayi ta shafa gefen fuskanshi, manal tace "my abdool ba kaga ammi tayi kyau ba? sai naga tama fi da kyau waye yake kula da ita haka? kuma banga Atika ba?"
Abdool yana gani jikin ammi ya fara rawa jin manal ta tsareta da tambaya, murmushi yace "bari naje nayi freshen up"
tashi yayi, itama manal ta tashi suka fita, ameesha fitowa tayi zufa ya gama wanke mata fuska, kallon ammi tayi tace "ta ina zan fita daga gidannan?"
shiru ammi tayi ganin hawaye a idon ameesha ta nuna mata window, da sauri ta janye labulen tana duba window, waro ido tayi ganin tsayi domin upstair ne, kallon ammi tayi, ammi tayi
shiru zuciyanta yana tsinkewa, tace "ba komai ammi karki damu zan dira ta nan matukar zan tsira amma daga yau mun rabu ba zan sake zuwa ba"
kafin ammi tayi wani yunkurin ameesha ta rufe ido tana addu'a ta dira, yazeed dake zaune a mota yaji jikinshi ya bashi wannan su manal ne suka shigo domin yaga megadi yanata kiran waya a kashe, shika kiran wayan ameesha yayi yaga a kashe, fita yayi daga motan yana dudduba ta inda zai fara shiga gidan ta ɓarawon hanya domin ya fito da ameesha, ido ya ɗaga sama dan ganin stair me tsawo, zaro ido yayi ganin ameesha tana dirowa daga saman stair, da wani irin gudu ya isa daida inda zata faɗi akan wani dutse dake da tsini, buɗe hanu yayi ta faɗo a kanshi tare suka zube kasa, tana jinta a hanun mutun ta kankameshi gam taki buɗe ido, shima kankameta yayi yana kallon kyakkyawan fuskanta dake ɗauke da zufan wahala, a hankali ta fara buɗe idon ta sauke akanshi, wani irin murmushi haɗe da hawaye tayi, kiss tayi mishi a gefen kumatu tace "thank you"
kasa tashi sukayi a wajen, a hankali ya fara share mata hawayen yace "babu godiya tsakaninmu kin manta nace zan kareki da yaddan Allah a duk lokacin da kika shiga matsala?"
a hankali tace "thank you"
wannan karon with emotion tayi maganan, zai tashi yaji ta kara kankameshi tace "thank you"
tasan badan Allah ya turo mata shi ba da yanzu ta mutu ko kuma ta samu mummunan rauni, ganin tana hawaye yace "to ni sakeni idan kuka zakiyi"
ta share hawayen tace "na daina"
jan karan hancinta yayi yace "good girl tashi akaina to"
tashi tayi, ta mika mishi hanu ya riketa shima ya tashi, karkaɗe jikinshi yayi sannan ya karkaɗe mata nata yana rike da hanunta suka fara tafiya, kunna wayanta keda wuya momy ta kirata, a hankali ta ɗauka tace "hello momy"
momy tace "ina zaune kawai naji kamar kina cikin matsala ameesha"
a hankali tace "babu komai ina tareda ya yazeed"
momy tace "to shikenan yanzu hankalina ya kwanta Allah ya kareki da kariyarsa"
tace "ameen momy"
katse wayan tayi, taga yazeed ya ɓata rai, suna shiga motan tace "ya yazeed na rasa meyasa baka son momy kuma fa tanada hankali ka sani, tana kula da kowa tana bawa kowa respect, kaga yadda take respecting Abba komai ya sata yinshi take jikinta yana rawa, wani lokaci yadda take bawa kowa kulawa har tausayi take bani, meyasa ba zaka saki jiki da ita ba?"
girgiza kai yayi yace "haka kawai batamin ba"
tayi shiru sabida ko fahad idan tayi mishi maganan haka yake cewa, gara Imran yana zama da ita suyi hira sosai, yace "manal da abdool sun dawo yanzu babu zuwa wajen ammi ko?"
jikinta a mace tace "babu, amma zanyi kewarta ji nake kamar na rabu ne da ganin mama"
murmushi yayi yace "meesha da kowa zai zama da irin zuciyanki da baza'a samu matsala ba a cikin mutane, duk zalincin da ƴarta tayi miki amma kike sonta haka?"
tace "nima bansan dalili ba sai naji son matar har cikin raina"
ganin tana magana kanta a kasa yace "ɗago ki kalleni"
a hankali ta ɗago kanta tana kallon kwayan cat eye's nashi, wani irin kyau idanunshi suke mata ga gashin dake saman idon zara zara harma yafi nata yawa, a hankali ta sauke kanta zuwa karamin bakinshi dake murmushi ji tayi gabanta ya faɗi, lumshe idon yayi yace "baki kalleni sosai ba"
kasa ɗago ido tayi sai wasa take da dogayen yatsun hanunta farare tas,
murmushi yayi kawai yaci gaba da driving.
Abdool ya shiga ɗaki yana murmushi yana lumshe ido, luggage nasu ya buɗe sannan ya ɗauko wani akwati dake gefe ya buɗe babu komai a ciki, ajewa yayi akan makeken gadonsu dake shimfiɗe da farin bedsheet, buɗe luggage ɗin yayi ya fara cire kayanshi yana sawa a cikin luggage ɗin da babu komai, nata kuma yana sa mata a cikin wardrobe, a hankali ya kara lumshe ido tunawa da wani abu a ranshi, a fili yace "i miss you all"
takalmanshi duka ya shirya sannan ya ɗau duk wani abinda yasan ya shafeshi a ɗakin ya zuba a cikin luggage ɗin, kallon hoton dake hanunshi wanda ya zana yayi, shi da ameesha ne ya zana su a hoton suna rungume da juna, ameesha sanye da wando kamar yadda ta saba a baya, a hankali ya shafa hoton yana dariya mara sauti idonshi cike da hawaye yace "nasan zaki yafemin idan kikaji uzurina i miss you so much my meesha, yau zan bayyana miki komai kuma zan durkusa gabanki na roki yafiya nasan kinada taushin zuciya, ba zaki taɓa kin yafewa man naki ba, ina son ganin muna sharing matsalanmu kamar baya, dariyanki kukanki magananki tsawanki duk nayi kewansu, i love you so much my meesha"
karaf ya faɗa kunnen manal wacce ta shigo yanzu, kallon tayi ya juya baya yana kallon hoton gabanshi kuma akan gadon luggage ta gani ya shirya komai nashi, ta kalli wardrobe dake buɗe taga kayanta ne kawai a ciki babu nashi, sai kuma hoton daya kurawa ido nashi da ameesha yana shafa hoton yana faɗan wasu maganganun da suka kusa fasa mata zuciya, idanunta take suka sauya kala suka koma jajur harma sunfi na kullum idan ranta ya ɓaci, jikinta ya fara rawa a hankali take takowa ta bayanshi yanajin karan takalminta amma bai juyo ba kuma bai daina kallon hoton ba, hanunta ta ɗaura a kafaɗanshi tace "my abdool"
cire hanun yayi, ta kara ɗaurawa a mugun fusace ya juyo ya nunata da yatsa yace "don't dare touch me miss manal umar maidawa"
manyan idanunta suka kara girma da wani irin shock take kallon Abdool, bakinta yana rawa tace "ab..ab..abdool me nayi?"
murmushin takaici da hawaye masu zafi suka wanke mishi fuska yace "me kika yi?"
zata taɓashi yayi wurgi da ita, faɗuwa tayi kasa kanta a kasa, yace "me kikayi fa kikace?"
dariya yayi tare da hawaye yace "me kikayi manal kike tambayata?"
bata ɗago kai ba tace "kenan kasan komai?"
zuwa yayi gabanta ya durkusa akan kafafunshi yana kallonta bata ɗago kai ba yace "sharrin da kika yiwa su umma, sharrin da kika yiwa Ameesha na zubar da ciki, sharrin da kika yiwa Imran, wace Anty da kikayi, ture Ammi da kikayi daga kan stair duk nasan komai"
bata ɗago kai ba har yanzu tace "to meyasa baka nuna min ka sani ba?"
yace "sabida kinada ciwon zuciya dr yace zaki iya mutuwa nan da shekara huɗu gashi kin samu sauki kuma kin wuce shekara huɗu, kin san wani abu? banso ciwon zuciya ya kasheki nafi son ki rinƙa mutuwa kullum kina dawowa kina ɗanɗanan azaban duk wani abinda kika aikata"
murmushi yaga tanayi, ya tashi kawai ya ɗau luggage ya fara ja zai fita tace "ka manta abu ɗaya bakasa a cikin laifuka na ba"
shiru yayi ta tashi daga zaunen da take tace "Alhaji umar maidawa wato mahaifina wanda ya buɗemin company ɗin m.u.m wanda ya bani duk wani gata na duniya yayi min karatu nice na kasheshi"
a firgice ya kalleta, murmushi tayi mishi da idanunta da suka koma jajur tace "yes kaji labarin kasheshi akayi ko? to ai nice na ƙona motar da yake ciki sannan na tafi can ɗakin hotel ɗin da budurwarshi take ciki idan ban manta ba sunan hotel ɗin enjoy sannan ɗakin number 14 ne"
idanunshi a waje yake kallonta ganin daidai ta faɗa, zuwa tayi inda yake tana takowa a hankali tace "kasan me? tun ranan da naga kace inada taɓin hankali a kotu ka wanke kaninka nasan ka gane komai, sannan yau naga ka bani kayan da muka fara haɗuwa dashi kaima kasa nasan tabbas da abu a kasa, sannan kasan wani abu ɗaya a cikin laifukana da ban karasa faɗa ba?"
murmushi tayi mishi sai kuma tace "ammi nice na zubar da cikin jikinta a lokacin da dady ya mutu sabida banso ta haifi kowa mu zama mu biyu akanta, ina fatan baka manta zancen da nake faɗa ba a kullum wato idan Inason abu ni kaɗai nakeso na mallaka banso na haɗashi da kowa, idan naga zan rasa to fa saide kowa ya rasa"
jikin Abdool yana rawa ya buɗe baki zaiyi magana ya kasa, baisan time ɗin daya shaƙe wuyanta ya fara yin baya baya da ita ba, hanunta ta ɗaura akan nashi tana jin azaban zafi kamar zai kasheta, idanunshi sunyi jajur jijiyoyin kanshi sun taso, saida ya haɗata da jikin bango kafin ya kara danna hanunshi a wuyanta yanaso kawai yaga ta daina numfashi, cikin azaba ta fara cire hanunshi, da karfi tana harhaɗa magana tace "ka sakeni my Abdool"
kanta ya fara bugawa da jikin bangon, ihu ta fara tana neman kwace kanta tana hawaye, shima hawayen yake, da wani irin marin dayasa gefen bakinta fashewa ya fara jini ya ɗauketa, ammi dake zaune akan wheelchair taji karan buga kai a jikin bango ga ihun da manal take, tana bakin kofan ɗakinsun duk taji komai domin tun lokacin da manal ta fito take biye da ita, cikin rawan da jikinta yake ta danna danger dake jikin wheelchair nan take ya fara kara ɗit ɗit ɗit
ganin basu buɗe ba ta tura kofan da kafarta, gani tayi Abdool yana shirin kashe manal, waro manyan idanunta tayi tana girgiza mishi kai tareda ɗaga hannu alaman ya bari, da kyar manal ta tureshi ta kwaci kanta, juya baya yayi yana kuka me sauti kallon ammi tayi ganin tana kara danna danger yana kara tace "ammi na babu abinda yake faruwa muna nan lafiya nida abdoo karki damu kinji ammi na?"
smmi kallonta take sai kuma ta kalli abdool da yake kuka kara danna danger tayi tanaso ya juyo amma yaki juyowa, cikin wani irin tsawan da yasa ɗakin girgiza manal tace "ɗit ɗit ɗit kin dami mutane da ɗit ɗit ɗit nace miki komai lafiya ki koma ɗakinki"
cikin sanyin jiki ta juyar da wheelchair zata koma ɗakin taga man ya juyo yaja luggage ɗin yana tafiya, da gudu manal ta fara binshi durkusawa kasa tayi a gabanshi ta haɗa hanu biyu ga bakinta dake jini tace "my abdool soyayyanka yasa na aikata komai, bansan yadda zanyi ba my Abdool, idan ka tafi ka barni wallahi zan kashe kaina, na yadda ka tsaya kamin duk wani hukuncin da kaga ya dace dani, na yadda ka kasheni Indai a hanunka zan mutu bazan juri ganinka da wata ba"
kafanshi ta rike ta ɗaura kanta a kafarshi tana wani irin ɗan marayan kuka, yana tsaye shima hawaye yake, tace "dan Allah abdool, dan Allah, dan girman Allah kada ka tafi zan mutu, soyayyanka zai kasheni zuciyata zata tarwatse, wallahi na yadda ka kasheni kafin ka tafi zaifi min kwanciyan hankali"
yadda take magana babu karya ko kaɗan duk abinda take faɗa daga zuciyanta yake fitowa, Abdool yasan irin zazzafan soyayyan da take mishi shiyasa yakeso ya tafi ya barta yasan zatafi jin zafi fiyeda komai da zaiyi mata, janye kafarshi yayi yaja luggage ya fara tafiya, kanta ta ɗago daga kasan, idanunta sun koma kamar jan gauta sun kumbura sosai, gashinta zuwa yanzu sun barbaje sun zubo har suna rufe mata fuska, ga jinin dake zuba daga kanta yana sauka goshinta, ga bakinta dake jini sakamakon marin da yayi mata wanda tunda ammi ta haifeta bata taɓa jin azababben mari irinshi ba, da wani irin mugun gudu ta shiga ɗaki ta fito da bindiga karami a hanunta, yanasa hanu akan handle na kofa zai fita tace "Abdool"
bai juyo ba tace "kalla zan kashe kaina da wannan bindigan dana siya da sunanka, idan na kashe kaina mutane biyu ne za'ayi zarginsu kai da kuma ammi, to amma nasan ammi zata tsira sabida itace ta haifeni ba zata kasheni ba, kai kuma fa? ba zaka tsira ba domin na siyi bindigan da sunanka tun ranan da naga ka fara gane halina, kasan taya akayi na siya? to ai kwaya nasa maka a ruwa ranan da dare ka fita a hayyacinka kafin na baka takaddu guda biyu kayi sign, kasan bindiga nawa na siya da sunanka? bindiga biyu kasan ɗaya yana wajen waye?"
murmushi me sauti tayi sannan tace "kalli nan"
a firgice ya kalleta, video ta nuna mishi na wata mata a ɗaure cikin wani ɗaki me duhu tace "kasan wacece wannan?"
ganin ya kasa magana yana kara kallon video da yaga kamar Anty ce, tace "wannan ai maman ameesha ce, da zaran ka fita kafin na mutu zance musu su kasheta su aje gawan a fili tareda bindiga kasan za'a fara bibiyan waye ya siyi bindiga daga nan sunanka za'a gani, nima ina nan ina kwance na zama gawa kuma ga bindiga a gefena ana dubawa kuma sai aga kaine ka siyi bindiga, daga nan kasan me za'ayi?"
hotonshi ta nuna mishi a cikin wayarta an rubuta WANTED ajiki tace "za'a fara manna wannan hoton a kowane bango da akasan yana cikin nigeria, sannan a social media ko ina za'a raba hotonka ana nemanka duk wanda ya sameka za'a bashi babban kyauta, kasan me ameesha zatayi?"
wannan karon dariya tayi sosai ganin Abdool jikinshi yana mugun rawa harma ya saki luggage ɗin, tace "ameesha itace zata fara tsananka sabida kaga wannan text ɗin dana rubuta?"
nuna mishi tayi tace "hmm bari na karanta maka, cewa nayi Abdool shine ya kashe mamanki yace saide ku duka ku zauna babu iyaye domin nace mishi ta sadakinki ne ummanshi ta mutu shiyasa ya sace mamanki"
tace "koda na mutu akwai mutane biyu dana basu wannan text ɗin nace suyi forwarding wa ameesha"
murmushi tayi ganin yana takowa a hankali tace "zaka iya tafiya mr AbdoolRahman haruna lamiɗo".
*Duhu da haske is ₦400 via 8144818849 hauwa shuaibu mapi opay, your evidence of payment via 08144818849*
_jiddah ce...._
managarciya