Kungiyar Cigaban Matasan Najeriya Ta Karrama Wani Mai Son Cigaban Matasa
Shi yasa Kazaure ya samarwa wasu aikinyi jami'an tsaro masu kula da harkar shige da fice ,watau immigration a turance , wanda a halin da ake ciki yanzu suna nan suna karbar horo a jihar Zamfara. Ya ce babu abin da ke kara jefa matasan kasar nan cikin mawuyacin hali kamar rashin aikinyi a kasan nan , musamman matasan da basuda wadanda zasu tsaya masu, wajan samun aiki.
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
Shugaban kungiyar neman hadin kan matasa ta kasa ( United Nigeria Youths) a turance ,,Alhaji Haruna Shehu ya yabawa Alhaji Hamza Ado kazaure bisa ga namijin kokarin da yake yi na son ci gaban matasan Najeriya.
Wannan yabon ya zo ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Abuja, ya kara da cewa yabawa Alhaji Ado Kazaure ya zama dole kama da yadda yake kokarin yaga ya gina matasan kasannan ta hanyar samar musu da aikin yi.
Ya kara da cewa Alhaji Ado Kazaure babu abinda yake ci masa tuwo a kwarya kamar yadda matashi zai gama karatu bashi da abinyi.
Shi yasa Kazaure ya samarwa wasu aikinyi jami'an tsaro masu kula da harkar shige da fice ,watau immigration a turance , wanda a halin da ake ciki yanzu suna nan suna karbar horo a jihar Zamfara.
Ya ce babu abin da ke kara jefa matasan kasar nan cikin mawuyacin hali kamar rashin aikinyi a kasan nan , musamman matasan da basuda wadanda zasu tsaya masu, wajan samun aiki .
Shehu yace da za'a sami mutane irin Alhaji Ado Kazaure wajan taimaka wa matasa ta haujin samun aiki , yace da abubuwa sun zowa matasan da sauki , kuma da an rage yawan bangar siyasa da matasan suke shiga .
Ya kara da cewa yanzu haka kungiyarsu tana bin hanyoyin da ya dace domin ci gaba da samun wadanda zasu yi amfani da damar da suke dashi domin samarwa matasan kasar nan aikin yi.
Don haka shugaban kungiyar ya bukaci shugaban nin yan siyasa da su daina amfani da matasa wajan bangar siyasa, musamman wajan basu kayan maye don kauda hankalinsu saboda idanuwarsu su rufe.
managarciya