Sabon Karin Haraji: Gwamnati Na Aiki Da Doka Da Maslahar Jihar Adamawa---Mataimaki Na Musamman Ga Gwamna

Sabon Karin Haraji: Gwamnati Na Aiki Da Doka Da Maslahar Jihar Adamawa---Mataimaki Na Musamman Ga Gwamna

 

Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan jihar Adamawa a Kafafen Sadarwa Muhammad B. Tukur ya magantu biyo bayan rahoton da jaridar Yola 24 ta wallafa kan batun karin kudin haraji da gwamnatin jihar ke shirin ƙaƙƙabowa, B Tukur ya wallafa a shafin na facebook da harshen turanci ga fasarrar kalamansa.

 
An ja hankalinmu kan batun haraji shanu da ya haifar da cece-kuce a tsakanin al’umma a ‘yan kwanakin nan musamman a kasuwannin kananan hukumomin Mubi da Gombi, gwamnati na aiki bisa tanadin doka da kuma maslahar jihar. Domin kawo cigaba amma makiya sun yi masa karkatacciya kalamai da ba sa fatan alheri ga jihar da gwamnatinsa.
 
Kudaden da ake samu daga masu sayar da shanu a kasuwar shanu ta Adamawa ba za a iya kwatanta abin da suke biya a kasashe makwabta da jahohin da ake gudanar da ayyuka iri daya ba.  ya kuma bukaci jama’a da su yi tunani tare da nuna muradin jihar da ci gabanta a zuciya.
 
Naira 5000 da ake biyan shanu a kasuwa ba a karbar haraji daga masu kiwon shanu a cikin jihar amma kudin shiga ne da ake biyan dillalan da ke shigowa jihar domin sayan shanu, na roki jama’a da su yi watsi da ’yan bogi da ke kokarin tunzura su a kan gwamnati wato aiki dole ne su daidaita kasuwa don inganta rayuwarsu.
 
Gwamnati ta tsara kasuwar shanu mafi kyau a garin Mubi kuma nan ba da dadewa ba za a fara aikin gine-gine, za a yi irin wannan ci gaban a sauran kasuwannin da ke wasu shiyyoyin domin bunkasa IGR na jihar da kuma kawo ci gaba a jihar.