An Yabawa Tsohon Gwaman Zamfara Kan Samar Da Tallafin Shanu Da Shinkafa Ga Ƙungiyar Kiristocin Jihar Zamfara
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara mai biyayya ga tsohon Gwamna Hon. Abdulaziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara) ta yaba da kokarinsa na farantawa Al'umma rai a dukkan yanayi duk kuwa da cewa ya shafe kimanin shekaru 3 baya aiki.
Shugaban Jam’iyyar, Hon. Lawal M. Liman Gabdon Kaura ya yi wannan yabon ne a ranar litinin a lokacin da yake gabatar da tallafin Kirsimeti na bana da tsohon gwamnan jahar Zamfara ya baiwa kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, da yan kungiyar Igbo mazauna jihar Zamfara, da kuma kungiyoyin yarbawa da Ibo masu goyon bayan jam'iyyar anan wani garin Gusau.
Sakataren Jam’iyyar, Hon. Sani Musa Talata Mafara ne, ya wakilci shugaban inda ya bayyana cewa al’ada ce tun lokacin da tsohon Gwamnan yake kan karagar mulki, inda ya kara da cewa hakan ya ci gaba da rike shi har bayan shekaru 3 da barinsa.
A cewarsa, Gwamna Abdulaziz Yari Abubakar da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar sun ci gaba da tallafa wa jama'a, inda ya kara da cewa a lokacin da aka fara azumin watan Ramadan na kowace shekara, da bukukuwan Idil Kabir da Mauludi an bada tallafin hatsi iri-iri, Tufafi, Shanu da Raguna, Tsohon Gwamna da Manyan masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar ne suka baiwa Al’ummar Jihar a dukkan mazabu 147 da ke kananan hukumomi 14 na Jihar domin a rage wa jama’a kuncin rayuwa.
Hon. Lawal M. Liman ya ci gaba da cewa, jam’iyyar APC a halin yanzu tana bukatar Gwamna Abdulaziz Yari Abubakar a matsayin shugabanta na kasa saboda girmansa, sadaukarwa, cancantarsa da kuma iya salon mulki domin samun ci gaba.
Shugaban ya ce sabanin abokan hamayyarsa wadanda ba jin dadin Jama’a ne ke gaban suba ,kawai sune son cimma burinsu na son rai, tsohon Gwamnan ya yi duk mai yiwuwa don ganin ya samu sauki da ga ‘yan kasa.
Da suke karbar tallafin, Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya CAN, Rev. Iliya Tsiga, Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Igbo, Cif Emmanuel Anokwuru, Shugaban kungiyar Igbo APC na jihar Zamfara, Mista Collins Ofodile da Shugaban kungiyar Yarbawa ta APC reshen jihar Zamfara. , Mista Ishaq Lawal sun ce basu san irin godiyar da zasu wa tsohon Gwamna Hon. Abdulaziz Yari Abubakar ba, ata bakin su, kamar yadda ya saba, dabi'ar sa ce irin wannan al'ada tun lokacin da yake shugaban cin jihar ta Zamfara.
Sun yi alkawarin dawwamar da Addu’o’insu na ganin an dawo da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban kasa baki daya.
A wajen taron, kungiyar Kiristoci ta CAN ta karbi buhunan shinkafa 400, Shanu 10 da Naira miliyan daya, kungiyar al’ummar Igbo buhu 40 na shinkafa da shanu 2, APC Yoruba Wing buhu 20 na shinkafa da saniya 1 yayin da APC Igbo Wing. ta samu buhunan shinkafa 40 da shanu 2.
managarciya