HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta 41

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta 41

   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 



          Page 41

Cikin sanyin jiki ta aje wayarta ta koma ta kwanta tana jin tamkar ba ita ba. Ji take tamkar rayuwarta ta baya ba ita ce tayi ta ba, baki ɗaya komai sai yake zuwa mata tamkar a mafarki ko a wani littafi da take karantawa.

       Lumshe idonta tai tana hango yadda Mustapha ke marairaicewa yana nuna tsantsar kulawa da ita da duk abin da ya shafe ta, tana lura da yadda yake yawan kallonta yana murmushi yana girgiza kansa alamar yana cikin farin ciki da nishaɗi a duk lokacin daya ganta.  Ita kam tasa a ranta ta gama soyayya haka zalika ba zatai aure ba duk dan wasu shekaru biyar zuwa goma masu zuwa, amma ga shi kai tsaye abin mamaki abin al'ajabi ta amsa ma Mustapha da bakinta cewar tana sonsa, kenan tana shirin komawa a fagen masoya a karo na biyu a rayuwarta kenan? Hakan na nufin ta manta da abin da Abubakar ya yi mata kenan na cin amana da muguwar yaudara? Gaskiya batai ma kanta adalci ba amsa soyayya da tai kai tsaye batare data tuna baya ba kota ji kishin abin da Abubakar ya yi mata ba ta amsa ma Mustapha cewar tana sonsa.
Shin wai ma ya zatai da tarin matansa ne duk da ya ce mata yanzu matansa biyu ne? Ita fa bai kamata ace ko aure zatai ba ta auri mai mata ba, kamata ya yi ta auri wanda bai da mata wanda zata zauna ita kaɗai a gidanta sai mijinta su yi rayuwa mai cike da soyayya da kula da juna, amma idan tace zata auri mai mata tabbas ba zata samu damar cika burinta ba na yin soyayya da rayuwar farin ciki a gidan aurenta ba, ta sani sarai yadda wasu matan ke hana amarya rawar gaban hantsi a cikin gidan aurenta suna cewa ta zo da rayuwar banza zata lalata masu tarbiyyar yara daga an fara maganar shike nan sai komai ya zama tarihi na rayuwar farin cikin. Ita kuma ta jima da tsarawa kanta irin rayuwar auren da zatai indai zatai aure da gaske to sai dai ta auri wanda zasu maida tsakar gidansu tamkar filin wasa inda za su sakata su wala su dinga saka kaya ƙanana masu ɗaukar hankali suna wasan zagaye gidan suna komai tare irinsu wanke-wanke da wanki da girki ya zama komai zatai tana jikin mijinta suna yi tare suna firar soyayya suna ba juna nishaɗi suna faranta ran juna. Idan kau haka ne ai bai kamata ta amsawa Mustapha ba cewar ta amince da soyayyarsa ba tunda yana da mata yana da yara kenan ba zai iya bata irin kulawar da take buƙata ba. Ta sake gyara kwanciyarta sosai tana hasko yadda ma lamarin zai wakana a tsakaninsu da matansa.

Afnah ce ta shigo da gudu tana sallama tace ta je ana kira inji Baffa haka suke kiran maigidan su duka don haka ake kiransa.

A hankali ta tashi ta fice tana tunanin ko Kano zai je ne yasa yake kiranta ko tana da saƙo. Tana sallama ta sha jinin jikinta domin ganin Kawu Mansur zaune yana latsa waya yasa ta fahimci inda kiran yake da ma'anarsa.

Cike da natsuwa ta ƙarasa ta fara gaida shi sannan ta zauna ta sadda kanta ƙasa bata da ta cewa kuma sai jiran abin da zai ce mata kawai.

Kawu Mansur da sai kallonta yake gani yake ta ƙara kyau ganinta yake tamkar ba ita ba, ganinta yake tamkar an sauyo ta batai kama da wadda ta aje yara har uku ba, tafi kama da budurwa ƴar jami'a mai karatu a matakin farko.

Bayan ya gama kalle ta yana ta jin nishaɗi tare da jin cewa yafi kowa dace da samun mace a rayuwarsa ya samu da ƙyar ya saita kansa ya ce mata, "Ranki ya daɗe nasan ba za ki yi mamaki ba don kin ganni ba a gidanku, saboda ke ba yarinya bace ba, kuma dama can ban ƙasa a gwiwa ba sai da na bayyana maki abin da ke ƙasan zuciyata game da ke, na yadda kika sace min zuciya kikai min fashin duk wani kuzari da jin daɗi na rayuwata ta hanyar cusa min tsumin ƙaunarki a jinin jikina Jiddah. Ina so ki sani wallahi ba ki bina bashin rantsuwa amma ban taɓa ganin yarinya ko kamuwa da soyayya ba farat guda irin yadda na kamu da taki soyayyar daga ganin farko da nayi maki a kotu ba. Jiddah ki sani cewa ba komai ba ne a tarenmu illa HAƊIN ALLAH saboda shi ne kawai ya haɗa mu a lokacin da nake niyyar yanke wa ƙanwata hukuncin da bai kamata ba nasa son zuciya da son abin duniya a lokacin idanuna sun rufe an ban kuɗi na aje komai na manta koni waye na manta yadda nayi alƙawarin zan yi adalci zan guji rashawa da cin hanci a kan aikina, sai gaki a lokacin da babu wani tsoron Allah ko jin nadamar abin da zan aikata kika juya min zuciyata daga kallo guda ɗaya na sauka daga layin dana hau na cin amanar aikina na koma na daidai wanda ashe alheri ne hakan a gareni saboda ƴar'uwata ce ashe a gabana ban sani ba. Jiddah don Allah ki sake taimakona a karo na biyu ki sake ceto zuciyata daga irin son da take maki mai cike da tsabta da nagarta." Ya yi shiru yana kallonta don jin me zata ce.

Jiddah da take jin tamkar duk an ɗaure mata duk wata jijiya ta jikinta ta buɗe bakinta da ƙyar tace, "Na gode sosai kuma na fahimce ka Kawu amma sai dai don Allah ina son kai haƙuri ka bar wannan maganar saboda Ni ba aure ne a gabana ba yanzu, asalima so nake na cigaba da karatuna saboda ina da sha'awar yin karatu mai zurfin gaske a rayuwata ko don yarana idan sun girma su yi alfahari da hakan. Don haka nake baka haƙuri don Allah Kawu Mansur kar kai mun mummunar fahimta don Allah." Hawaye suka zubo mata domin sai taji zuciyarta ta kare sosai.

Shima sai ya ji jikinsa ya yi sanyi sosai, matarsa dake laɓe tai murmushin mugunta ta ji har a ranta zata taimakawa yarinyar don ganin ta samu abin da take buƙata na rayuwa don dama taji matuƙar tausayin yarinyar ranar da taji labarinta kawai kishin mijinta ne yasa ta binne tausan a ƙasan ranta. Cike da ƙaunar Jiddah ta koma gidanta ba tare da taji me mijinta zai ce ma jiddar bama.

Muryarsa irinta masu karaya ya ce mata, "Shike nan Jiddah zan ƙyale ki a yanzu na baki lokaci ki yi karatu ki yi duk abin da kike amma ki sani ina sonki kuma idan ke ɗin rabona ce nasan zan sameki insha Allah. Ina maki fatan alheri kuma ko da yaushe ƙofar taimakona gareki a buɗe take Jiddah ke da yaranki." Ya tashi ya fice yana jin kamar ya yi kukan shima.

Nan ta zauna ta ci-gaba da kukan da bata san ko na me ye ba, har taji muryar Baffa kanta yana cewa, "Haba Jiddah ba kuka ya kamata ki yi ba tunda ya fahimce ki sai ki gode wa Allah ai ba ki zauna ki kama kuka ba. Ina jiranki ki kawo min takardunki da sunan makarantar da kike son zuwa naga yadda za ai." Ya kama hannun Afnah suka haye bene.


Alawiyya sai yamma ta sauka gidansu Jiddah saboda jin haushin ƙin amsa mata waya da tai kuma ta kama waya ta kashe yasa Alawiyya yi mata zuwan bazata don ta yi wa mijinta kamun ƙafa saboda ta gaji da yadda yake rayuwa a wahale ya takura kansa ya takura wa su dake tare da shi hatta yaransu ba wanda yake kulawa sai Jiddah ita ma tasan saboda mai sunanta yake kulata. 


Tana shiga ba kowa a gidan ga alama don haka tai nufin shiga sashen Jiddah ta watsa ruwa ta kwanta kafin su dawo ta ɗan huta da gajiyar tafiyar da tai.

Sai dai tana zuwa ta iske Jiddah kwance tamkar tana barci sai ajiyar zuciya take alamar ta ci kuka ta gode wa Allah.

A hankali ta isa gabanta ta ɗora mata hannu kan fuskarta ta ambaci sunanta a hankali.
Jiddah ta buɗe idonta ta ɗora su kan fuskar Alawiyya sai kawai ta ƙwaƙwume ta sosai ta fashe da kuka sosai.
Ita ma Alawiyya dama zuciyarta tuni a karye take don haka sai ita ma ta fashe da kuka ba mai lallashin wani a tsakaninsu.

Jiddah ce cikin kuka take cewa, "Wai me yasa ne rayuwata ba zata gyaru ba? Me yasa har zuwa yanzu na kasa samun natsuwa kamar kowace mace? Me yasa ne wai na kasa yin farin ciki har yanzu?"


      Alawiyya ita ma cikin kukan take cewa, "Kar da kice haka don Allah Jiddah ke ɗin ta musamman ce nasan dole sai kin ga abubuwa masu dama na musamman kema kafin komai ya zama tarihi a gareki. Shin Jiddah baki da labarin cewa sai macen da takai mace maza kamar irinsu Faisal da Mustapha ke cewa suna so? Baki da labarin cewa sakayya ce tasa maza ke kwana da tashi da ciwon sonki ? Na rantse maki da Allah ban ji komai ba dana fahimci Babansu Anam na sonki sai farin ciki da nayi da jin daɗi saboda nasan duk gidan da kika shiga sai ya yi albarka sai kwanciyar hankali ta yawaita da jin daɗi don haka nake kwana taya mijina addu'ar Allah Ya mallaka mai ke a matsayin mata, kinga kenan ba za mu sake yin nesa da juna ba zamu rayu a waje guda gida guda ƙasan miji guda Jiddah.
Amma kar ki ɗauka dole zan maki Jiddah ina so dai ki yi tunani ki nazari a tsakanin Mustapha da Faisal ki zaɓi guda domin na yadda da son da kowane daga cikinsu ke maki."

Jiddah ta janye jikinta daga na Alawiyya ta koma can gefen gadon ta raɓe  tana gunjin kuka tace da ƙarfi. "Me nayi maki da zafi ne da har kike min wannan maganar? Me yasa kike son kunyata ni tare da ci mun fuska ne Alawiyya? Ashe akwai ranar da kishi zai sa ki yi min wannan kallon? Kin manta da cewa Ni dake a Uwa ɗaya Uba ɗaya muka rayu haka kuma muke cigaba da rayuwa ne? Alawiyya ina hankalinki da tunaninki yake ne da har suka barki ki kai min wannan mummunar fahimtar? Kin ban mamaki Alawiyya ban taɓa tunanin za ki min haka ba ko a mafarki na gode sosai ba mamaki don ina zaune a gidanku ne yasa ki kai min haka amma ba komai zan koma namu gidan ko da kuwa ace ban da shi zan nema." 

Alawiyya ta daskare a gun ta kasa ko ɗaga halshenta tana ganin Jiddah ta ɗauki hijabinta ta fice daga ɗakin tana kuka sosai.

Itama kukan ta saka tana jin me yasa tai ma Jiddah maganar ne? Ga shi nan ta kasa fahimtar ta ai har ta yi tunani na daban kan lamarin. 

Jiddah na fita ta leƙa ɗakin mai aikin gidan tasan su Afnan na can na wasa ta tarkata su kai tsaye tasha ta nufa ta hau motar Kano tana rungume da yaranta tana kuka mai sauti wanda yasa su ma yaran kama yin kukan, kowa na motar na kallonsu ba mai bakin yi mata tambaya don duk wanda ya ganta zai fahimci mutuwa ce kawai akai mata tasa ta a wannan yanayin.

Har suka isa Kano bata daina kuka ba, napep ta hau har ƙofar gidan Hajjo, zuwa lokacin ta daina kukan sai dai kallo guda zakai mata ka fahimci ta ci kuka bana wasa ba.

Yana zaune yana tunanin gobe ba bin da zai hanashi zuwa Kaduna kafin ya wuce wajen wata kwangilar aikin da ya samu sai ga napep ta tsaya ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin Jiddah a cikin mugun yanayi ba, kallo guda ya fahimci ta fi awa huɗu tana kuka kuma damuwa ce fal ranta , tabbas akwai abin da akai mata mai girma daya sa ta zo tun daga Kaduna har Kano a cikin wannan yanayin. 
Yana kallonta ta ba mai napep ɗin dubu ɗaya yana magana ta ɗaga mai hannu ta ja yaranta suka shige cikin gidan ko waigen mai napep ɗin batai ba.
Tsab ya tashi shima ya bi bayanta gabansa na faɗuwa sosai da sosai, sai ya ji shima duk damuwar ta nannaɗe shi ta ko'ina.
Tana shiga Hajjo na zaune tana duba wata tsohuwar jikka ta Uncle Salim data gani a ƙarƙashin gadonta Jiddah ta faɗa jikinta ta fashe da kuka mai cin rai.

"Hajjo me yasa Alawiyya zatai min haka ne? Akan me zatai min wannan ɗaukar? Me nayi mata ne da zata ce zan iya auren mijinta? Shin nayi kama da mai cin amana ne marar sanin darajar halacci da abota ne Hajjo?"

Hajjo da farko tsoro taji sai daga baya ne ta fahimta sai tai murmushinsu na manya tace, "Shi ne abin kuka Jiddah daga wannan maganar? Na ɗauka ai ke da Alawiyya har abada ba wanda ya isa ya shiga tsakaninku ya rabaku ai? Yanzu ina Alawiyyar take ita?"


Cikin kuka ta gayama Hajjo abin da akai tas.

Kawai samun waje ya yi ya zauna ya dafe ƙirjinsa da yake ji tamkar zai faso ƙirjin ya fito.

Me yasa Alawiyya zatai mai haka ne? Me yasa ta zama mai son kai irin haka? Ba ita ce ta kamata ta so zuwan Jiddah gidanta ba shi ne yake da buƙata gaba da baya na zuwan Jiddah gidansa saboda shike rayuwar aure tamkar ba aure ba, shi ne cike da baƙin cikin rayuwar aure da takaicin rayuwar auren baki ɗaya don haka Allah Ya kawo mai maslaha ta hanyar kawo Jiddah a rayuwarsa a karo na barkatai.
Hawaye suka zubo mai bai damu da gogewa ba ya samu da ƙyar ya taka ya isa inda take kife tana kuka jikin Hajjo ya dafa bayanta ya ce, "Jiddah me yasa ne Ni ko da yaushe nayi hangen samun sauƙi a rayuwar aurena sai naga ya faskara? Jiddah me yasa Alawiyya ke da son kanta da yawa ne? Don Allah ki taimaka min ki yi min alfarmar aurena don na samu ko da rabin farin cikin da nake gani da mafarkin samu ne a wasu gidajen Jiddah. Na rasa me yasa ke kaɗai ce nake ji a jikina cewar waraka ga baƙar rayuwar da nake mai cike da tauye haƙƙi da zalunci ba Jiddah. Don Allah Jiddah ki amince min ki yadda da Ni kar da ki bari a rabani da ke wallahi zan shiga mugun yanayi mafiyin wanda nake a ciki Jiddah." Kuka yake sosai tamkar ƙaramin yaron goye.

Hajjo sai abin ya bata tausayi sosai itama domin dai tasan wasu abubuwan dake faruwa na gidan Mustapha ɗin amma kuma bata da abin cewa saboda dai faɗan da ba ruwanka daɗin kallo ne da shi aka ce.

Mustapha ya sake janyo Jiddah jikinsa ko'ina rawa yake tsabar tashin hankali da shiga ruɗu ya ce, "Princess don Allah ki tuna da cewa kin amince min da kanki kin amsa min cewa kina sona don Allah ki taimaka min to ki yi iyakar yinki gun korar duk wata katanga da zatai mana gicci a soyayyarmu Jiddah."

Hajjo ta miƙe tsaye ta kama hannun yaran da su kai cirko-cirko suna jiran kaɗan sui kuka suka shige ɗaki.

Jiddah ta janye jikinta tana son ta tashi ita ma ta bi su Hajjo ɗakin Mustapha ya kama hannuwanta ya tsugunna ƙasa ya ce, "Don darajar Allah Princess kar da ki zama silar lalacewar rayuwata! Tabbas idan kika ƙi Ni ban san wane irin gararin rayuwa zan faɗa ba, idan kika kasa amsar soyayyata ki ka aure Ni ba, kada ki yi mamaki idan aka ce maki an ganni na koma shaye-shaye ko na haukace duk ba wanda ba zai iya faruwa ba idan kika barni Jiddah."

Cikin kuka ita ma tace mai, "Na rasa ya zan da kaina baki ɗaya kun saka Ni a halin ha'ula'i ban san waye zan ɗauka ba ban san waye zan duba lamarin soyayyarsa ba, don Allah ku ƙyale Ni haka nan na jima da daina soyayya baki ɗaya a rayuwata."

Da ƙarfi ya ci-gaba da girgiza ta yana kuka yana cewa, "Ba ki min adalci ba idan har kika sakani a cikin jerin waɗanda ke sonki a yanzu kin cutar da Ni domin baki min adalci ba sam, yadda nake sonki tun kafin kisan miye so, nake ƙaunarki tun kafin kisan mece ce soyayya nake sonki don Allah ki daure ki amshi soyayyata Princess wallahi ke ce duniyar soyayyata kece wadda nake mafarkin samun natsuwa da aurenmu don Allah ki agaza min ki ji tausayina ki share min hawayen idanuna ki wanke min zuciyata daga dattin dake kewaye da ita Princess don darajar Allah kar da ki barni na lalace ki ji tausan yarana iyayena don Allah Princess."

Bata da yanda zatai da shi ta amsa mai har cikin zuciyarta tana sonsa, saboda samun wanda zai maka soyayya irin wannan tabbas ya cika masoyi haka yasan me yake kuma ba son yaudara ko ƙarya yake maka ba. Don haka tai ajiyar zuciya ta dube shi tace, "Kai min alƙawarin cewa zaka sauya daga duk wani halin rashin kirki naka, haka zalika zaka zama mai min adalci tsakanina da matanka, sai magana ta ƙarshe ba zan zauna da matanka ba, zaka aje Ni gidana daban kai min alfarmar zama gidana har abada ba tare daka haɗa Ni da matanka ba, to tabbas zan aure ka idan kuma zaka cigaba da nuna min soyayya tamkar yadda kake nuna min ita a yanzu domin soyayya a jinina take ban jin daɗin zaman aure babu soyayya ba zan iya juriya ba a wannan lokacin zan iya sake waje kan rashin kulawa."

Rumgume ta ya yi yana saukar da ajiyar zuciya, natsuwa na ratsa shi ta ko'ina, ji yake ya samu natsuwa da kwanciyar hankali mai ɗorewa tunda Jiddah ta amince da soyayyarsa. 

Cikin farin ciki yake ce mata, "Na gode sosai Princess insha Allah zan cika maki dukkan wani burinki zan zama mai share maki hawayenki, ba makawa alƙawarinki zai zama abin riƙe wa gareni har abada."

A hankali ta zare jikinta daga nashi tana jin tamkar ta sauke wani babban nauyi da ya danne mata zuciya, sai ta ji duk wata damuwa ta fice daga cikin zuciyarta.

Zaman dirshan ya yi gabanta yana ƙare mata kallo cikin zuciyarsa yana gode wa Allah daya azurta shi da samun mace kamar Jiddah matsayin matar aure.
Ita ma kallonshi take ƙasan ido tana ganin yadda yake da kyau na daban komi na shi ya yi mata, ga shi ɗan gayu ko da yaushe ƙamshin turarensa ke bayyana zuwansa waje tun kafin ya zo wajen, gayunsa na birgeta tana son miji ɗan gayu wanda ko da yaushe yake cikin tsabta da ƙamshi kamar dai yadda Mustapha ya kasance. Hancinsa ta kalla yana da dogon hanci wanda ya fi nata sosai tsawo, ga shi da idanu masu kyau fuskarsa Masha Allah komai ya yi mata yadda take buƙata. Babban abin da ya sake tafiya da hankalinta wushiryarshi babba mai ƙara mai kyau idan yana dariya, ita kanta sautin dariyarsa abin tsayawa ce a ranta, murmushinsa na matuƙar birgeta tabbas ita ma tana sonsa ba yanzu bane ta fara sonsa ba kawai dai bata maida hankali bane da ta gane ita ma ta kamu da sonsa.

Sai ga su suna ta tsokanar juna kowa na jan kowa, suna ta dariya tamkar ba sune ba suke kuka yanzu ba cikin damuwa da tashin hankali ba.

Mustapha ya dube ta ya ce, "Princess wai ya naga sai wani kallona kike ne hala kin ga ɗan mummuna ne."

Tai dariya sosai tace, "Anya kuwa an taɓa gaya ma kana da kyau kuwa Prince?"
Yana murmushi ya ce mata, "Kawai dai ki ce min kin lura da muni na kawai Malama."

Tana murmushi tace, "Kasan wani abu kuwa Prince? Allah ka fini kyau sosai prince kana da hanci gaka da fararen idanu ga fuskarka siririya daidai misali gaskiyar magana ka dinga gode wa Allah daya azurtaka da kyawu na gasken-gaske ."

Yana murmushi yana kallonta wai Princess ce ke cewa yana da kyau har ya fita kyau? Tabdijam! Shi da yake lalata yini guda wajen tunanin irin kyawunta da dirinta wanda babu wanda zai kalleta bai so ta zama abar mallakarsa ba. Jiddah na da kyau na gaske wanda kallo guda ma kana iya fahimtar yadda Allah Ya azurta ta da kyawun jiki dana fuska.

Kallonsa tai ta taɓe baki tace, "Ka tashi ka tafi gidanka kar da a zo nemanka ba ruwana."

Kallon kin cika rigima ya yi mata ya sadda kansa ƙasa don bai san abin da zai ce mata ba kan maganar da tai mai, ya lura ita ma zatai kishi amma yana fatan tai kishi irin na ƴan boko wanda ya halarta bana hauka ba wanda matan yanzu ke yi ba.

Ganin ya kasa bata amsa yasa tai murmushi tace, "Na baka tsoro hala, na tuna maka da matanka?"

Baice mata komai ba dai sai murmushi da ya yi don ya lura Princess dabance ko a jerin matan.
Sai taji itama kamar ta zaƙe da yawa don haka sai ta sauya zancen da cewa, "Allah ka je gida kai wanka ka ci abinci domin na fahimci baka ci komai ba kana tare da yunwa."

Girgiza kansa ya yi alamar bai jin yunwa. Itama girgiza kanta tai alamar yana jin yunwa fa da gaske take.

Daɗi ya ji sosai a ransa yadda Princess ke fahimtar abin da ke damunsa kai tsaye na nufin ta damu da shi sosai.
Tabbas yunwa yake ji ya kasa cin abincin ne saboda sam bai masa ba, yana son jin abinci mai daɗi a bakinsa sosai yake son daɗi amma ya rasa yanda zai koman ya kawo mai daɗin ba a san yadda za a sarrafa mai shi ba ya bada abu mai ma'ana ba, don haka yafi son cin abincin kan titi  da ya ci abincin gidansa.

Ko da yake mutane nayi mai mummunar fahimta kan hakan har ma wasu na cewa ai yana siyen kayan abinci mai daɗi yana ɓoyewa a ɗakinsa bai iya ba matansa sai dai su ya barsu da tuwo da tsakin shinkafa ko da yaushe, shi kaɗai ke cin daɗi a ɗakinsa ba ruwansa da matansa da yaransa, sosai abin ke ƙona mai rai duk lokacin daya tuna abin ji yake ransa ya ɓaci sosai har ya ji ya tsani aurenma baki ɗaya.

Jiddah lura da tai ya yi zurfi a tunani daga maganar wasa sai taji bata ji daɗin hakan ba, don haka ta dube shi fuska cike da shagwaɓa tace, "Prince shi ne ina maka magana za kai banza ka ƙyale Ni ko? Gaskiya Ni ba zan yadda ba." Magana take cike da shagwaɓa abin da yake matuƙar so kenan a rayuwarsa yaga mace na yi mai shagwaɓa abin na bala'in birge shi sosai, don haka sai ya samu kansa da manta halin da yake ya saki baki da hanci yana kallon yadda take mai shagwaɓa abin birgewa.

Samun kansa ya yi da lallashinta tamkar wata ƙaramar yarinya haka ya dinga lallashinta  yana jin shauƙi sosai na ratsa dukkan jikinsa na ƙaunarta.

Haka suka kwashe tsawon lokaci suna kwasar soyayya inda Jiddah ta dinga zuba mai shagwaɓa yana biye mata abin nayi mai daɗi har dai Hajjo ta gaji ta leƙo tace basu ji an kira sallah bane ba? Kan dole suka tashi ba don ransu na so ba ta raka shi har zaure, a can ma sai suka sake buɗe wata sabuwar firar suna ta dariya suna jin farin ciki tamkar karda su rabu.

Mustapha ya kalli Jiddah kallo na so da ƙauna ya ce, "Allah ji nake tamkar na sace ki kowa ma ya huta Princess. Kinga yadda ki ke da bala'in kyau kuwa wai? Allah duk wanda ya sameki ya yi dacen mata ta nunawa a cikin jama'a a baka lambar yabo."

Sadda kanta ƙasa tai tana murmushi tace, "Kai fa don baka ganin kanka ne kawai yasa kake cewa ina da kyau, amma nesa ba kusa ba ka fini kyau gaka ɗan kyakkyawan gaske uwa uba gaka ɗan gayu, gaskiya ina matuƙar ƙara gode wa Allah da Yasa na sameka a lokacin da sam ban zata ba, lokacin da ban taɓa tsammanin zan samu kamar ka ba Prince."

Ajiyar zuciya ya yi yana murmushin dake ƙara masa kyau ya ce mata, "Wallahi Princess har mamakin kaina nake akan ki baki ɗaya komai nawa ya sauya tun daga kan wasu daga halayena da tabi'una duk sun sauya saboda soyayyarki don darajar Allah ki amince ki ci-gaba da tafiya dani cikin rayuwarki, sannan ki dinga ban shawara kan duk abin da kika ga ban daidai ba don haka shi ne soyayyar gaskiya."

Cike da fara'a tace, "Tabbas naji daɗin maganarka amma don Allah Prince kaima ka dinga gayamin gaskiya kan dukkan abin da ya shafe Ni zan murna da hakan sosai da sosai."

Wayarsa ya kalla yaga yanda lokaci ya ja sosai don haka ya kalleta kamar zai kuka ya ce, "Princess zan tafi nayi sallah naga lokacin ma sauri yake ko dan yaga muna tare ne yasa yake sauri Yau oho."

Da ƴar dariyarta ta amsa mai da cewa, "Shike nan Prince ka je kawai Allah Ya tsare min kai Yasa ka kasance cikin farin ciki da natsuwa Ya buɗa maka dukkan ƙofofin alheri."

Farin ciki fal ransa ya dinga amsa mata da "Amin Ya Allah Princess." Abin yana birgeshi daman ya ji ana mai addu'a sai ya ji yafi kowa samun dace da macen kirki.

Haka suka rabu suna ɗagawa juna hannu kowa fuska cike da annurin jin daɗi.


Jiddah na komawa taga miss call na Alawiyya dana Baffa har dana Maman Alawiyya ba adadi don haka ta fara kiran Baffa don jin abin da ke faruwa.

Cike da dattaku yake maganar, "Ɗiyata kina ina ne tun ɗazun nake nemanki cikin gidan nan baki ba jikokina?"

Sai a lokacin taji cewar bata kyauta ba, don kawai Alawiyya sai ta bar gidan ba sallama? Amma ya zatai hakan shi ne daidai bata san ko da wasa Alawiyya ta ɗauka cewa tana son mijinta don haka ta bar gidanma baki ɗaya.

Cike da jin kunya tace mai, "Baffa ina Kano ai."

"Kina Kano fa kika ce? Me ake yi ne a Kanon da kika tafi ba sallama Jiddah?"

Hawayenta suka dawo don haka sai kawai ta fashe da kuka tace, "Baffa Alawiyya ce wai tace ... Kuka ya hanata magana don haka tai shiru tana jan majina.

Baffa yai murmushi ya dubi Alawiyya dake zaune gabansa tana ta kuka ita ma ya girgiza kansa ya ce, "Saboda hakan kika bar gidanku kika tafi Jiddah? Yanzu kin kyauta min kenan da za ki yi fushi ki kwashe min jikoki kibar gida? Me nayi maki Ni to?"

kukanta ya ƙara ƙarfi sosai ta cigaba da ba shi haƙuri tabbas tayi laifi mai girma amma ranta ne ya ɓaci ta rasa abin da zatai don haka taga dacewar barin gidan kawai, don haka ta bar gidan tare da yaran cikin tashin hankali.

Baffa ya jima yana mata nasiha ya ƙare da cewa, "Ki kwantar da hankalinki babu wanda ya isa ya yi maki dole kan aure ko zaɓar mijin da za ki aura ɗiyata sai wanda kike so ya kwanta maki a rai shi ne kawai wanda zan ba aurenki amma duk na yi maki iyaka da su baki ɗaya harma da Mansur ɗin babu wanda zai sake takura maki don haka gobe ki dawo gida na kammala maki komai na karatunki ranar Monday za ku fara karatu, ki yi haƙuri da abin da ƴar'uwarki tai maki bata kyauta ba, kin san yadda mu ke mu maza ba ruwanmu da cewar waccan macen idan na aureta akwai kunya ko wani makamancin haka, ku mata kune kukasan kunya kan aure banda maza basu da kunya kan mace."

Sai a lokacin ta tsaida kukanta ta gode mai tace gobe suna hanya ita da yaran insha Allah.

Bayan tai sallah ta kira Maman Alawiyya ita ma dai kan tafiyarta ce tai mata faɗa sosai tace maza ta koma gidansu gobe kar ta sake jin irin wannan ya faru tabar gidan Baffa.

Itama haƙuri tai ta bata har ta sauko suka gaisa sosai ta ƙara da yi mata nasiha sosai suka gaisa da Haidar ta kashe wayar ta kwanta tana jin tamkar an ɗauke mata nauyi.

Tun suna waya da Mama take ganin kiran Alawiyyar na shigowa wayarta ta share har ta gama wayar tana ta kiranta amma ta ƙi ɗaga kiran, don har ga Allah taji haushin abin da Alawiyyar tai mata wai ta zaɓa mata  mijinta matsayin mijin da zan aura akan me to? Kenan tana nufin zan iya kishi da ita har wata rana su yi faɗa abin kunya kenan ya tabbata ace sun yi faɗa kan namiji kuma tasan indai zata auri Faisal wata rana sai ɗaya ta ga laifin ɗaya. Don haka zata nuna mata kurenta ta hanyar kulle ta kwana biyu.

Cikin dare online ta hau suka haɗu da Prince ɗinta suka dinga amayar da ruwan ƙauna kowa ya fito da ciwon da ke kwance a ƙasan ransa kan soyayya,anyi aman kalaman ƙauna anyi ma soyayya fata-fata kamar wasu sabbin amare ranar farko haka suka raya daren da nuna ƙauna ga juna ta hanyar bayyana abin da ke cikin zukatansu.

Wajen ƙarfe uku na dare sukai bankwana ba dan sun gaji ba sai don gobe zatai tafiyar safe wanda shi ne zai kai su tasha su hau mota da safen.

Ko bayan sun bankwana kowane kasa barci ya yi sai ajiyar zuciya da karanta saƙon nin juna da sukai.

Jiddah bata ankara ba sai jin kiran Sallah tai, abin ya bata mamaki ƙwarai yadda ta kwana ido biyu kan soyayya ta manta yadda namiji ya ci mata mutunci ya raba ta da farin cikinta yasa ciwon hawan jini ya  kamata ya dasa mata takaici yasa ta fita hayyacinta Yau kuma ita ce namiji yasa ta kwanan farin ciki yasa ta manta komai na baƙin cikin ɗa namiji ya aikata mata a baya. So kenan ba abin da bai sawa yasa ka a farin ciki wani lokacin ya saka a baƙin ciki.

Mustapha na kwance sai godiya yake ga Allah wanda ya nufe shi da fita daga ƙangin rayuwar da yake ciki na rashin samun cikar burinsa na samun macen kirki ta ƙwarai wadda zata iya yi mai duk abin da yake so zata saka shi farin ciki idan yana cikin damuwa haka idan yana cikin nishaɗi zata ƙara mai da shauƙi.

Kasa daurewa ya yi sai da ya kira number abokinsa Ali Ɗangote cikin daren don ya bayyana mai irin halin da yake ci na samun wadda yake mafarki wadda ko da yaushe yake yin zancen ta .
Cikin magajin barci Ɗangote ya ɗaga kiran don yasan ba lafiya ba kira haka cikin dare.

Mustapha cikin muryar farin ciki yake cewa, "Dilla Malam ka kauda barci daga Idonka ka ji wani kyakkyawan labari daga bakina yanzun. Ko kasan cewa Jiddah ta amince da Ni ta ban dukkan soyayyarta har ta amince da maganar aurena?"

Ɗangote abokin Mustapha ne sosai yasan yadda Mustapha ke fama da rigimimar gidansa haka yasan burin Mustapha na auren wayayyar mace wadda ta ƙware a soyayya haka shi ɗin yasan yadda Mustapha ke masifar son Jiddah tun shekarun baya.

Sosai ya taya abokinsa murna don yasan cewa yanzu abokinsa zai samu kwanciyar hankali tunda ya samu abin da yake buƙata .
Jin Mustapha bai da niyyar barci ya kashe wayarsa ya juya ya cigaba da barcinsa duk da yana jin kamar kiran sallar asuba.


Wajen ƙarfe takwas na safe Jiddah ta gama shiryawa ta shiryawa su Afnah don haka ta kira Prince don ya kaisu tasha kamar yadda taima Baffa alƙawarin tafiya da safe.

Suna gama karyawa ya shigo sai ƙamshi yake, idan ba gizo idonta ke mata ba sai taga ya ƙara yi mata kyau har wani haske ya ƙara kamar ba shi ba.

Hajjo ta ƙara yi mata nasiha tai mata faɗa sosai sannan suka fice zuwa tasha.

Suna zuwa suka samu mota don haka ta shiga tana kallon yadda baki ɗaya jikinsa ya yi sanyi idanunsa suka kaɗa  su kai jajir damuwa muraran kan fuskarsa. Ta san itama tana jin yadda yake ji amma ya zatai? Ya zama dole ta tafi ne don haka ta kauda kanta kawai don bata son ta sake karya mai zuciya har itama tata zuciyar ta ida karyewa.

Motarsu na ɗagawa ya fara zubo da hawaye daga idanunsa ya yi sauri ya bada kuɗin motarsu ya haye mashin ɗinsa ya ba shi wuta sosai har saida kowa ya kalle shi.

Jiddah ta sadda kanta ƙasa kawai tana jin yadda bugun zuciyarta ke ƙaruwa tamkar wadda tai gudun gaske.

Motarsu bata jima da tashi ba kiran wayarsa ya shigo mata ta ɗauka tana ɗagawa ta ji ya fashe da kuka yana cewa, "Princess don Allah kar ki tafi ki barni don Allah Princess." Kuka yake sosai wanda sai da taji nata hawayen sun zubo mata ita ma.

Bata da bakin yi mai magana don haka sautin kukansa kawai ke dukan zuciyarta, yayin da hawayenta suka kasa tsayawa don haka ta kife kanta a cinya ta cigaba da kukan zuci dana fili marar sauti.

Sun jima a yanayin kowa ya kasa daina kukan kuma kowa ya kasa magana na tsawon lokaci har sai da yaran suka fara fahimtar abin da ke faruwa sannan tai mai sallama ta kashe wayar ta kife kanta cikin cinya tana saukar da ajiyar zuciya.

Har suka shiga Kaduna bata san sun isa ba, saboda tayi nisa a tunanin soyayyarta da Prince. Bata taɓa tunanin cewar zata wayi gari da soyayyar wani Mustapha ba ɗan'uwa ga Uncle Salim ba, ita bata ma tuna shi ko ta hasko ko da fuskarsa a baya amma yanzu ga shi cikin ikon Allah sun wayi gari cikin ƙaunar juna ta gasken-gaske, ta yarda da cewar haɗuwarsu ita ake kira da HAƊIN ALLAH wadda ba sanin wani ba shawarar wani sai wayar gari kawai da ita su kai.

Komai ya tsaya ma Alawiyya saboda ta lura sosai Jiddah ke fushi da ita, tunda har ta kasa ɗaga mata kira kuma tabar gidan. Kuka take sosai duk da bata lafiya a kwanakin nan amma haka take jurewa don kawai ta samar wa da mijinta natsuwa amma hakan ya faskara sai ma ƙarawa kanta damuwa da jawo matsala da tai tsakaninta da Jiddah.

Me yasa Faisal zai masu haka ne? Me yasa ya shiga tsakaninsu don kawai ya raba su? Ya manta yadda suka wahala kan neman juna shi ne zai saka masu da hakan bayan sun ga juna? Ya kamata ta nuna mai cewa bai yi masu daidai ba kuma akwai abin da ake bari don kunya ko da ya zama halas ne. Sai a yanzu ma take hasaso irin rainin da Faisal ya yi mata wanda har shahararsa tasa ya wanke ido ya wanke baki ya ɓullo da maganar son auren Jiddah.

Wai ita ce Faisal ke ɗauke ma kai, yana mata ciccin magani yana nuna mata halin ko'in kula da ita kanta da yaranta akan zai ƙara aure? To idan ya ƙara auren ya kenan zai mata kuma? Tabbas sai ta wayi gari ya juya mata baya ita da yaranta baki ɗaya idan ma bai sake ta ba.

Lallai Jiddah masoyiyarta ce wadda bata da kamarta a faɗin duniya tun da har take mata faɗa kan mijinta ya san ciwon kanta. 

Wayarta ta kalla sunan Jiddah ne da take ta kira amma bata ɗauka ba, kiran wayar Faisal ne ya shigo wayarta kamar ta ɗauka amma kuma sai ta ji ya kamata ta nuna mai ita ma mace ce fa tana da ƴancin gaske a gidan mijinta ba zata iya ɗaukar kowane irin cin fuska daga mijinta ba.

Hakan yasa ta kashe kiran kawai, tai wurgi da wayar ta kwanta tana jin yaushe ne ma tai saken da Faisal ya yi mata irin wannan rainin? Zumbur ta miƙe tsaye ta shige toilet tai wanka ta fito ta ɗauki cikin kayan Jiddah ta saka ta nufi kicin ta fara haɗa girki don tai ma kanta alƙawarin sakin ranta ba zata sake sakama kanta damuwa ba kan hidimar Faisal ba, amma tabbas ya sake kawo mata raini sai ta haɗa shi da soyayyar tai masu wankin babban bargo ta ji dalili.

Nan da nan ta haɗa abin da take buƙata ta fito ta zauna ta ci iyakar cinta ta jawo wani littafi ta fara karantawa kira ya shigo mata daga Lagos.
Tana ɗagawa aka fara kora mata bayani kamar haka, "Madam dama wata tsohuwa ce ke son magana da ke ta damu mutane ko da yaushe kuka take tana cewa a kira mata ke ko a waya ne tana son yin magana dake, to da dai mun share ta sai mu ka ga bata lafiya a kwanakin nan, kuma tana cikin jerin waɗanda Gwamna ya yafe mawa amma taƙi tafiya tace dole sai an haɗa ku don ta ganki a kwanakin baya a cikin gidan nan, shi ne dai nace bari na kira mata ke ga ta nan." 
Cike da mamakin ko wace tsohuwa ce tace mai ya bata wayar.

Cikin kuka Inyami ta ambaci sunan Alawiyya da Hausarta wadda har zuwa yanzu bata koma ta daidai ba.
Ko da Alawiyya ta ji sunan ta tashi zaune sosai, domin ta gane muryar Iyami mai abinci Lagos ce uwar riƙon Jiddah da ita a shekarun baya.

Iyami cikin kuka tace, "Don Allah ina Jiddah take ne? Ina son ganin Jiddah don Allah ki haɗa Ni da ita na nemi gafararta kan abin da nayi mata don Allah ki yi min wannan lamunin Alawiyya ke ma ki yafe min tabbas na cutar da ku sosai."

Alawiyya tai ajiyar zuciya tace, "Iyami  ki daina kuka natsu muyi magana da ke. Me ye ya kai ki gidan Yari ne?"

Iyami na kuka na gaya mata abin da ya kaita gidan yarin har ta ƙare ta gaya mata da ta ga Baban Jiddah ma a gidan.

Alawiyya tai murmushi tace, "Bayan shi ma akwai mijinta dake nan duk nice na kai su ajiya don su gyara halayensu."

Gaban Iyami ya faɗi jin cewar Alawiyya ce ta kai Baban Jiddah gidan yarin to ina ga ita da ta riƙe Jiddah riƙon cin amana?

Nan ta saki baki tai ta garza kuka tana neman tafiyar Alawiyya ta kuma haɗa ta da Jiddar.

Duk da cewar Iyami ta cuce su ai ta yi masu gatan riƙe su, ta kuma hana wasu su cuce su, ita kaɗai ta amince ta cuce su bata yadda kowa ya ci zarafin su ba, ta sha yin dambe da ƙatti kan sun taɓa su ko suna neman keta masu mutunci.

Sai taji tana son sake ganin Iyami a rayuwarta don haka tace cikin muryar tausayi, "Ki yi haƙuri ki daina kuka zan aiki a zo min da ke Iyami har Jiddah duk muna jiranki kar da ki ji komai mun yafe maki."
 
Iyami tai ta godiya, da Hausarta, tana ƙarawa duk ta cika wa Alawiyya kunnuwa da ƙarar kukanta.

Baban Jiddah na zaune a gefe ya buga tagumi yana kallon yadda Iyami ke neman gafarar su Jiddah sai kunya ta kama shi, wai ace shi ne Baban Jiddah amma bai isa ya ce ga yadda ta koma ba yanzu. Ya san ba don bai isa ya ce bai gane ɗiyarsa ba, to ba shakka da bai gane ta.

Hawaye suka zubo mai ya hasko yadda yai rayuwa da mahaifiyarta mace mai haƙuri da kauda kai da tausayi amma haka ya banzatar da ita ya dinga tafiyarsa yana mantawa da ita.

Haka ta haifi Jiddah cike da takaici da rashin jin daɗin abin da yake mata, amma shi ko a jikinsa yana sane da yadda mahaifiyarsa ke takura mata amma ba ruwansa har dai ya kaita ƙarshe tace ya bata takardar ta.

Iyami ta dubi Baban Jiddah tana kukan farin ciki tace, "Na gode wa Allah sun yafe min yanzu haka za su aiko a tai da Ni, na ji daɗi da ban mutu ba na nemi tafiyarsu.
Ina maka nuni da kaima ka je ka nemi yafiyar Jiddah idan kana son samun kwanciyar hankali idan ba haka ba kuwa ba zaka sake farin ciki ba a rayuwarka." Ta jima tana mai nasiha irin tasu wadda suka ga hau a rayuwa.

   Ranar da Jiddah ta dawo Kaduna ta iske Alawiyya bata tafi ba sai kawai ta sauya ɗaki ta bar mata wancan sai dai idan wani abu ya kawo ta ɗauka dole sai ta zo ta ɗauka bata magana.

   Jiddah na shigo wa ɗakin ta ga Alawiyya zaune tana waya, ko kallo bata ishe ta ba, kawai kayan da take buƙata ta ɗauka ta koma ɗakin data sauya, sai dai Yau wayar da Alawiyya tai ta sata kuka ta tuna mata wata rayuwa wata mata wani bigire wani yanayi na baya daya wuce. Har ƙasan ranta ta ƙagara gobe tayi taga zuwan matar don har zuwa yanzu tana cin moriyar abubuwa da dama da matar ta koya mata na fannin girki ba wanda bata iya ba.

     Washegari sai ga Iyami an kawo tayi baƙi ta rame duk tsufa ya yi mata sallama. Da gudu Jiddah ta ruga ta rungume ta tana kukan farin cikin ganinta, duk da cewar Iyami ta cutar da ita ai tafi mahaifinta gunta tun da shi kasa riƙe ta ya yi don haka ya kaita uwa duniya don a riƙe ta, ita kuma ba dangin Iya bana Baba asalima ba addini ɗaya ba haka ba yare ɗaya ba amma ta amshe ta tun tana miririyarta ai kuwa bai kamata ta yada Iyami ba.

Sun jima suna kukan haɗuwa Iyami na neman tafiyarsu suka yafe mata, aka baya ɗaki guda a cikin gidan ta zauna. Wani abin farin ciki ta samu Jiddah ta gaya mata cewar tana so ta musuluntar da ita, ba ƙaramin daɗi abin ya yi masu ba, shi kanshi Baffa ya yi murna sosai da jin zata musulunta. A ranar aka musuluntar da ita ta amsa sunan Hawwa'u (Jiddah) Allah ke nan Yau ga Iyami ta musulunta bayan a baya ita taso saka Jiddah nata Addinin.

Ko da yaushe Iyami na son yi wa Jiddah maganar Babanta amma tana jin tsoro saboda Jiddah ta bata labarin yadda rayuwarta ta kaya bayan sun rabu duka. 

Amma Yau dai ta kasa haƙuri tai mata maganar wanda Jiddah tai mirsisi tace ita bata da wani uba da yafi Baffa don haka ta daina mata maganar wani.

Ƙarshe dai sai da Baffa ya shiga maganar sannan Jiddah ta amince da cewar ta yafe mai kuma a sake shi amma kar wanda ya gaya mai inda take.
Iyami tace, "Ai yasan inda kike tun ina can na gaya mai, kuma a ranar da nayi waya da Alawiyya yana tare da Ni ko ranar.
Tabbas ya yi nadama kamar yadda nayi haka ma uban yaranki ya yi nadama yadda ya kamata ki gode wa Allah Jiddah domin duk wanda ya cuce ki tun a duniya yake fara ganin sakayyarki.


Duk lokacin da Baffa ya dawo yaran suna murna suke rugawa ɗakinsa. Sosai yake murna da zuwansu ɗakinsa, yana son yaran jinsu yake tamkar da gaske jikokinsa ne daya haifi mahaifiyarsu ko mahaifinsu. Wani ɓangaren kuma ladabi da biyayyar Jiddah na ƙara sawa yana jin ta a ranshi sosai, yarinyar ke burge shi don haka yake jin tausayinta yake da burin yaga ya tallafi rayuwarta ta tsaya da ƙafafunta ko bayan ransa ba zata sake kukan rashin gata ba.


    Kamar wasa Jiddah ta fice sabgar Alawiyya kuma taƙi komawa Kano baki ɗaya ta fice daga sabgar Faisal itama abin kamar wasa kuma Baffa ya kawo ido ya saka mata bai ce mata komai ba, haka ita ma can Mama ta saka mata ido saboda Maman Faisal ɗin ta kira ta tace kada wanda ya shiga sabgar Alawiyya da Faisal ɗin a barsu su ƙara ta can su suka sani.
Ita kam tayi haka ne don ta ƙwatarwa da Alawiyya ƴancin ta gun Faisal ya gane kurensa yadda ko ance gana ya yi mata irin haka ba zai sake ba.

Shi kuma tun yana ganin zata dawo ne ko zata daina fushin da take tun da bai mata komai ba, kawai rainin hankali ne ta zo da shi da zata wani tafi Kaduna ta zauna ko kiranta ya yi bata ɗaukar kiran.
Gefe guda kuma Jiddah tayi blocking na number shi bai ganinta a online haka ko ya kira bata shiga da ya matsa mata ma sai ta samu lokaci ta turo mai kashedi na musamman har ta kira shi da mai raba zumunci mai yanke abota. 

Tun daga lokacin ya tabbatar da cewa Jiddah bata taɓa amincewa da aurensa don haka ya koma kan Alawiyyar yanzu. Sai dai tai mirsisi ta ƙyale shi kuma abin takaici ba wanda ya saka baki kan ta dawo Kano ɗin.
Jiddah ta dubi Alawiyya ta ƙara haɗe fuska tace, "Malama ya za ki zo ki takura min bayan kin san cewa na bar maki wancan ɗakin don gudun takurawarki?"

Alawiyya ta langaɓar da kanta gefe guda alamar neman afuwa tace, "Don Allah ƴar'uwata abar alfahari na mai tausayi na ko da yaushe ki yafe min ki manta baƙin halin da na nuna maki, ki yi min aikin gafara ko na samu sukuni a zuciyata. Tabbas na manta cewa Ni dake tamkar uwa ɗaya Uba ɗaya muke auren miji guda ya haramta garemu. Sai dai idan ba ran guda a doron duniya ne ɗayar zata iya auren mijin don cigaba da riƙe yaranmu da shi kanshi mijin."


Jiddah ta kalleta fuska ba walwala tace, "Ban taɓa tunanin za ki yi min abin da kikai min ba Alawiyya. Ko kin san da cewar duk lokacin da nake cikin ƙuncin rayuwa addu'a nake Allah Yasa ke baki cikin ƙuncin. Haka zalika duk lokacin dana tunaki fatana gareki ki zama cikin aminci amma sai ga shi kin watsa min ƙasa a ido kece mai neman kai Ni ga tashin hankali da damuwa. Ban taɓa zaton ke ce za ki iya raba zumuncinmu da amincinmu ba sai ga shi na gani na shaida da karin kaina. Ke a tunaninki idan auren miji guda ya gitta a tsakaninmu za mu dawwama ne yadda muke ? Ke a naki hangen auren mijinki wata mafita ce mai ɗorewa a garemu? Uhmm! Kin wauta kamar yadda ya so kansa Alawiyya ban za ci cewar baki son mijinki ba sai yanzu, tabbas ya kamata ki natsu ki gane me kike ki fahimci waye mijinki don samun kwanciyar hankalinsa da naki baki ɗaya. Kin ban kunya kin sa naji ba daɗi da har kika iya barin ɓarakar da mijinki zai iya saka wata a cikinta. Akan me za ki yi hakan Alawiyya? Ke fa babba ce a fannin aikinki shin ba za ki zama babba ba a cikin zuciyar mijinki ba? Don Allah ki gyara halayenki domin ban gamsu da kulawar da kike ba Faisal ba sam Alawiyya. Idan barci kike ya kamata ki farka haka nan kafin ya haddasa maki wata matsala barcin."

Sosai Alawiyya ke fahimtar maganar Jiddah tabbas daman can tasan Jiddah mace ce mai son kula da kulawa haka zalika bata sake da duk abin da take so, ba ƙaramin asara bace ga namiji ba ya rasa mace kamar Jiddah ba. Tabbas ta taya Prince murna domin ta lura da cewar shi ne zakaran gwajin dafin da ya ci gasar sace zuciyar Jiddah a cikin jerin mazan dake karakaina kan neman amincewar ta kan ƙaunarsu.

Cikin mintuna ƙalilan suka haɗa kansu,sai ga su suna ta dariya kamar ba su ba. Alawiyya ta dubi Jiddah tace, "Yau fa muna da babbar baƙuwa a gidan nan nasa an ɗauko ta nasan suna gab da isowa nan ba da jimawa ba."

Jiddah tai murmushi tace, "Kina nufin Iyami wai?"

Da kallon mamaki Alawiyya ta kalli Jiddah don ita dai tasan bata gayama kowa zuwan Iyami ba, haka zalika bata gayama Jiddah da bakin ta ba.

Jiddah tai murmushi tace, "Kina manta aikinki kina manta aikina ban san me yasa ba."

Alawiyya tai dariya tace, "Ba fa za ki kwantar da Ni ba, nasan dole akwai yadda akai kika san da zuwan Iyami, kawai ki gayamin."

Jiddah tai dariya tace, "Madam kin manta da cewa ɗakina kike zaune? To a cikin ɗakin akwai wayar da na aje wadda duk wanda ya yi magana tana naɗewa tana turawa a wayar hannuna, don haka duk maganar da ki kai akwaita a cikin wayata ba wadda ban sani ba." 

Alawiyya tai murmushi tace, "Na jinjina wa babbar Lauya mai ɗinbim basira da kaifin ƙwaƙwalwa Barista Jiddah."

Jiddah ta kwashe da dariya tace, "Har kin tuna min da shari'ar da zan yi gobe ta wata yarinya da ƙanin mahaifinta ya lalata mata rayuwa saboda abin duniya. Kuma abin takaici shi ne mahaifin yarinyar shi ne ya riƙa shi har girmansa ya saida komai nashi don ya inganta mai rayuwa amma shi ne ya yi mai sakayyar lalata mai yarinya ƙarama yar shekara takwas wai bokansa ya ce mai zai arziƙi idan ya biya buƙatarsa da ita, kuma zai samu kujerar da yake nema ta siyasa."

Nan da nan Alawiyya ta haɗe rai tace, "Dole ne ma na raka ki gobe kotun domin naga yadda zata kaya, bai kamata ki bari a ja lokaci ba gun shari'ar tun da ga alama akwai shaggun a gun mugun."

Jiddah tai murmushi tace, "Ba shi ne damuwata ba sai wani tsinannen miji da ya saki matarsa saki uku bayan ya gama amshe mata komai na dukiyarta kuma ya raba ta da danginta sannan ya kwashe mata yara mata wai zai kai su Makkah aikatau. Shi ne kawai na je kotu rannan ake gayamin wata mata na nemana kamar ba zan bi takan ta ba sai kuma nace a bata lambata ta ace nace ta kira Ni.

Shi ne fa ta kira Ni take gayamin zai tura mata yara Makkah aikatau har ya amshi kuɗin aikinsu na shekara biyu, bai bata ko sisi ba kuma bai nemi shawararta ba kan lamarin duk da cewar tun suna yara ya sake ta ya amshe gidan da suke ciki duk da cewar nata ne na gado ya amshi dukiyarta da sunan zai juya mata sai kawai gani tai ya kama gyaran gida ya sai mota, bata san hawa ba bata san sauka ba sai ganin masu gini tai sun shigo sun kama aikin gini, yana dawowa tai mai magana ya ce tasa mai ido ba ruwanta. Karshe dai sai ga motar kawo amarya an kawo an saka ta cikin fallelen ɗakin da aka gini, bata samu damar tanka mai ba washegari ya danƙara mata takardar saki uku ya ce tabar mai gidansa idan tana da mai iya ƙwace mata kuma ta turo ya amsar mata. Hakan duk bai ɓata mata rai ba ta haɗe fushin ta zata tafi ya ce kar ta bar mai yaro ko guda ya bar mata su, don ba abin da ya'ya mata za su tsinana mai a rayuwa. Haka ta nufi gun danginta ashe suma duk ya bi su ya yi mata sharri don haka suka kore ta ita da yaranta ƙarshe gidan haya suka kama ta ci gaba da sana'ar saida abinci tana biyan kuɗin haya shi ne yanzu yaran duk sun girma har biyu sun samu mijin aure zai kama su ya kai su Makkah aikatau don shi azzalumi ne na gaske."


Alawiyya tai ajiyar zuciya tace, "Lallai ya kamata a ƙwatar masu ƴancin su, amma me zai hana ki buɗe ofis kema kamar yadda na buɗe a Kano? Sai inga sai kin fi samun damar taimakawa duk wanda ya kamata Jiddah."
Jiddah ta jinjina kanta kamar mai tunani tace, "Kin kawo shawara kema amma fa karatu zan koma har Baffa ya gama yi min komai. Amma duk da haka akwai lokacin da zan ware don hakan insha Allah."


Wayar Jiddah tai haske alamar kira zai shigo, sai ga wata waƙa mai daɗin gaske ta indiya na tashi daga wayar. 
Alawiyya na ganin yadda Jiddah ke murmushi alamar taji daɗin kiran wayar da akai mata.
Furucinta na farko yasa ta gane da wanda take waya, Mustapha ne ko tace Prince kamar yadda taji Jiddah ta ambata.

Ba kunya Jiddah ta saki baki ta dinga yi ma Prince ɗinta shagwaɓa abin kamar a mafarki haka Alawiyya take ganin lamarin yadda Jiddah ke waya cikin shauƙi da farin ciki ta kuma soyayya wayar.
Ita kanta Jiddah ta birgeta ina ga shi wanda ake abin don shi? Haka take raya wa a ranta, lalle ne Mustapha shi ne zaɓin Jiddah kuma Jiddah ita ce zaɓin Mustapha don ga alama sun haɗu a mahaɗar da kowane daga cikinsu ke so.

Jiddah ga alama ta manta da Alawiyya dake zaune baki buɗe tana kallonta cike da mamaki sai kalamai suke musaya ita da Prince ɗinta zuwa can ta marairaice murya ita ala dole kuka take yi.

Lallai ta tausaya wa matan Mustapha indai ba su kasance yadda yake ba to tabbas akwai daru a gaban Jiddah don za su ce ne ta asirce masu miji ta mallake shi, tunda zuciya na san mai kyautata mata kuma ga alama Jiddah ta dage gun hakan.

Sun jima suna wayar wadda farin ciki ke ƙaruwa duk bayan kalma guda da Jiddah ke ambata a kan fuskarta.

Alawiyya tasan daman can Jiddah akwaita da son rayuwar soyayya don haka ne ma tafi kallon Film ɗin indiya akan na Hausa ko da suna gun Iyami idan suka saci jiki suna zuwa kallo gidansu wata Badiyya to indai Hausa ne Alawiyya ke murna amma idan suka iske an saka indiya Jiddah ke murna har da rawa, musamman idan Film ɗin jaruminta ne Rothick Roshan.

Ko haka nan suna maganar soyayya idan suka ga wasu na fira Jiddah kan taɓe bakinta tace, "Ni fa ba kowace soyayya ke birgeni ba, kamar yadda ba kowane namiji ke birgeni ba. Idan ta ga wani ɗan gayu tace "wannan kam ya birgeni sosai. Idan taga wanda bai da tsabta takan ce, "Wannan kuwa ko za a haɗa min da kyautar gidanmu ba zan amshi soyayyarsa ba."

Tun fil'azal Jiddah tana son soyayya tana son mai kyau haka tsabta na matuƙar jan ra'ayinta kan kallon namiji idan suna tafiya.

Sun kwashi awowi suna ta shan soyayyarsu wadda har Alawiyya ta gaji ta tashi ta fice tana jinjina wannan lamari na Prince da Princess ɗinsa.

   
          Washegari da wuri suka shirya zuwa kotun saboda da abin kowace daga cikinsu ta kwana, suna shiga kotun  ƴan jarida su kai masu caa, domin zuwa yanzu sunansu ya kewaye ko'ina da ance Barista Alawiyya za a ce Barista Jiddah.

Bayan kowa ya natsu ne aka fara shari'a mai cike da son kai da nuna rashin adalci ƙarara, wanda hakan ya fusata Barista Jiddah tace zata shigar da shi kanshi Alƙalin ƙara bayan kammala shari'ar.

Kasancewar da dama sun san waye Alƙali Mansur sun fahimci kuma shi ne ke mara ma Barista Jiddah baya kan kowace shari'ar da take yasa wasu ke ba Alƙalin shawarar ya yi adalci idanma cin hanci ya amsa ya maida ya yi shari'ar gaskiya kafin ƴan jarida su fara watsa labarai musamman da suka fahimci yadda zukatan Baristocin suka hasala har ta kai ga Barista Jiddah tace ta aje shari'ar amma tana gayyatarsa babbar kotu don ya kare kansa.

Abin da Alƙalin bai sani ba ashe hada ƴan gidan talabijin da rediyo suka halarci shari'ar kowane ya ɗauki abin da ke faruwa ya watsa.

Abin da ya ja hankalin sauran Alƙalai kenan suka yo mai caa kowa na cewa zai zubar masu da mutunci, a nan take aka aiko da takarda an maida shari'ar babban kotu dake high court dake Abuja.

Abin da ya ƙara ɗaukaka sunan Barista Jiddah kenan nan da nan sunanta ya dinga yawo a jaridu da gidajen rediyo da talabijin.
A can ne ta haɗu da wani matashi wanda ya jiƙu da Naira ya sha karatu har ya ƙoshi ya nace mata kan yana son ta.

Hon. Yusuf Matashi shi ne sunansa,ɗan siyasa ne kyakkyawa ajin farko a kyawu yana rayuwarsa a Abuja amma siyasa tasa babu inda bai sani ba, haka ba inda bai da masana'anta ya haɗa kasuwanci da siyasa yana yi kuma ba laifi komai na tafiya yadda ya kamata gare shi.

Lokacin da akai shari'ar ne ya ga Jiddah nan take ya ji duk duniya bai da wadda yake so yaga dacewarsa da ita irin Jiddah, duk da cewar akwai tarin ƴan mata ƴaƴan masu hannu da shuni dake bibiyar rayuwarsa domin ya kula su amma abin ya ci tura, wasu sun sha yi mai tayin kansu ko da na rana guda ne amma ba tasu yake ba. 
Shi kansa mamakin kansa yake yadda kallo guda yai mata wani kakkaifan abu ya fito daga idonta ya shige cikin nashi idanun ya bi jikinsa ya shige kowace kafa ta jikinsa.

Ita kam Jiddah bata san wainar da yake toyawa ba, tana gama shari'arta suka ƙara kwana biyu ita da Alawiyya suka dawo gida cike da farin cikin nasarar da suka samu, wanda akai ta kawo kyautuka ana ba Barista Jiddah saboda jin daɗin namijin ƙoƙarin da tai gun ƙwatarwa matar nan haƙƙinta ita da yaranta, ta kuma ƙwatarwa yarinyar da ƙanin mahaifinta ya lalata a lokaci guda duk da cewar manyan shari'ar gaske ne duka biyun amma ta haɗa su ta make lokaci guda.

Dr. Faisal da gaske abin ya fara damunsa na Alawiyya kwata-kwata ba tashi take ba, sai dai ya gani a labarai tai kaza tai kaza baki ɗaya bai cikin tunanin ta, abin da ya fara ba shi tsoro kenan ya shiga damuwa ya je kai tsaye ya samu mahaifinta da maganar.
Sai dai shima kamar yadda kowa ya nuna ba ruwansa da sha'anin su haka ya ce mai ba ruwansa da shiga abin da ba ruwansa sun fi kusa.

Iyakar tashin hankali yana ciki sai kuma ga saƙon ta wai ya sake ta ko ya samu takardar sammaci ko da yaushe.

Ranar ya tarkata ya nufi Kadunar hankali tashe, domin yasan wace ce Alawiyya akwai ta da kafiya da naci da ɗaukar wa kanta abu komin wahalar da zata sha indai tasa kanta bata ganin wahalar sa.

A kar cat ya isa gidan, amma ba wanda ya kula da ko zuwansa a gidan sai yaran Jiddah kyawawan gaske da su.

Yana zaune yaran nata wasansu yana kallonsu yana tuno yaransa su Anam da Ammar yana murmushi hakimar ta fito cikin shirinta na barin gidan tana waya, ko kallon inda yake ba tai ta nemi wucewa. Sakin baki ya yi yana kallonta yadda tai wani kyau na daban ta sauya ta ƙara haske na ban mamaki komai ya ji tamkar wata ƴar shekaru ashirin.
Ganin zata bar shi zaune yasa ya jawo gyalenta ta baya tilas ta juyo, ta watsa mai idanunta masu haske da kaifi.

Lumshe idonsa ya yi yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa kamar zata fito don fargaba saboda yasan yadda kallon matar tashi yake yasan mai ke biyowa baya idan ta yi shi.

Tamkar bata san shi ba, tamkar Yau ta fara ganinsa haka take binsa da kallo, abin da yasa yaran suka zubo masu ido suna ƙare masu kallo tamkar sun samu talabijin.

Jiddah da akai ma waya ana kiranta bakin get ta fito cikin takunta tana tunanin waye ya ke kiranta ta amshi saƙo kuma wai daga Abuja? Ta ga yaran sun yi zuru suna kallon su, tai murmushi ta kama yaran ta tura su ɗaki, ita kuma ta raɓa ma'auratan ta fice tana murmushin yadda ko kallo bata ishi Faisal ba duk yadda yake zuzuta mata yadda yake ƙaunarta yake burin aurenta, Yau ga shi gaban matarsa ya zama abin tausayi ba ta ita yake ba ta kansa ma yake.

Tana fita ta iske mutane biyu kallo guda tai masu ta fahimci tabbas duk inda suka fito su ɗin ma'aikata ne. Bayan sun gaisa ne guda daga cikinsu ya bata wata takarda da makulli ya ce, "Daga Abuja muke saƙo ne daga Hon. Yusuf Matashi ya ce a kawo maki kafin ya iso bai nan ne, ya ce ya jinjina maki sosai kan yadda ki ke jajircewa kan aikinki."

Sosai tai godiya domin wannan ba shi ne farko ba gunta yanzu ba, ta samu kyautuka sosai daga mutane daban-daban wasu da kansu suke zuwa wasu kuwa aikowa suke kamar hakan. Don haka tai godiya ta amsa tana tsaye taga sun hau mota guda sun bar guda sai a lokacin ta fahimci motar ce kyautar da aka kawo mata.

Cikin gidan ta koma don ta gayama Alawiyya duk da cewar tana tare da mijinta suna karawa. 

Da fara'arta ta shiga falon suna zaune Alawiyya na latsa waya Dr. Faisal na tsugunne gabanta ya kama kunne yana bata haƙuri ita kuma hakimar ko a jikinta. 

Kamar ta wuce sai taga rashin dacewar hakan don haka ta isa kusa da su tai magana, "Ahh! Abbansu Anam ne a gidan namu Yau? Maraba sannu da zuwa, don Allah zan ari Madam ɗin taka minti biyu ba yawa pls."

Alawiyya ta watsa mata harara, shi kuma ya kasa ko ɗago wa daga tsugunnen da yake balle ya bata amsar maganarta.

Alawiyya tai murmushi ta tashi ta nufi Jiddah suka fice Jiddah ta bata saƙon da aka kawo mata yanzu.

Ihu Alawiyya ta saka ta rungume Jiddar tana murna sosai, ita ce ta tuƙa motar ta shigo da ita cikin gidan.
Sanan ta buɗe takardar zunzurutun kuɗi ne masu nauyi da daraja har na Naira miliyan goma wai ta zuba mai ba yawa.

Suna cikin hakan Baffa ya shigo suka nuna mai ya saka albarka sosai ya yi addu'a domin yana da niyyar sai mata motar sai ga shi wani ya riga shi don haka ya ji daɗi sosai ga mota babba mai tsadar gaske.

Wayar Jiddah tai ƙara taga baƙuwar lamba kamar kar ta ɗauka sai kuma ta tuna don a kira ta kan aikinta take riƙe da wayar don haka ta ɗaga kiran kai tsaye.

"Ina fatan ina magana da Barista Jiddah ne?"

Wata sansanyar murya ce mai cike da izza da gadara tai furucin.
Samun kanta tai da ɗaga kanta tamkar gabanta wanda ya yi maganar yake.

"Sunana Yusuf Matashi daga Abuja."

Ajiyar zuciya tai domin ta gane shi yanzu shi ne ya aiko mata da kyautar musamman a Yau ko ma ta ce a yanzu.

"Ina fatan ban laifi ba dana aiko maki da ƴar ƙaramar kyauta wadda nasan kin fi ƙarfinta nesa ba kusa ba, sai dai ina son aikin haƙuri don Allah kin san abinki da mai nema sai a hankali."

Kasa cewa komai tai domin yadda yake maganar tamkar wanda ake ma susa ko wani babban saraki shi ne ma abin da yafi tafiya da hankalinta.

"Don Allah ki yi min magana kin sa sai magana nake ba tare da kin ce min ko da ƙala ba, hakan sai naga tamkar kora da hali ne fa Barista."

Sai da tai da gaske sannan bakinta ya furta, "Ina jinka ai."

Tana jin sautin ajiyar zuciyarsa, wanda ya tilas tata zuciyar yin tata ajiyar ita ma.

"Don Allah Barista ki ban aron lokacin ki ina son zuwa don mu yi magana mai muhimmanci dake jibi don Allah kar da kice min a'a." Ya idasa maganar tamkar zai kuka.

Jikinta baki ɗaya sai ya yi sanyi ta rasa me ke shirin faruwa da ita ne haka?
Alawiyya hankalinta na kanta don haka sai ita ma kasa gane inda Jiddar ta dosa taga jikin Jiddar ya yi sanyi nan da nan komai ya sauya ma Jiddar.

"Don Allah a taimaka ace na zo Barista."

Cikin sanyin jiki tace, "Shike nan ina nan ina jiranka sai ka zo ɗin."

Wata ƴar ƙara ya yi irinta farin ciki ɗin nan ya ce, "Wow! Gaskiya ban taɓa samun albishir da ya yi min daɗi irin wannan ba duk a wannan shekarar don haka kyauta ta musamman na nan zuwa gare ki ladar wannan albishir da ki kai ma Matashi."
Murmushi kawai tai tace, "Na gode sosai da saƙo Allah Ya saka da alheri. Sai na ganka."

Bata ba shi damar cewa komai ba ta kashe wayar saboda kar da rawar da jikinta ke yi yasa wayar ta faɗi ƙasa ma.

Hannunta Alawiyya ta kama suka shige ɗaki ta kama tambayarta abin da ke faruwa cikin yanayin damuwa ta zayyana mata komai.
Cikin sauri Alawiyya ta saka sunan Hon. Yusuf Matashi a yanar Gizo sai ga bayanansa da hotonsa ya bayyana.
Matashi ɗan ƙwalisa ajin farko a kyawawa jajir da shi ga hanci fuskarsa na kewaye da ƙasumba kwance lub a fuskarsa.

A nan suka ji tarihinsa da aikinsa sun sha mamaki sosai jin saurayi ne bai taɓa aure ba, kuma har yanzu bai da ra'ayin auren tun da bai  samu wadda tai mai ba duk da tarin matan dake binsa.

Ita kanta Alawiyya sai da jikinta ya yi sanyi kan lamarin.

Saƙo ya shigo wayar Jiddah

"Barista daman nasan yadda na zata haka kike ashe ma kin fi yadda na zata. Tabbas ke ce nake jira shekara da shekaru ban ganki ba sai a yanzu don Allah ki ban damar mallakarki don na idasa rayuwata cikin aminci da walwala.
Naki Yusuf Matashi."


Alawiyya ta miƙawa wayar ta zauna ta dafe kanta tana hasko fuskar Prince ɗinta.

To ko ya kenan za ai?

Taku a kullum Haupha ✍️