Gwamnatin Zamfara Za Ta Dauki Mayakan Sa-Kai 2000 Don Yaki Da 'Yan Bindiga
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta amince da daukar sabbin mayakan sa'kai dubu 2 don shiga cikin rundunar yaki da 'yan bindigar wadda gwamnatin jihar ke tafiyarwa a kokarin baiwa jama'a cikakkiyar kariya daga batagarin,
Shugaban kwamitin da ke kula da dakarun masu yaki da yan bindigar a Zamfara Mr Bello Bakyasuwa a jawabinsa gaban manema labarai a ranar Alhamis da tagabata a birnin Gusau ya ce sun karbi umarnin daga gwamna Bello Matawalle game da daukar sabbin yan sa'kai,
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa Gwamnan jihar ta Zamfara Bello Matawalle ne ya yi umarnin kafa kwamitin na musamman don yakar matsalolin yan ta'adda da garkuwa da mutane da kuma ta'ammali da miyagun kwayoyi,
A cewar Bello Bakyasuwa akalla mutane dubu 6 da 700 suka mika takardun neman aikin a sassan jihar ciki har da mata said ai duka-duka mutum dubu 2 za a dauka don gudanar da aikin,
Jihar Zamfara na sahun jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar yan ta'adda da ke garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
managarciya