MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani Fita Ta 42 Zuwa 43
Page 42------43
Baki ɗaya sai Bilkisu ta rasa yanda za tayi, da gaske ba fuskar Inna take gani a jikin madubin ba idan ta kalla, to mi hakan ke nufi kenan ?
Bai kamata ta sake tada ma Babansu hankali ba, domin ko yanzu bai zaune bai tsaye kan lamarin maganin Innar tasu, gashi Ibnah fushi yake da ita bai ko kiranta, balle ta nemi shawara garesa, amma fa duk rintsi duk wuya ba zata lamunci kalan wannan azabar ga Innar tasu ba, duk faɗan Inna duk mitarta yanzu babu, rabon da Innar ko ruwa tasha cikin daɗin rai har sun manta, dan haka zata samu mafita gaskiyar kan lamarin Innar tasu, domin ta jima tana zargin Innar tasu na ɗauke da muggan baƙaƙen Aljanu, kawai furta wa ne batai ba, amma yanzu anzo gun da zata ɗauki mataki da kanta.
Tayi shiru tana tsara dukkan matakan da zata ɗauka kenan taji an dafa kafaɗarta, cike da mamaki ta ɗago sai kuwa su kai ido huɗu da ƙawarta Shema'u Yahaiya ce ashe.
Bayan sun gaisa ne Shema'u ta dubi inda Inna take kwance ta yamutsa fuska tace ma Bilkisun, "Tun yaushe Inna ke kwance ne ba lafiya ? Bilkisu ta dubeta da fuskar mamaki, "Amma dai yau baki jin dai-dai ko Shema'u ? Sau nawa kina zuwa kina duba jikin nata amma ace ke ce ke wannan tambayar ?
Kanta ta dafe Shema'un alamar mantuwa tace, "Ke ni fa yau ki mun uzuri ji nake kamar ba ni bace yau, amma kuwa kun jaraba yi mata maganin Aljanu Bilkisu ?
Girgiza kai Bilkisun tayi, "Ban da na asibiti babu abin da ake mata, dan Baba bai yarda da maganin ƴan tsubbu ba Shema'u, kwanakin baya da aka kira wani munga bala'i sosai a gidan nan ai.
Murmushi Shema'un tayi tace to zan amso maki wani magani gun Kakana, indai Aljanu ne ana kawo maganin zasu fara neman hanyar guduwa da kansu, amma fa ki sani idan sune ranar da na kawo maki maganin ba za ki yi barci ba, domin za su yi ta razanaki suna baki tsoro dan su ƙwace maganin daga gunki, sai dai kina tsorata to ki sani ba zata taɓa warkewa ba, kuma ke da ita har abada."
Tana gama maganar ta miƙe tsaye, "Na tafi Bilkisu sai na kawo maki, ki kula domin naga idanun ɗiyar Azam a gidan nan." (Tayi gaba ba ko waiwaye)
Duk sai Bilkisu ta sake shiga wani tunanin domin yau zuwan Shema'u yazo mata a wani kala, gashi sai sakin maganganu take waɗanda ta rasa gane kansu ita kwata-kwata ma.
Shema'u na zuwa zaure ta zama hayaƙi ta ɓace, tana gaggaɓa dariya mai ban tsoro, tana cewa, "Huraira zan taimakeki ne kawai dan Nasir na san yarinyarki, ba yan haka da na bari Rayhanatu azam ta cigaba da zama matsayin ke, ke kuma kina dajin mibrazul ladak, kina bautuwa.
Kamar yadda ta yi niyya a ranta, ƙarfe ɗaya na dare ta farka domin zuwa ta ga halin da Innar tasu take ciki, dan haka ta lallaɓa ta fice daga cikin ɗakinsu ta nufi ɗakin Innar tasu jikinta ko ina rawa yake kasancewarta mai shegen tsoro ga uban duhu daya mamaye gidan baki ɗaya.
Cikin sa'ar gaske ta iske ɗakin a buɗe, dan haka labulen kawai ta naɗe ta afka cikin ɗakin, idanunta fes kan gadon Innar tasu.
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un !
Ita ce kalmar da Bilkisu ta faɗi, lokacin da idanunta suka sauka kan ƙaton baƙin ƙadangaren da ke kwance bisa gadon Innar,
Jikinsa baki ɗaya baƙi ne, irin baƙin da bai da kyau ko alama, amma idanunsa duk da suna a rufe zaka iya hango yanda suke jawur kamar wata wuta ce ke ci a cikinsa.
Kasa komawa baya tayi, sai ta kama kiran sunayen Ubangiji, cikin muryar tsoro da firgita.
Wani uban juyi ƙaton baƙin ƙadangaren yayi sai ga wasu manyan hannuwa sun burtso daga cikin jikinsa, duk hannu ɗaya yayi tsawon dogon maciji ga su sirara ba tamkar sillen kara, sai ƙara tsawo suke ga alama gun Bilkisun suka nufa kai tsaye.
Zuwa yanzu, Bilkisu ta fara karanto karatun Alƙur'ani mai girma da ƙarfi tana tofa ma hannuwan, wanda wata shafceciyar akaifa ke wali a jikinsu, ko shakka babu wannan akaifa na iya kashe mutum har lahira.
Wutar ɗakin ta ɗauke, duhu ya yawaita cikinsa, yanda ko tafin hannunta Bilkisu bata iya gani, balle ta ga mugun abin da ke tunkaro ta.
Wata girgiza ƙadangaren yayi sai ya koma suffar Huraira, amma fa haƙoranta cako-cako, hancinta a wangame, kumatunta sun lotsa kamar ka zura yatsa ya shige.
Fuskarta tayi wata kafceciyar gaske, sai tunkaro Bilkisu take bakinta na ambaliyar gullama-gullama ta jini baƙi ba kyan gani.
Zuwa yanzu Bilkisu ta gama aminta da cewa Aljanar ba ta da imani ko da yaushe zata iya cutar da ita, dan haka sai ta fara karanto suratul Muluk (Tabaraka) cike da yaƙinin Ubangiji zai kare ta daga sharrin wannan Aljanar.
Ilai kuwa sai ga Aljanar nata neme-neme a cikin ɗakin bata ga inda Bilkisu ta ɓoye mata ba, hakan yasa ta dawo da haske sosai a cikin ɗakin wanda ya fi na farko haske.
Bilkisu na tsaye inda take tana kallon yanda Aljanar ke ta nemanta dan haka sai ta ƙara dagewa da karanta surar cikin yakana da godiya ga Allah.
Harta juya da nufin komawa ɗakinsu sai kuma ta ji bata iyawa, dan haka ta nufi Aljanar gadan-gadan tana tofeta da ayar Allah, sai kuwa ta kama birgima tana sauya halitta zuwa halittu masu ban tsoro na gasken-gaske, amma duk da haka Bilkisu bata saurara mata ba, addu'a take sosai da karatun yanda ya kamata, sai da ta tabbatar Aljanar tayi laushi, ta galabaita sannan tace mata....
"Maza bani labarin inda Innata take ko na ida toyeki kowa ya huta."
Cike da razana Aljanar ke magana cikin galabaitar gaske, "Ki yi haƙuri Huraira na dajin sammun zauwaj cikin fadar shugaba."
Sai da gaban Bilkisu ya faɗi, jin zarginta ya zama gaskiya.
Cigaba da karatun tayi, wanda jikin Aljanar sai baƙi yake kamar an kashe icce mai wuta, ihun naiman taimako kawai Aljanar ke yi, amma ina, ita Bilkisu ranta ya gama ɓaci ji take ko Aljanu nawa za su bayyana zata iya toyesu a lokacin.
Wata kyakkyawar Aljana ta bayyana cikin suffar kamala da natsuwa, ta dubi Bilkisu tace, "Ya ke Bilkisu kiyi sani cewar mahaifiyarki nagare su cikin aminci da natsuwa a halin yanzu, amma nan da kwana uku idan ba ta dawo ba, to tabbas za ta mutu, kuma kasheta za ai."
Cike da ɓacin rai Bilkisu ta dubi Aljanar, domin tasan tuggun Aljanu ba laifi zuwa yanzu.
"Wace ce ke ? Daga wane waje kika zo nan ? Miye silar bayyanarki a gareni ?"
Murmushi Aljanar tayi tace, "Suna na Raƙiyyatul Zayyanul murrash, ban kasance daga jinsin fararen Aljanu ba, sai dai na kasance daga ɓangaren mai kula da kare lafiyar masoyinki da duk wanda ya shafesa.
Taci gaba da magana tana kallon Bilkisun.
"Sunan wannan Aljanar Rayhanatu kuma ɗan Sarkin fararen Aljanu ne ya turo su, nasan baki san abin da ya haɗa ki da su ba, da suke ta yawan bibiyarki da mahaifiyarki ba ko ?
Bilkisu ta girgiza kanta alamar hakane.
Raƙiyyatul Zayyanul murrash taci gaba da cewa, "Wata rana a islamiyar ku kin kori wani baƙin kare kin jefesa sau biyu har kika ji masa rauni, to ba kare bane kika jefa, jarumi sadauki Abduljalal bin Uwais ne (Yah Malam)kika jefa, shi kuma lokacin yaje yaƙi ne da baƙaƙen Aljanu ƴan sarautar mu dake shiga jikin bil'adama suna wahal da su, kafin ki je gun ya fafata ƙazamin yaƙi da su, duk ya fatattake su, yana shirin barin wajen ne kika je da yara kikai masa wannan rauni, wanda shi ne silar da sauran yaran aljanun mu suka koma suka ci galaba kansa, abin da bai taɓa faruwa gareshi ba kenan tunda yake, hakan yasa ya fusata ainun ya rantse sai ya ga bayanki ta mummunar hanya, idan baki manta ba tun daga ranar kika fara fuskantar ƙalubalen rayuwa na bayyanar aljanu gareki duk inda kika je ko ?
To ba ke kaɗai suka takura mawa ba, harda Huraira mahaifiyarki, ita kuma masifarta da tujara tare da ɗumbin jahilcinta yasa ko da yaushe suke samun galabar azabtar da ita duk lokacin da suka bayyana gareta.
Zuwa yanzu bamu da lokaci mai yawa domin dajin da Huraira take yana da matuƙar nisan gaske, kuma ba kowa ne zai kasheta ba sai ainufin budurwar Abduljalal bin Uwais wato Aljana Suwaibatul Zabbar wadda a yanzu tana laddin Laraba taje ne ta koyo haƙuri da juriya gun wani babban malaminsu dake ƙasar Misra, bata da haƙuri bata da tausayi haka bata da imani hakan yasa Abduljalal bin Uwais kasa aurenta duk da cewar shima yana sonta, jin labarin babban malamin mai suna Imam bin Khumaini yasa ya umarce ta data je ƙasar Misra tayi shekaru goma gun Malamin da alƙawarin tana dawowa za su yi aure, to yanzu haka dai labari ya sameta na cewar Abduljalal bin Uwais saurayinta ya fara soyayya da wata bil'adama wato ke."
Idanuwa waje Bilkisu ke kallon Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash tana mamakin yanda ta zama masoyiya ga aljanin da ke da burin ɗaukar fansa gareta.
Cike da al'ajabin maganganun Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash Bilkisu tace, "Ya ke wannan Aljana, ta yaya na zama masoyiya ga wanda ke da burin ɗaukar fansa a gareni ?
Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash tace, yawan ibada da kyawawan halayenki da sanin Alƙur'ani da kikai sosai yasa Abduljalal bin Uwais faɗawa cikin soyayyarki, kuma ina san ki sani shi ɗin bai taɓa neman abu ya rasa ba, a tarihin rayuwarsa, ke ce kawai kika taɓa fidda jini a jikinsa, haka ke ce kawai kika taɓa cin galaba a kansa, hada waɗannan abubuwan suka saka ya fara soyayyarki ba tare da ya fahimta ba sam.
Yanzu zan kawo biyu daga cikin hadimaina ni da ke zamu tafi dajin domin ɗauko Huraira kafin Suwaibatul Zabbar ta cimma ta, tabbas idan ta rigamu kasheta za ta yi idan muka rigata shike nan ta tsira."
Zuwa yanzu zuciyar Bilkisu ta gama bushewa dan haka ta amince da maganar Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash .
Sai lokacin Aljana Rayhanatu ta nemi alfarmar a sake ta ta tafi, amma sai Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash tace, "ke ce za ki kaimu dajin dan haka tare da ke za muyi tafiyar bisa sharaɗin kina neman bijere mana zan kashe ki a kan hanyar."
Sunayen wasu aljanun ta ambata sai gasu sun bayyana ɗaya sak Bilkisu ɗaya kuma sak Inna Huraira, ta je ta kwanta bisa gadon Innar.
Bilkisu ta dube ta, tace "Zuwa gobe kiyi ɗan tauri-tauri domin Baba ya fara samun kwanciyar hankali.
Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash ta dafa Bilkisu ta nuna Aljana Rayhanatu suka ɓace.
Wata uwar dariya Abduljalal bin Uwais (Yah Malam) ya saka, yace "Haƙiƙa Raƙiyyatul Zayyanul murrash kinyi babban kuskure wanda ba zai taɓa gyaruwa ba, domin zan amfani da wannan damar na ci galaba akanki ta hanyar ɓadda Nasir daga duniyar su .
To fa abin ya fara sauya salo fa, ko ya za su kaya ne ?
Ku cigaba da bibiyar alƙalamin Haupha.
managarciya