ANA BARIN HALAL....: Fita Ta 42

ANA BARIN HALAL....: Fita Ta 42

ANA BARIN HALAL...

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe

Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

Idan kana/kina sha’awar:

_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._

_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._

_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._

_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._

_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
*Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t

*Page 42*


*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE  ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559

**********
Isowan shi kenan ya ƙira wayana, lokacin kuma yayi daidai dana idar da sallan ishaa, haka na tashi na ƙarawa hijabin da nayi sallah turare kaɗan, dama an turara shi da kabbasa, ko kula tambayan da hadiza take na ina zanje banyi ba, ɗaukan flask ɗin nayi da take-away dana saka cake a ciki nayi na fice, ina ji suna ta tsokanana, ina isowa jikin motan kuwa ya buɗe mun ƙofan gefen shi, shiga nayi na zauna, duk hankalina yana kanshi,  domin ya kwantar da kanshi akan stearing motan yayi shiru, duk hankali na naji ya tashi, zama nayi na ajiye ɗan basket ɗin dana sako komai,   "Yayah. A.G" na samu kaina da ambatan sunan shi, shiru bai amsa mun ba sai ɗan numfashin shi da sautin yake fita da alaman baya jin daɗin shi,  "don Allah ka ɗago kanka" na sake faɗa, shiru kaman bazai ɗago ba, har na fara tunanin na ƙira yayah Ahmad, sai kuma ya ɗan juyo ya dubeni a hankali batare da ya ɗaga kan shi akai ba,  "Eeshaa nah"   ya ƙira ni a hankali,  ajiyan zuciya na sauƙe a hankali,   "ko asibiti za'aje? Na ƙira yayah Ahmad"?   Tasowa yayi sosai ya zauna yana kallo na,   "sun ganni ae tun da yammah a haka, amma basu damu ba, sai hidiman su suke tayi, M.G wai har dacewa ya kusa samun sauƙi ya huta,  shiyasa nazo wurinki"
Dariya ce tazo mun amma nayi saurin mai da ita nayi murmushi, don yadda ya marairaice mun kaman wani baby yana magana cike da shagwaɓa,   "nikan wallahi da duk kabani tsoro, yanzu irin wannan shagwaɓa kaman baby zaka iya kulawa dani kuwa"? Na faɗa ina kallon gefe don kada dariya yazo mun.
"Beauty ni ae baby ne a wurinki, gaskiya ki shiryah sosai, don kulawa zaki bani kaman baby ɗin, ina son kulawa sosai beauty",  ya faɗa yana wani kashe mun ido.
Da sauri na kawar da kaina gefe, a hankali nace,  "tou ni wa zai bani kulawan"?
"duk ni zan baki, akwai inda dole na naware na baki, amma lokuta da dama aikin kine, kinga ko bacci zanyi sai kin lallaɓani kafin na iyayi",  ya faɗa yana ƙura mun ido, ae kam ban shiryah ba dariyan nan ya kubce mun, ido ya ƙura mun yadda nake ta ɓalɓala dariyan, ɗaga ƙarshe dole shima ya dara kaɗan,  "me ya baki dariya"?
Ido na dukka suna zube akan shi nace,  "tou ba namiji bane yake lallaɓa mace, kai kuma kace ni zan lallaɓaka,  har kayi bacci, tou yayah kake bacci da?"
Ɗan ya mutsa face ɗinshi yayi ya wani tura bakin shi gaba, irin sakalun yaran nan yace,   "ina yaro mummy ke lallaɓani nake bacci, tana shafa kaina tana ɗan bubbuga bayana a hankali har nayi bacci, dana girma kam da ƙyar nake baccin, ina da bashin bacci sosai akaina, sai munyi aure zan biya, zaki lallaɓani baby"?  ya ƙarasa faɗi yana wani langwaɓar da kai kaman zaiyi kuka,  kunya naji maganan shi ya bani, kawai sai na share shi na ɗauko cup  na zuba mishi tea, zuma na saka ina gauraya mishi a hankali, shidai ya wani ƙura mun ido,  nidai ban sake bi takan shi ba na cigaba da juya tea ɗin har ya mun yadda  nakeso, miƙa mishi cup ɗin nayi,  bai sa hannu ya karɓa ba sai ido da ya wani lumshe yana ƙare mun kallo,  "ka karɓa sai na miƙo maka cake ɗin"  na faɗa ina wani mummunan jin kunyar shi,   "ki bani a baki nikam" ya faɗa kaman bashi ba,  "don Allah ka karɓa bazan iya baka ba, ina jin kunyan hakan",  na faɗa still ido na yana kan cup ɗin tea ɗin, hannu ya miƙo na bashi tea ɗin, da ƙyar na juya na miƙa mishi, idon shi akan lallai na,  "woow beauty hannun ki ya ƙara kyau, baby kinyi kyau sosai",  ƴa faɗa yana karɓan tea ɗin,  nidai ban kula shi ba na ɗauko cake guda ɗaya na miƙa mishi,   kai A.G duniya ne, ashe dama haka yake? Baki ya buɗe wai na bashi,  hararan shi nayi nace,   "plz mana A.G" matsu da kanshi yayi kusa da ni murya chan ƙasa -ƙasa yace,   "Eesha numfashi na zai ɗauke, plz ki bani",  da sauri na kai cake ɗin bakin shi, shi kuma ya datsa kaɗan bai sake ba yana kallon ido na, ganin ni dai bazan iya wannan kallon ba kawai na kawar da kaina, ina jin shi a hankali ya dinga gutsura yana shan tra ɗin, yana cinye wa na sake ɗauko wani, a haka yaci har uku, sannan ya shanye tea ɗin,  "thanks" naji ya furta, nidai ban iya na kalle shi ba, kaina a ƙasa nace,   "za'a je asibitin ne?"  "zaki rakani ne"? Juyowa nayi na kalle shi da sauri,  "eh mana, saura 2dys fah ki zama tawa".
Share shi nayi ban iya cewa uffan ba, chan naji yace,   "beauty ɗazu numfashin nan ya takura ni fa, har sai da mummy ta mun allura,  M.G yana ta mita da akace ya ɗan jira ni na huta" ,  ya ƙura mun ido, nima ƙura mishi nayi kaɗan,   "baby ina son ki kula dani sosai, kada ki gajji da A.G ki plz".
Runtse ido nayi sannan na buɗe su akan shi, ganin har yanzu irin kallon yake mun yasa na kawar da kaina gefe,   "Eeshan A.G zata kula da shi har sai ya manta akwai wata kulawa a duniya wanda ba'a mishi ba",  na faɗa cike da jin kunyan shi,   " Eeshan A.G",  ya furta a hankali, sao duk mukayi shiru babu abinda yake tashi sai sautin numfashin shi, wasa nakeyi da zoben hannu na kaina a sunkuye a ƙasa, jikina kuma ya bani idon shi yana kaina.

Aran wayan shi ne ya saka na ɗago kaina a hankali na dube shi, handsfree ya saka yayi shiru,   "A.Gn mummy ina ka shiga ne? Ya ɗan lafah maka? Kazo kachi abinci ko",  dukka naji mummy ta jeho mishi tambayan lokaci ɗaya, idona yana kan fuskan shi ganin yadda ya ya mutsa fiska kaman zaiyi kuka,   "kai mummy na girma fah da tambayan nazo naci abinci, nifa ina wurin Eesha kuma ta ciyar da ni, am ok mummy" ya faɗa yana maida kallon shi kaina, ina jin ta tayi ɗan dariya kaɗan tace,   "ahh tou masha Allah tunda har ka fita wurin doug, ka gasheta tou sai ka dawo",   miƙo mun wayan yayi bata gama maganan ba, jiki na rawa na karɓa nafara gaisheta, cike da jin daɗi ta amsa tana ƙara mun godiya,  nidai bam wani iya sakewa ba na miƙa mata wayan, kashe wayan yayi ya kwantar da kan shi akan stearing motan,  
Chan kuma ƙiran M.G ya shigo, ɗauka yayi ya saka a handsfree,   "Kai ƙaton sakali ba'a sallamu ka bane  har yanzu"?  M.G ya faɗa yana dariyan shaƙiyanci,
"Nakasa sallamuwa ne ƙaton banza, fargaban dawowa nake na kalli mummunar fuskan ka nan, bayan naga kyakkyawan halittah a gabana".

Dariyan mutane dayawa naji, wanda alama ya nuna handsfree suka saka suma, kuma daga ji abokanan su ne, zare ido yayi kaɗan yace,  "mutanen mu sun iso kenan"? Ya faɗa yana wani sosa kai,  M.G yana dariya yace,  "za'ayi fitinannen ango marar haƙuri, tou kadawo ba mutanen mu ba har ƴan Gombe ma sun iso, ga Babban yayanka ma mai baka matar yana jin ka, kabarta ta huta kaz kagaisa da ƙattin munana da suka taro",
Murmushi yayi yana shafa gemun shi, baice komai ba ya kashe wayan ya juya haba ɗaya yana kallo na,  "Beauty naje"?
Murmishi nayi bance komai ba,  "Eeshan A.G",  ya sake ƙirana, nidai ɗaga mishi kai kawai nayi alaman eh,   "tou ko sallameni" juyowa nayi na kalle shi,  "saida safe Allah ya ƙara sauƙi",  na faɗa ina ɗauko basket ɗin da yake ajiye.
"No baby ba haka ba, ki gaya mun wani word da zai mantar dani ganin mummunar fuskan gardawan da zanje na tarar",
murmushi nayi ina ƙara mamakin buɗewar bakin shi, 
"zan gaya maka ta waya",  "naƙi wayon baby, ki gaya mun yanzu, idan ba haka ba bazan iya tuƙa kaina ba",
Kallon shi ina jin tausayin shi a zuciyata,   "Allah ya kaika lpy angon Eesha, yasa har waye gari har ranan da zan zama mallakinka kada mummunar fuskar M.G ya dameka, ko wani lokaci ka dinga tunawa da kyakkyawar fuskar  Eeshan A.G".
tafi naji ya fara yana,  "masha Allah ƴar aljanna, madallah da kykkyawar mace mai daddaɗan lafazi, baby goodnyt",  buɗe motar nayi ban ko iya juyawa na kalle shi ba na wuce cikin gida, duk kunya da mamakin kaina ya rufe ni,  har sai da na daɗe da wucewa tukun ya tafi.


*********
Washe gari friday mukayi kyakkyawan liyafa a haraban gidan mu,  nayi kyau iya kyau, anyi shi kuma ya ƙayatar, dayake bikin gida mu babu african time, dayawa an hallarah, hatta dangi ango da wuri suka iso,  komai yayi babu laifi, haka akayi taro lafiya aka watse lafiya.

 Da daddare Abbah ya ƙirani zuwa parlon shi,  ina zuwa na same shi tare da Ummie, Yayah muhammad, Yayah Ahmad, Yayah Umar, gefe ɗaya ga Aunty Rakiya da Hajiya ummah kusa da shi, wucewa nayi wurin yayah muhammad na zauna a ƙasan inda yake, a hankali duk na gaishe su, shiru nayi kaina a ƙasa, chan naji Abba yace,   "malam muhammadu buɗe mana taro da addu'a ko".

Addu'a sosai yayah muhammad yayo ana binshi da Ameen, bayan ya gama Abba yayi gyaran murya tukun yace,   "Ayshaa ɗago kanki ki kalle ni",  haka na ɗaga kai na kalli Abba,  "kinsan meya taru mu yau duka anan"? Girgiza kai nayi duk jikina a sanyaye,  ƙura mun ido Abba yayi kaɗan har zuwa wani lokaci,  sannan ya buɗe baki yace,  "sallama da nasiha, sallama bawai na rabuwa ba, a'a, sallama wacce take da fa'idah, take da daraja take da muhimmanci, amma a ƙasanta mai ciwo,"  ina jin ya faɗi haka na maida kaina kan ummie danaga gaba ɗaya yanayin ta ya chanja, a hankali na maida kaina kan Abba,   "munyi farin ciki da murna da Allh ya nuna mana wannan kyakkyawan rana na gobe da za'a ɗaura miki aure, wanda shine sanadin sallaman da zamuyi dake bawai don mun ƙosa da ke ba, ko gajjiyawa, sai dai yadda haka addinin mu ya umurta da muyi, Ayshaa da ace uba yana aurar da ƴar shi, kuma ya basu wurin zama su zauna a cikin gidan shi, a al'adance, tou wallahi Ayshaa kece irin ƴar da irin uba irina zaiyi,  tabbas ke ƴace mafi soyuwa a zuciyata saboda halinki da ɗabi'un ki, ni mahaifinki ina miki albishir da cewa na yafe miki a zaman da nayi dake daga ranan haihuwar ki danayi har zuwa ranan da zaki bar hannuna, har ranan ƙarshen rayuwarki, ke ƴar albarkace wacce ta fito a tsatson ƴar aljannah, kinyi dace da mahaifiya ta gari, wacce ta baki tarbiya na gari, wanda shi nake fata Ayshaa ki nuna a gidan auren ki, ki nuna ke ƴar Nana khadijah ce, ki nuna ke tarbiyar Nana khadijah ce, yadda kika zauna lafiya damu, na roƙe ki ki zauna lafiya da mijinki da ahalin shi, yadda kika mana biyayyah kiyi sama da shi wa mijinki, yadda baki taɓa kawo mun ƙorafin kowa ba a gidan nan, don Allah kada ki kawo mun ƙorafin mijinko, don tabbas zan iya ƙinshi, ko mahaifiyar kice kika kawo mun ƙorafinta wallahi zan ƙita a zuciyata ballantana mijinki, ke ƴace lafiyayyah mai mutunta kowa, ina so ki mutunta ƴan'uwan shi da iyayen shi Ayshaa, don Allah kada akawo mun sukanki, kiyi haƙuri ba haƙurin cutarwa ba, idan akwai abunda ya sha miki gaba, ga mahaifiyar ki da ƴar'uwata Rakiya ki tun karesu da shi, na yadda dasu ɗari bisa ɗari zasu baki shawara, kada ki cinye abu a zuciyarki ya illataki irin yadda ya illata ƴar uwarki",  yana zuwa nan ya sunkuyar  da kanshi ƙasa, yayi shiru.
Nidai dama tunda ya fara nake kuka na ƙasa-ƙasa, amma yana zuwa wurin sai sautin kuka na ya ƙaru, hannu yayah muhammad ya ɗaura akaina yana shafa mun,     "Eyyah usumanu kada ka raunana zuka tanmu, wannan rashi na habiba ya ƙone ka muma ya ƙone mu Usmanu,  ga tafiyar baiwar Allan nan da yazama na farin ciki amma kullum fargaba nakeji a zuciyata na kewan da zaka shiga usmanu am,"  ta faɗa tana share hawayenta, ɗago kaina nayi don jin muryan yayah Umar yana, "haba ummie ku da zaku mata nasiha da fatan alkhairi cike da farin ciki shime zaku ɓuge da kuka,? Aunty Rakiya don Allah kuyi haƙuri",  ya faɗa yana ƙara basu haƙuri.

Shiru parlon yayi na lokaci mai tsawo, sannan Abba ya dakatar da shirun,   "Allah ya jiƙan habiba da rahma, Allah ya raya abunda ta bari da imani"   gaba ɗaya aka amsa da   "Ameen"   banda ni kaɗai da na amsa a cikin zuciyata,  "Allah yasa duk abubuwan da nagaya miki kiyi amfani da su Ayshaa,  Allah yayiwa sabuwar rayuwar da zaki shiga albarka,  Allah ya baki zuriya nagari masu albarka,"  "Ameen" kowa ya sake amsawa, Hajiya ummah Abba yace ta yi mun nasiha, amma fir ta kasa,  "usmanu am me zance wanda baka faɗa ba, har ma abunda ni bazan iya ba duk ka faɗa, fata na dai Allah ya zaunar da ita lafiya yadda mahaifiyarta ta zauna da kowan mu lafiya, ae magana ya ƙare tunda tayi dace da uwa tagari irin khadijah, duk da dai dace da miji nagari adali ne ya zaunar da ita lafiya, don babu irinka a duniyan nan usmanu, mahaifin ka sak kabiyo a halin kirki," ta ƙarasa tana ta share hawaye da jan majina.
Ummie Abba ya bada dama ta mun nasiha, amma ummie yau kaman ba ita ba, cewa Aunty Rakiya kawai tayi ta mun, haka kuwa akayi Aunty ce ta mun nasiha da jan kunne sosai akan riƙe sirri, da kiyayan ƙawaye da shawara da su, daga nan Yayah muhammad yayi mun, yayah Ahmad ma ya mun, kowa cike da saka mun albarka,  amma aminin hafsy da Abba yace saura shi, gyara zama yayi sosai ya ƙira sunana da ɗan ƙarfi, har sai da na ɗaga kai na dube shi,   "Abin ƙaunar kowa da kowa a gidan nan, nidai abun da zan gaya miki shine,  HAƘURI! HAƘURI!! HAƘURI!!!
BIYAYYAH! BIYAYYAH!! BIYAYYAH!!!
TSAFTA!
KULA DA GIRKI!
IYA MAGANA!
SUN DANGIN SHI!
wanda duk nayi imani da Allah kin samu training akan su sosai,  na ƙarshw duk wanda ya ɗaga iki yatsa ki sanar dani, idan baiyi hankali ba sai na harbe shi, don da a taɓa mun ke, gara a ɗaga garin bauchi da kewaye, atou gara a san da haka",  ya ƙarasa kowa yana ƙyalƙyalewa da dariya,  ranƙwashi Ummie da ke kusa da shi ta kai mishi tana cewa,  "kaji sarkin hankali babban kobo kawai".
Dariya shima yakeyi yace,  "tou ummie nah idan ba haka nayi ba duk kun raunana mana zuciya, nida nake soja ƙarshe nayi abun kunya na ɓuge da rabza kuka, don ina ganin Abba namijin ƙoƙari yayi bai fashe da kuka ba",  duka dariya sukeyi banda ni dana kwantar da kaina akan cinyar yayah muhammad inata share hawaye nah.
 "aiko zuciya ta sanyaya kaɗan umaru ɗan albarka, ae ni ba ƴan pamilyn mijin nake so ka harbe wa ƙafa ba,"  sai ta ɗanyi ƙasa da murya tace,  "hauwa munfukar gidan nan zaka harbewa ƙafa  don ranan har parlor na ta biyo A.G tana kai sukar uwarku, laɓewa nayi a jikin ƙofa da naji alaman shigowarta, amma da yake Aisha tayi kalan sokaye shiru naji bata gaya mun abun da ya faro ba, shiyasa naƙira ƙanina kawun babanku masaka ayita sauƙan qur'ani, duk sharrinta ya koma kanta, ita ta sani munafukar kawai",  hajiya umma ta faɗa tana ƙasa da muryah.
Abba ne yace "shine ba'a gaya mun ba"?
"Tou wani abu zaka iya wanda bakayi shi ba abaya usmanu? Kawai nagama koai tunda na haɗata da Allah,  kuma zaiyi maganinta",  ta ƙarasa tana hararan Abba da yayi shiru baice komai ba.

Haka dai muka tafi muka barsu a parlon shi da su yayah muhammad.


**********
Washegari saturday
A babban masallacin ƙofar fada aka shaidah ɗaurin auren
*AMINU GARBA INUWA (A.G)  DA AYSHATU USMAN UMAR (U.U)*
sai kuma

*MUKHTAR GARBA (M.G) DA HEEDAYAH GARBA INUWA*

tou jama'a masoyan A.G ina jiran tukwaicin wannan rana daga gareku, yai masu tsoron kada ta auri M.G nawa, da kuma Aliyu mazan ƙwarai ango habiba, duƙ su sake mun mara nayi fitsari, masu cewa idan ban bawa A.G ba sun bar karantawa yau ina jiran tukwaicin ku 
Ruƙayyah Aminu zaki karanta ko sai mext page?
Aunty Rakiya Abbakar yau roƙom ayi aure ya ƙara ko? 
Jikalle duk anyi yadda kuke so yau 
Gobe idan Allah ya kaimu sai na huta ko? 
Ana barin halal group
Muyi nishaɗi
Novel  2
Gidan Aunty nice
Gaskiya writters fan
Duk na baku kyautan wannan page ɗin


*AUNTY NICE*