MAMAYA: Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 19

Page 19
Cikin fuskar rashin walwala ya sake dubanta "Cewa nayi kizo muje asibiti ankwantar da Bilkisu. Banza tayi dashi taci gaba da ƙoƙarin kunna wutar hayaƙinta, tamkar Allah baiyi ruwansa a gunba. Kallonta yayi cike da zafin kai ya kula bama tashi take ba, sai wani ƙoƙarin hura wuta take yanzu ya kula da shigar dake jikinta ma baki ɗaya tamkar wata sabuwar mahaukaciya. Ranshi ne ya ɓaci ko mahaukaciyar ce ba zata tashi haukanba sai da yazo neman buƙatar taimakonta ? Cike da hasala yayi kwallo da kaskon wutar bata ankara ba taga rushin ya watse wani har bisa jikinta, ta fasa uban ihu tana kallonsa hankalinta tashe "Bazan yarda ba wallahi kasan me ka aikata mun kuwa ? To wallahi kayi ƙarya yaro banga uban da zai fitar da kai daga cikin gidan nan ba yau, akan me zaka zo ka tadamin hankali kan wata yarinya marar ji can ? Wannan hayaƙin dakake gani yafi yemun zuwa birnin Makkah balle asibiti matattarar cuta. Gaba ɗaya ya tarkata ƙullin magungunan ya warwatsesu ya zubar, cike da ɓacin rai ya daka mata wata uwar tsawa "Zaki zo mu tafi koko sai kema kin buƙaci ganin likitan ? Kallonsa tayi taga yanda baki ɗaya ya wani juye zuwa suffar ɓacin rai yasa tasha jinin jikinta, "Wani matsiyacin kallo yabita dashi yana ƙoƙarin kwance belt ɗin wandonsa, ai da gudu ta watsa ɗakinta tana "Allah ya isa ban yafe ba, rabbi ya bimun haƙƙina ko cikin dare ne. Bata jima ba ta fito bata canja kayanba balle ta goge tarkacen fuskarta ba, kallon ina zaki haka yayi mata, turɓune fuska tayi dan itafa ba zata cire kayan nan ba sai lokaci yayi ƙilan ta samu wani lamarin yayi tasiri. "Malama kije ki sauya shiga zuwa ta mutunci ki wanke fuskanki ina waje ina jiranki na baki minti biyar ban san ɓata lokaci kin san dai. "Kasan Allah yau sai dai a fasa zuwan amma ban cire kayan nan akan me? Yaro sai sani asara kake kana juyani kamar wata baiwa. " Ban san ace na dakeki ne da tuni na sauya maki kamanni Inna ki guji taɓuwar lafiyarki kiyi abin da nace inba haka ba ya zaro belt ɗin yana naɗesa a hannunsa alamar ko wane lokaci zai iya kai mata duka. Kamar tai kuka haka ta koma ɗakin ta cire kayan ta fito ta wanke fuskar tana rayawa a ranta tana zuwa sai ta ci uban yarinyar akanta akai mata asara mai girma.
Duk abin da ke faruwa akan idonsa ya faru, yanzu wannan shegen yaron ya gama da babin Mal. Aminu kenan dole ya sake wata hanyar domin idan yace yasa shi ya cigaba da takura mata za a samu wanda zai bi diddiƙin lamarin har a bankaɗo sirrin dake boye da Bilkisun abin da bai fata ko kaɗan, yafi san sai ya gama wahal da yarinyar sannan ya kasheta idan yayi hakan ne hankalinsa zai kwanta, sannan yasan cewa ya ɗauki fansar abin da tayi masa.
Kallon wata Aljana yayi yace "Barriratul azam kiyi sauri ki isa asibitin ki tabbatar da kin canja Bilkisun kin maye gurbinta, ki dinga tsorata Huraira da malaman asibitin duk wanda ya nufo ɗakin da nufin taimaka mata. "Angama Yah Malam ta bi iska ta ɓace.
Daga cikin makarantar kai tsaye Babansu Bilkisu kasuwa ya wuce dan yana da tabbacin Nasir zai kula da Bilkisun yanda ya kamata dan haka hankali kwance yayi tafiyarsa kasuwa yana jinjina yanda yaron ke son Bilkisun, murmushinsu na manya yayi sanda ya tuno yanda ya maida fuskar malaminsu Bilkisun.
Sanda suka isa asibitin sosai Huraira ke da niyyar dukan Bilkisun duk da bata ga ya take ba amma tasan hada lalaci da shegen son jiki yasata narkewa dan kawai bata san tayi maganin aljanun dake addabarta ko wace rana, ko a motar daman sai da yayi mata kashedin wai banda hantararta da mata magana cikin tsawa, kamar wani ubanta yaro duk yabi ya takurawa rayuwarta, daga matsalar aljanun gidan sai matsalaisa kawai ke damuwarta yanzu, yaron bai da kunya gashi ba fara'a ko da yaushe fuskarsa ba wasa tana da tabbacin yana iya zaneta cikin gidan nan kawai yasa ta ƙyalesa harma ta biyoshi amma duk zata huce kan ja'irarr yarinyar ta dubesa a fusace tace "Wai uwar me ya sameta ne da kazo ka takurani kai mun uwar asara haka ? Ko inda take bai kalla ba tuƙinsa yake har ya isa asibitin. Tun daga bakin get ɗin asibitin Inna Huraira ta fara rarraba idanuwa, domin ranta bata yayi wayau yayi mata ya kawo ta office ɗinsu ai mata uwar azabarsu ta gado da suka iya ganama bayin Allah.
Cike da tsoro tace "Dan wa uwaka da ubanka ka aje ni anan na koma gida ba zan sake ko kallon inda kake ba, yanda na tsufan nan bani kyan ganuwa idan kukai mun halinku wallahi, nan da nan idanun Inna suka raina fata tabi ta tsure ta nemi fita hayyacinta ba data ga wani soja ya buɗe get ɗin ya kunna motar ciki, tana ganin yanda sojoji ke wali a harabar yasa ta sadaƙar yaron nan ya kawota makisarta, ganin sojoji uku sun rugo duk da bindigu hannunsa yasa ta fasa ihu tai lamo kan kujerar motar tana matse hawayen firgicin gaske. Suna zuwa suka sara masa suka buɗe masa marfin motar ya fice cikin sauri yana gaya masu su fito da Innar zuwa inda Bilkisun take zaije gun likitanne shi.
Wani soja ya buɗe murfin motar yana cewa "Hey madam come aut . Ai sai Inna ta sake cukuikuyewa alamar bata fitowa, to waima uwar me yace mata da yare ne ? Tambayar dake yawo a kwalwanta kenan. "I say come aut Madam. Ya maimaita cikin ɗaga murya abin da ya ida ranaza ta kenan ta fara tsinema Nasir ta uwa ta uba, fahimtar bata gane me yake nufi ba yasa ɗayan bahaushen yai mata magana da Hausa cikin murya mai taushi "Babah kuzo muje a kaiku inda ɗakin yake dan Allah karda Oga ya fito ya iske kunanan komi zai iya faruwa. "Yaro ka tabbatar har ga Allah ba kawo ni yayi ku ci zalina ba ? Kallon rashin gane maganarta yayi mata, amma sanin idan Major ya fito ya iske su gun sune a ruwa yasa ya lallaɓata ta fito kamar ace arr ta ruga suka nufi room ɗin da aka kwantar da marar lafiyar Major ɗin.
Wani irin karkarwa jikinta keyi saboda tsabar zazzaɓin dake jikinta, kamar ana shafa fuskarta haka taji, cikin dauriya ta buɗe idanunta da sukai jawur azabar ciwo, wata mata ta gani da kayan asibiti gashinta fari fat idanunta ma hakan halshenta har kan ƙirjinta hancinta guda ɗaya tal sai ƙaramin baki kamar girman ƙofar hancin mutum.
Rufe idanunta tayi tana karanto addu'ar data samu a zuciyarta, daidai nan Inna Huraira ta bango ƙofar ta shigo kamar an watsota tana dube-dube idonta ya sauka kan gadon da Bilkisun take kwance ga malamar jinya ta juya baya komi take yi oho mata. Ajiyar zuciya tayi ta maida ƙofar ta saka key tace " Masha Allahu yau zanci ubanki daga ke har munafukar malamar asibitin dake gabanki. Fuuu ta iso ta fisgo rigar malamar ta bayanta da zummar tana waigowa ta kwashe ta da mari.
Bilkisu baiwar Allah, tana fara addu'ar barci mai nauyi ya ɗauketa bata sake sanin duniyar da take ciki ba.
Taja-taja taji ta kasa juyo da likitar gata dai ba wata mai girma ba, dan haka saki rigar ta tiƙa mata uban dundu ta bayan tana cewa "Shegiyar nan ina zaman zamana cikin aminci ina maganin damuwata kika sa matsiyacin yaron can yaje ya ƙare mun tujara ya tarkatoni to ta kanki zan fara idan yazo kisa ya halbeni dan ubanki.
Gaba ɗaya ƴan gidansu Malam Aminu sun aminta da ya samu matsala , inba mai matsala ba waye zai yi abin da yake yi haka ? Mahaifiyarsa ta kallesa cike da tausai tace "Kana yawaita addu'a kuwa Aminu ? Na jima ina zargin abubuwan dake faruwa dakai wasu lokutan ina ganinka babu alamar hayyacinka tare da kai, shin ka manta cewa kai malamin islamiyya ne mai koya addu'a kowace iri ? Tunda ta fara magana yake jin jikinsa yayi sanyi, tabbas tayi gaskiya ya manta rabon da yayi addu'a komi ya kwance masa, tunda wata rana da la'asar zashi islamiyya yayi wanka ya fito kenan daga toilet ya ga wata ƙatuwar mage kwance kan katifarsa kamar bata da rai, kasancewarsa mai shegen tsoron mage yasa shi daka tsalle gefe guda yana haki da tunanin ta inda ta shigo ɗakin harma ta mace masa kan katifa, tsabar tsoron da yaji yasa ya kasa taɓuka komi sai kyarma, yana cikin kyarmar yaga magen ta tashi zaune abin mamaki irin zaman mutane tana kallonsa fuska cike da farin ciki har wani murmushi take yi, bai san sanda ya buga ihu ba ya faɗi gun a sume ba, ya jima a haka sai can ya farka lokacin anata kiran magrib. Tun daga ranar ya fara ganin sauyi daga Bilkisu Ahmad duk sanda ya ganta sai gabanshi ya faɗi, wata rana an tashi makaranta sai yaji kamar ana jansa bai tsaya ko ina ba sai ajinsu Bilkisun, yana zuwa ya isketa tsugunne tana toya wasu takardu tana ɓabɓaka dariya mai ban tsoro, ya dubeta cikin mamaki da al'ajabi yace "Bilkisu Ahmad kanki ɗaya kuwa kike anan a wannan lokaci kina aikata shirka ? Cikin wani yanayi ta ɗago ta kallesa ta tuntsure da dariya mai amo tace "Kayi wautar ganina Aminu domin ni ba wanda yasan sirrina na farko balle na uku yau kaga na farkon karkai yunƙurin sanin sauran dan hakan na daidai da shiga daji farautar Sarkin ɗan Sarkin ifiritan duniya da nufin kashe shi, ta sake kwashewa da dariya mai amo tace "Daga yau ni da kai mun fara takun saƙa dan haka karkai tsammanin sassauci kaima bance ka sassauta munba, ta zo ta e shi ta wuce tana dariyar ban tsoro.
Tun daga lokacin yake fuskantar barazana daga gareta duk daren duniya sai ta wahal dashi har wata rana ya ganta tana magana da wata basu san yana bayansu ba, take gayama waccan ɗin cewa "Da Malam Aminu zai gane da ta bani, sai waccan take tambayarta "Akanme ? Sai yaji tace mata "Tace duk sanda na zo islamiyyar nan bana iya kare kaina dan haka yana da ikon rama duk cutar da nake masa da dare. Jin hakan yasashi ɗaukar matakin kullum a makaranta sai ya daketa ya wahal da ita yanda take wahal dashi sune sirrikanta biyu da yasani sai kau na karshen na ganinta tana cin kan mutum ɗanye. Sosai mahaifiyarsa tai masa faɗa kan sakaki da addu'ar da yake yi, wanda ya ɗau alƙawari ya daina sake da addu'ar a ransa harma da fili .
To jama'a ko ya Inna zata ƙare da Aljanar likita data daka ta zaga ?
Taku ce Haupha