HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta 39

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta 39

HAƊIN ALLAH:

   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 


  
                  Page 39

             Kotu

Wajen ya yi tsit sai ƙarar na'ura mai bada iske dake juyawa, sai kuma ƙarar takardu  da ake karantawa.

Magatakarda: ya miƙe ya ce, "Kotu na cigaba da sauraren shari'ar Malama Fatima wadda ta kashe mijinta har lahira, kamar yadda mai Shari'a ya yanke hukunci, don haka idan Malama Fatima na kusa ta matso.

Nan da nan aka fito da Fatima zuwa inda ake ajiye masu laifi.


Alƙali tunda ya shigo yake kallon mutanen wajen musamman masu sanye Da kayan Lauyoyi amma bai ganta ba, hakan yasa ya kasa natsuwa ya jawo wayarsa ya kira lambarta, amma sai ya jita a kashe, nan da nan hankalinsa ya tashi domin yasan da wa take shari'a, yasan basu da imani akan shari'ar nan babu abin da ba za su iya aikatawa ba. Shi kanshi sun ba shi manyan kuɗaɗe sun harhaɗe shi da cewar kar da Barista Alawiyya tai nasara akan shari'ar nan so suke a kashe Fatima kawai saboda son zuciya da ganin bata da kowa bata da galihu. Ya ja ajiyar zuciya lokacin da ya tsinkayi muryar Lauyan mai ƙara na yi wa Fatima tambayoyi.

Lauyan mai ƙara, "Malama Fatima wancan zaman kin maida mutane marassa amfani kin yi amfani da baiwarki kin rufe bakinki ruf kin ƙi bayyana ko da kalma guda ce kan duk wata tambaya da akai maki, hakan na nufin cewa kin san kin aikata laifin da ake tuhumarki baki da bakin kare kanki ne ko ko ya abin yake?"


Fatima, "Ba haka bane ba, wancan lokacin na kasa magana ne sam."


Lauyan mai ƙara, "Ko dai wancan lokacin baki da wata kariya ne yasa ki kai hakan don a dinga jan shari'ar har zuwa lokaci mai tsawo don ki ɓata ma mutane lokaci?"


Barista Alawiyya, "Ya mai girma mai Shari'a ya kamata Lauyan mai ƙara yasan abin da yake gayama wanda ake tuhuma saboda yana sauka kan layi sosai."


Mai Shari'a cike da jin zafin Barista Alawiyya dama ga an ba shi ƴan canji kanta don haka sai ya ce, "Ba ki da ikon hana Lauyan mai tuhuma aiwatar da aikinsa yadda ya kamata ki kiyaye harshen ki."


Lauyan mai tuhuma cike da jin daɗi ya sake duban Fatima ya ce, "An ce dama can baki son shi lokacin da ku kai aure don haka ki ka dinga zubar mai da ciki idan kin samu wanda hakan ya ɓata mai rai sosai har ya taɓa dukanki wanda kika sha alwashin ba zai sake dukanki ba don haka kika kashe shi."


Fatima cikin alamar kuka, "Ba gaskiya bane ba, mijina bai taɓa dukana ba, tunda na aure shi, kuma ba auren dole nayi ba."


Lauyan mai tuhuma, "Kin ce ba auren dole ku kai ba, shin kina da shaidar hakan ne?"


Fatima, hawaye suka zubo mata, domin ta tuna da tsohuwa ko tana ina yanzu? Ita kaɗai ce shedar ta kuma bata san inda take ba, don haka tai shiru.

Lauyan mai tuhuma cikin murmushin mugunta, "Kotu na buƙatar ganin shaidar ki akan ba auren dole ku kai da marigayi ba...

Tsohuwa, "Assalamu alaikum. Ina da magana ya mai Shari'a, domin nice shaidar da ake nema wadda ta bada auren Fatima ga mijinta mai rasuwa."


Nan take sai surutu ya hautsine a kotun, shi kanshi Alƙalin sai ya ji wani iri domin an tabbatar mai da cewar Fatima bata da kowa a Kaduna daga Lagos aka auro ta kuma bata da iyaye irin karuwan can ne kawai aka auro.

Kotu ta ba tsohuwa damar fitowa fili ta tsaya aka bata Alkur'ani tai rantsuwa.

Fatima ta kalli tsohuwa cike da mamaki fal a fuskarta har hawaye suka zubo mata na farin ciki, tabbas ta fita daban a mutane domin ita ce mai kukan farin ciki cikin kukan baƙin ciki a lokaci guda.

Alƙali, "Tsohuwa kotu na buƙatar jin gaskiyar abin da kika sani ga me da auren Fatima da mijinta."


Tsohuwa, cike da natsuwa ta faɗi yadda akai auren ba tare da ta ƙara komai ba ko ta rage komai ba.

Lauyan mai tuhuma, "Tsohuwa to ke ya kike da Fatima ne?"


Barista Alawiyya, "Ina neman alfarmar kotu ta tsawatar wa Lauyan mai tuhuma saboda yana mata tambayoyin da ba huruminsa ba ne ba."


Alƙali cike da fusata ya ce, "Kotu zata kore ki daga wannan shari'ar idan kika sake irin wannan maganar Barista...


Ƙarar sautin takalmi mai tsini ne yasa kowa ya kalli ƙofar shigowa, tana sanye cikin doguwar rigar leshi ta ɗora rigar Lauyoyi bisa rigarta fuskarta kamar ko da yaushe ba wata kwalliya sai kwalli da man leɓe da powder kawai a fuskarta amma sai sheƙi take, Barista Jiddah kenan wadda bata samu damar fitowa da wuri ba saboda ta shiga kasuwa siyen kayan Lauyoyi kasancewar bata da su kuma bata gayama Alawiyya ba saboda tana son ta siya da kanta ne kawai, sai dai kuma suna dawowa ne ta lura da Mustapha bai lafiya sai nishi yake don haka ta sake fita ta siyo mai magani sai dai ba abin da maganin ya yi tamkar ana ƙara mai ciwon ake ma, hakan yasa ta ruɗe ta kiɗime sosai ta rasa abin da ke mata daɗi baki ɗaya sai ta ji ta tsani kanta da kanta, sai a lokacin take jin me yasa bata ce ya koma gida ba tun da ya rako ta? Me yasa ta bar shi nan bayan yana da iyali, tana lura da yadda kowace rana sai sun kira shi kuma ga yanayin fuskarsa ba kiran mutunci ba ne su ke mai ba domin tana ganin yadda damuwa ke kwanciya kan fuskarsa idan yana amsa wayar. 
Shi kuma Mustpha ya yi haka ne daman don kada Jiddah ta je kotun Alƙali ya ganta saboda ya lura da yadda Alƙalin ke son ta, don haka kishi yasa ya kwanta jinyar ƙarya har ma ya daure akai mai allura har biyu don dai kada Jiddah ta je kotun tunda ga Alawiyya yasan zata gama komai.
Sai dai kuma ganin yadda Jiddah ta damu har ta fara haɗa mai kayansa tana cewa za ta saka direban Alawiyya ya kai shi gida yasa dole ya miƙe ya ce mata ya samu sauƙi kuma ba zai tafi ya barta ba, yadda suka zo tare haka za su koma tare.

Shi ne fa da taga ya dawo hayyacinsa ta tuna da wayarta ta kunna sai ga saƙon Alawiyya na cewar idan ba ta zo ba za su faɗi a shari'ar shi ne fa tai gaggawar zuwa kotun yanzu cike da burin cin nasara.

Kai tsaye wajen da Barista Alawiyya take ta nufa bayan ta watsa ma Alƙalin kallo na musamman, shi kau sai da ya yi ajiyar zuciya saboda farin cikin ganinta.

Barista Alawiyya ta koma layin ƴan kallo ta zauna domin ta lura wannan shari'ar ba ta ta bace babu komai cikinta sai tarin cin hanci da soyayya don haka zata koma gefe taga tsakanin soyayya da cin hanci wanne zai galaba.

Barista Jiddah ta bada gaisuwata ta musamman ga Alƙali ta ƙara da bada uzurinta na cewar ta je nemawa ɗan'uwanta Yayanta wanda suke tare magani don haka a gafarce ta sai yanzu ta samu damar zuwa.

Alƙali ya kalle ta fuska cike da fara'a ya ce, "Kotu tai maki uzuri kan koma miye Barista za ki iya cigaba da aikin ki."


Barista Jiddah ta dubi Lauyan mai tuhuma ta ce, "Wannan karon kai zan tambaya Lauya. Shin Fatima ita kaɗai ce a gidan mijinta?"


Lauyan mai tuhuma ya zaro ido waje, domin babu buƙatar sako sunan su Hajiya Turai a shari'ar har a gama ta don haka ya yi shiru.


Barista Jiddah, ta dubi Alƙali ta duka mai murmushi sannan tace, "Ya mai girma mai Shari'a ya kamata Lauyan mai tuhuma ya dinga amsa min tambayata saboda duk suna cikin ƙarin haske kan shari'ar nan."

Alƙali ya maka ma Lauyan harara ya ce, "Kotu na umaryarka daka buɗe baki ka dinga ba Barista amsar tambayar ta tunda ba wajen wasa bane nan ba."

Barista Jiddah ta sake sakar mai murmushi tace, "Godiya nake ga adalin Alƙali, Allah Ya cigaba da kare mana kai daga sharrin masu sharri dai."

Alƙali, cike da ɗoki ya amsa da "Amin Barista."


Barista Jiddah ta sake kai dubanta ga Lauyan mai tuhuma tai mai kallon zaka gane kurenka tace, "Shin matan Marigayin nawa ne, kuma yana da ƴaƴa ko bai da su?"

Lauyan mai tuhuma, cikin in'ina ya ce, "Ina ga kamar yana da mata."


Barista Jiddah cikin murmushinta na rainin hankali tace mai, "Barista kamar ya kana ga yana da mata? Shin baka san waye kake karewa ba ne ko ko ya akai?"


Barista ya kalli Alƙali domin yasan Alƙali yasan komai na case ɗin sun gama tsara komai Yau za ai faka-faka a rufe case ɗin a tura Fatima a kashe ta ta hanyar rataye wa.

Alƙali ya doka mai harara ya ƙara ɗaure fuska ya sake gyara zaman tabaran fuskarsa yai mirsisi.

Barista Jiddah ta kalli Alƙali fuska fal fara'a tace, "Ya kai wannan adalin Alƙali shin wace irin Shari'a ce wannan ake yi? Ta ya za a ce Lauya bai san waye yake karewa ba?"


Alƙali ya kalli Lauya fuska turɓune ya ce, "Kotu bata san wasa balle shashancin banza Barista kasan inda ka ke kafin nasa a tunatar da kai."


Barista Jiddah ta sake wurga ma Alƙalin murmushi shima caraf ya maida mata da martani.

Barista Jiddah ta dubi jama'ar kotun tana murmushi tace, "Ina son tunda Lauyan mai tuhuma bai san wa yake karewa ba to wadda ake tuhuma ta bayyana mana waye shi, sannan ta gangaro kan ita kanta ta bayyana mana wace ce ita saboda wannan hanyar ce kawai kotu zata fahimci gaskiyar lamarin sai kuma na gabatar da manyan hujjojina dake ajiye gefe."

Alƙali ya jinjina kansa alamar ya amince da maganar Barista Jiddah.

Ta taka a hankali ta kalli Fatima tace, "Kotu nasan jin asalin labarinki domin ta ji ta inda kika haɗu da Marigayin bayan ke a Lagos kike shi kuma yana Kaduna."


Kotu tai tsit bayan Fatima ta gama bayyana asalin labarinta baki ɗaya, nan take aka ga Alƙali ya fice zuwa ɗakinsa na hutu ya rufo bai ce komai ba.

Jama'a da dama kuke suke suna ƙarawa da suka ji irin wahalar da Fatima ta sha a rayuwarta, sai kuma aka dinga tambayar ina su kishiyoyin nata su ke? Tabbas ko makaho yasan cewa ba Fatima bace ta kashe mijinta ba su ne suka kashe mata miji don rashin tausayi suka ɗauke mata yara ƙanana.


Tunda ya shige yake goge zufa ya dawo goge hawaye masu zafin gaske da suke zuba mai.

Wace irin rayuwa ce wannan zai kashe ƙanwarsa da kansa don kawai abin duniya? Ashe dama Fatima ƙanwarsa ce da hatsarin mota ya raba su? Ashe daman Fatima na raye sun ɗauka ta mutu ai.

Ya tashi da sauri ya jawo wayarsa ya kira wata lamba, ana ɗagawa ya ce cikin muryar kuka, "Dada kun ga shari'ar Yau da ake gudanarwa kuwa?"

Tsohuwar cikin kuka tace "Tabbas naga Auta ta Muntasir na gane ta ashe dama ban gaya maku ba tana raye bata mutu ba? Daman ban sha cewa ku nemo min Auta ta ba ina yawan mafarkinta ba? Don Allah kai maza ka kawo min Auta ta ko Ni na zo da kaina kotun yanzu."


Cike da farin gane ƙanwarsa yake gaya ma mahaifiyarsa ta zauna yanzu zai kawo mata ɗiyarta har gida ba sai ta zo ba.


Can kotu kuma ganin Alƙali ya tashi ya shige bai magana ba sai abin ya ba kowa mamaki, mutane da dama kuma suka ɗauka tsabar tausayin Fatima ne yasa Alƙali kuka don haka ya kauce wa idanun mutane don ya koka mata lamarin rayuwar tata.

Barista Alawiyya ta dubi Jiddah a ɗan ruɗe tace, "Ban fa gane abin da ke faruwa ba Jiddah yi min bayani."

Barista Jiddah ta dubi Alawiyyar ita ma tace, "Tabbas wani abu zai faru amma ban san ko miye ba, sai dai mu jira kawai."

Fitowar Alƙali ce tasa kowa ya natsu aka cigaba da gwabzawa.

Alƙali ya dubi Fatima, "Shin yanzu ina kishiyoyin naki su ke?"

Fatima cikin natsuwa tai kwatancen unguwarsu don tasan ba inda za su je suna gida.

Alƙali ya bada umarnin a je a zo da su yanzu.

Barista Jiddah ta dubi Alƙali tace, "Zan gabatar da hujjojina wanda nake fatan daga su kotu zata huta daga wannan kai da kawowar da ake ana wahalar da baiwar Allah da bata ji bata gani ba, ta dubi wasu ƴan sanda tace masu, "Kuna iya shigowa da su yanzu kotu nada bukatar su a nan."


Nan take sai ga su Oga Dauda an shigo da su ga yaran suma an kawo su amma har zuwa yanzu barcin dai su ke na sihiri.

Barista Jiddah ta matsa gaban Oga Dauda tace, "Kotu nasan jin ta bakinka akan mutuwar mijin waccan baiwar Allah mai suna Fatima."

Oga Dauda ya gyara tsayuwarsa bayan an ba shi Alkur'ani ya rantse ya zayyana komai ya sani har da rana da lokacin da suka kashe shi sai da ya faɗi.

Kotu ta ɗauki kabbara baki ɗaya.

Daidai lokacin aka shigo da su Hajiya Turai sai zare idanuwa suke.

Ana tsaida su gaban Alƙali suka fara zayyana duk abin da sukai, suna gamawa suka fara ihu suna dariya alamar sun haukace.

Kotu ta bada umarnin a kaisu gidan mahaukata ai masu magani sai ai masu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Shi kuma Oga Dauda aka yanke mai hukuncin zaman gidan yari na har ƙarshen rayuwarsa shi da mutanensa.


Ya kalli Barista Alawiyya ya ce, "Don Allah ki yi min alfarma guda ki kula min da abin da ke cikin masoyiyata idan ta haihu ko miye na baki shi karda ki bari ya yi halina don Allah ya zama mutumin kirki ko na samu sauƙin azabar kabari idan yana min addu'a."


Barista Alawiyya ta amince mai, aka wuce da shi yana yi mata godiya sosai.


Bayan kotu ta watse Alƙali ya dubi Fatima sosai ya ce, "Shin za ki iya tuna wata rayuwa a wata ƙasa a wani bigire a wani babban gida mai ɗauke da mata da miji da yaransu huɗu maza da mace guda waɗanda faɗan boko haram ya tarwatsa su yasa suka bar ƙasar su zuwa  ƙasar Maradi a can ma basu tsira ba sai da suka sake yin gudun hijira zuwa Nigeria akan hanyarsu motar tai hatsari...


Sai Fatima ta fashe da kuka sosai ta miƙe tsaye tana nuna shi da yatsa tace, "Kana nufin Yaya Mansur ne kai? Ashe daman baka mutu ba kaima kana raye?"

Ya kama hannunta ya riƙe gam yana kuka ya ce, "Ba Ni kaɗai ba duk muna raye ku biyu kawai muka rasa a ranar ke da ɗiyar Yaya Amadu Hafsat ku kaɗai muka nema muka rasa sai aka ce mana kun ƙone don haka muka haƙura amma Dada bata yarda da hakan ba tana yawan cewa tana mafarkinki kina raye ashe kuwa da gaskiyarta kina raye Fatima."


Nan da nan Alawiyya ta rungume Mamarta tana tayata murnar gane ahalinta, tsohuwa ma sai kukan daɗi take jin ahalin Fatima na raye har ga Yayanta.

Daga nan suka tattara baki ɗaya suka nufi gidansu Fatima, a unguwar Malamai gida mai girman gaske wanda kana gani kasan masu shi sun tara abin duniya iyakar tarawa.

Suna shiga suka iske baki ɗaya dangi sun haɗu ana jiran zuwan Fatima.

Bayan an gama koke-koke ne Fatima ta sake basu labarinta ta nuna masu Alawiyya da mahaifinta. Ita ma Alawiyya ta basu labarinta dana Baba Hassu nan take kowa ya kama kukan rashin Hafsat ɗiyar babban Yaƴansu Fatima.

Daga nan sai aka koma kan Jiddah ba wanda bai tausayawa rayuwarta ba ita ma, don har babban Yaƴansu Fatima ya ce, "Tunda Babanki bai sonki Ni ina sonki don haka na ɗauke ki matsayin Hafsat kuma za ki cigaba da zama a wajena ni ne zan auradda ke."

Sosai Alawiyya ta ji daɗin lamarin ban da Dr Faisal da Mustapha don sun hango wani babban ƙalubale na shiga tsakaninsu da ita kuma Alƙali ya samu wata babbar damar mallakar ta cikin sauƙi.

Kowa ya watse aka bar Fatima da mahaifiyarta don su gana.

Abin da ya taɓa zuciyar Jiddah kenan ganin yadda Alawiyya ke cikin farin ciki tare da iyayenta suna sonta ita kau bata ma san inda nata mahaifin yake ba ta kama kuka.


Mustapha ma a ɗakinsa sai cakusawa yake da Maryam sai ruwan bala'i take mai ta gaji da zaman kishi da Hafsah sai dai ya zo ya zaɓi guda a cikinsu kawai.

Shi kam abin ma ya yi mai yawa, yanzu kam ji yake komai ya ƙara yi mai girma, ada ya fara mantawa da matsalar iyalinsa da yana tare da Jiddah ko da kiransa su kai sukai mai halin nasu yana aje wayar yake mantawa ba kamar idan ya kalli ɗakin jiddar sai ya ji ba komai su suka sani sui ta yi ma koma miye ya daina damuwa shi da zai mallaki kamar Jiddah miye nashi na nuna damuwa da lamarin su? Hakan yasa ya ƙara ƙiba ya yi haske kamar ba shi ba, yanzu kuma ga shi yana hango wani tarnaƙi na niyyar gitta wa a tsakaninsa da farin cikinsa da Jiddah. Tabbas ba zai iya barin Jiddah ta suɓuce mai ba ko da kuwa zai rasa komai yasan idan ya dace da Jiddah a hankali zai maida komai nasa har ma ya samu cigaba.

Alƙali kuwa yana komawa gidansa matarsa ta nufe shi da jarida cike da ɓacin rai ta wurga mai tace, "Ita kuma wannan daga wane jirgin ka kwaso ta? Kai yanzu ko kunya baka ji kake soyayya da sa'ar ɗiyarka?"

Ya ɗauka ya duba sai ga hoton Jiddah lokacin da take kashe shi da murmushin nan a kotu, sai ya ji kamar lokacin take mai murmushin bai san lokacin da ya saki nashi murmushin ba ya manta da gaban matarsa yake ma.

Ta kuwa fisge jaridar ta yaga ta shige ɗakinta tana cewa "An dai ji kunya idan an san ta, sai kuma ka yi mu gani idan tusa na kunna wuta."

Shi kam farin ciki yasa shi zama a gun yana ƙara hasko fuskar Jiddah a idanunsa.


Alawiyya ta iske Jiddah nata kuka tai ta lallashinta ko bata tambaya ba tasan kukan mahaifinta take sai ta sake jin cewar ya kamata ta gano duk inda yake domin ta tunatar da shi darajar ƴaƴa a rayuwarsa.

Sai da su kai sati guda cif sannan aka maida auren Fatima da Baban Alawiyya suka taho baki ɗaya Kano da danginta don zuwa su ga inda ƴar'uwarsu zata zauna, yaranta kuwa su Hassan tuni aka kai su gun wani Malami ya yi masu addu'a sai ga su sun tashi daga barcin da su ke cike da ƙoshin lafiya.

    

                    Kano

Tun kafin su Jiddah su dawo ta kira Hajjo ta gaya mata komai yake faruwa, sosai Hajjo tai farin ciki kuma tayi na'am da komawar Jiddah Kaduna da zama saboda hakan ne kawai zai sa Jiddah ta sake wayewa ta goge sosai kuma ta sake tsayuwa da ƙafafunta. Don haka ta kira Maman Jiddah tace ta zo Kano ɗin ita ma don su gaisa da iyayen Alawiyya duk da sun ce za su je har garinsu Jiddar amma dai a ganinta gwara ita ta zo nan kawai su haɗu.


Suna zuwa Mustapha ya kasa shiga gidansa don ji yake kamar yana matsawa Jiddah zata koma, shi kuwa bai jin zai iya haƙurin rashin ta ko da na kwana guda ne balle na zaman tsawon lokaci.

Bayan sun gaisa da Mamar Jiddah ne Hajjo tace mai, "Ya kamata ka isa gida su ganka haka nan tunda Allah Yasa an dawo lafiya ko?"

Bai da yadda zai yi ba don ya so ba, haka ba don yana jin kunyar Mamar Jiddah ba da bai tafiya amma tilas ya tashi ya fice.

Ya jima zauren gidan yana jiran Jiddah don ya ɗauka zata biyo shi amma shiru don haka ya sake komawa ciki ya dube ta ya ce, "Ɗan zo mana ki ji." Ya juya zuwa zauren.

Tana cikin yaranta da sai murna suke sun ganta ta miƙe ta bishi a baya.

Yana kallonta yana jin ƙaunarta na yawo a cikin zuciya da ruhinsa, ji yake tamkar ya ɗauke ta ya gudu da ita.

Ko da ya ganta cikin yaranta sai suka birgeshi ya ji dama yaransa ne da suka haifa da ita, ya ji ina ma ace shi ne mahaifan yaran da ya yi murna sosai.

Sai da tayi gyaran murya sannan ya dawo daga duniyar tunaninsa ta dube shi sosai tace, "Na lura kana da damuwa amma sai naga kamar bai kamata nayi maka kutse kan sanin ko wace iri bace, amma zan baka shawara ka rage damuwa bata da amfani ko kaɗan ka dinga haƙuri kana zama cikin farin ciki yafi zama cikin damuwa don Allah."

Sai ya ji yaushe zai sake kamar wannan macen ta kubce mai? Ai kuwa da ya tabbata a cikin masu babbar asarar rayuwa.

Murmushin jin daɗi ya yi na maganarta ya ce, "Tabbas ina cikin damuwa amma ban san ya zan na fahimtar da ke ba, sai dai ban sani ba ko zan iya gaya maki ba a chat saboda gudun faruwar wani abu, idan na gaya maki a gabana ban samu abin da nake nema ba tabbas zan iya samun matsalar sarƙewar numfashi, amma mu haɗu a chat anjima ki kula da kanki sai anjima." Ya wuce ya barta tsaye kamar an dasa ta ya barta da ƙamshin turarensa.

Afnah ce ta biyo ta, sai da ta kama mata hannu sannan ta dawo daga tunanin da bata san me take tunani ba.


Dr Faisal kuwa tunda Jiddah ta bi bayan Mustapha yake sakin tsaki akai-akai wanda tsab Alawiyya ta fahimci abin da ya sashi yin tsakin. Tun a Kaduna ta lura da yadda yake wani shigewa Jiddah yana zaƙewa yana yawan ambatar sunan Jiddah madadin nata sunan, tun a nan ta dasa mai alamar tambaya, sai dai matsayinta na lauya wadda tasan me take bata sha wahalar gane son da mijin nata ke yiwa ƙawarta Jiddah ba. Duk tarin kishinta, duk da tarin son mijinta da take hakan bai sa taji ko da ɗar ba kan hakan, sai dai kuma ta so ƙwarai ita ma ace Jiddah ce kishiyarta madadin wata jakkar da bata san daga wane banzan gidan ta fito ba, amma abin tambayar a nan shi ne waye Mustapha a cikin zuciyar Jiddah? Tasan dai Mustapha na masifar ƙaunar Jiddah ba ita ba kowa ya kalli Mustapha zai ga zallar ƙaunar Jiddah a idanunsa kwance amma bata taɓa ganin son kowa a idanun Jiddah ba, ko da yake Jiddah ta gaya mata ba zata sake aure ba, kamar yadda ba zata sake soyayya ba tunda jahilin saurayin makarantarsu Abubakar ya yaudareta ta tsani soyayya ta tsani yinta. A gefe guda kuma ga kawunta Mansur (Alƙali) dake ƙaunar Jiddah wanda kowa ya fahimta a cikin kotun. Ita kam ta shiga a tsaka mai wuya shin mijinta zata nema wa soyayyar Jiddah ko kuwa Kawunta Yayan Mamarta? Sannan tana bala'in tausayin Mustapha domin ta fuskanci yana cikin matsalar rayuwar aure shi ma.


To jama'a sai ku bata shawara wa zata taimaka mawa ya samu auren ƙawarta Jiddah?


                      Deeni 


             Wasa-wasa Deeni ya koma mahaukaci-.ahaukaci don dai zagi da duka ne kawai bai yi, amma labarin Jiddah da soyayyarta su ne kawai abin da bakinsa ke iya zayyana wa ko da yaushe. Mutane wasu tausayi yake basu yayin da wasu kuma ko a jikinsu gani su ke haka rayuwar take yanzu ai, duk abin da kai zai dawo maka sharri ko khairan don haka shima abin da ya yi ne ke komawa kanshi.

Wata rana sai ga baƙin mutane suka zo gari kai tsaye suka fara tambayar gidansu Jiddah ba su sha wahala ba aka nuna masu, mahaifin Jiddah suka aika nema aka ce bai nan ya koma Lagos da zama, suka tafi suka fara tambayar waye Deeni mijin Jiddah a nan ne ake nuna masu shi aka ce ya haukace.

Waya suka kira sai kuma suka nufi ofishin ƴan sanda sukai bayani nan take sai ga shi an aika an kamo Deeni an basu shi. Suka saka shi a mota suka tafi mutane nata kallonsu suna cewa ko me ya aikata kuma oho.

Tun mutane na maganar har suka daina aka share da babin Deeni.

Kai tsaye asibitin mahaukata suka kai shi, babban Likitan suka nema suka gana, suka tabbatar mai da cewa majinyacin na musamman ne don haka ai mai komai na musamman don ya warke a kan lokaci Madam da kanta ke buƙatar hakan.


Cikin ƙware wa da sanin makamar aiki ake duba Deeni da yake abin bai nisa ba kuma tsabar damuwa ce ta haifar da halin da yake ciki sai ga shi yana samun sauƙi sosai yadda ake buƙata.

               Tun da aka gama komai Mama ta tare gidan mijinta Baban Alawiyya sai tace a bata jikanta na gun Jiddah ta riƙe shi. Cike da jin daɗin karamcin iyayen Alawiyya Mamar Jiddah ta amince ta bada Haidar, sai kuma Kawu Amadu ya ce, "To ai kuwa anyi maki santatta domin nima Jiddah da jikokina su Afnah zamu tafi saboda su samu karatu mai kyau da inganci."

Mama da yake akwai kawaici da sanin ya kamata sai tai murmushi tace, "Ba komai ai, daga ka tafi da su ka rabani da kishiyoyi har biyu ai murna zan don kuɗin Malam sun huta na ƙosan safe."

Kowa gun ya kama dariyar abin da Mama tace.

Sai yamma sosai suka shirya suka wuce amma banda Alawiyya tace ita tare da Jiddah za su taho gobe.

Dare nayi Jiddah ta kwanta ta jawo wayarta gabanta na faɗuwa ta buɗe WhatsApp ɗin ta, sai kuwa ga Mustapha ta gani a online, ta tura mai saƙon: "Barka da dare ya gajiyar tafiya? Na gode sosai Allah Ya bar zumunci."
Yana karantawa ya maido mata da amsar: "Ba wata gajiya sai damuwar rashin ganinki a kusa da Ni baki ɗaya na kasa natsuwa na rasa me ke faruwa da Ni ne Jiddah."

Tana karantawa ta rasa amsar da za ta ba shi amma sai ta samu kanta da ce mai.

"Ta ya mutum kamar kai mai natsuwa da hankali zai rasa gane abin da ke faruwa da shi? Tabbas ya kamata ai maka tambayar me ka sha Yau."


Emojin dariya ya turo mata ya ce, "Ban sha komai ba sai ruwan zafi da ba ko madara."


Ita ma dai emojin dariyar ta tura mai tace, "Ni kam bana maraba da shayi ba madara domin bai min ba sam."

Ya maido mata da amsar, "Ke daman ai duk wanda ya ganki yasan ba kalar ruwan bunu bace ba, wannan ai sai dai mu muma da za ki dafa mana ai da mun shiga cikin hidimar shan madarar."


Wannan karan da tai dariya sai da Alawiyya ta aje abin da take ta kalle ta. Kuma ga shi ta ganta online kuma ba dai da Kawu Mansur take chat ba balle Falsal da damuwa tasa ma ya kwanta duk tasan ta ciwon son Jiddah ce kuma yake. Tunawa da tana da lambar Mustapha yasa ta duba shi sai kuwa ga shi ta ganshi a online don haka ranta ya bata da shi Jiddah ke chat tana dariya.

Sosai Alawiyya take jin daɗin yadda Jiddah take farin ciki domin babu abin da ya rage mata yanzu irin na taga rayuwar Jiddah ta koma kamar tata rayuwar tana tare da iyayenta waje guda tana gidan aurenta komai ya zama tarihi gare ta.

Tunawa da hakan yasa ma ta kira Likitan dake duba mata Deenin cikin sa'a kuwa ya yi mata albishir da warkewar Deeni har ma da kanshi yake neman wadda ta taimake shi ya yi mata godiya.

Murmushin mugunta tai ta nanata kalmar godiya, sai kuma tace "Ba damuwa zan zo gobe insha Allah Likita godiya nake sosai." Ka she wayar tana tunanin Baban Jiddah da ta sa aka kama shi aka rufe a kurkukun Lagos tana ga shi ma can zata tura shi a haɗa su waje guda a ajiye mata su har sai ta neme su.

Duk abin da take ba wanda Jiddah ta sani bata san Alawiyya ta kama Babanta ba haka bata san ta kama Deeni tai mai magani ya warke ba don kawai tafi son ya amshi hukuncin da zatai mai yana cikin hayyacinsa.

Ko da yake ta tausayawa rayuwar Baban Jiddah yadda aka bata labarin ya koma matsiyaci bai da komai bai da kowa shi kaɗai ke rayuwa cike da ganin ƙalubalen rayuwa mai tattare da tashin hankali.

Ko a gidan yarin ta sa an kai shi ɓangaren da ya dace da shi kuma lokuta da dama akan fito da su ai masu wa'azi mai ratsa zukata sosai kan haƙƙin yara kan iyayensu da haƙƙin iyaye kan yaransu.

      Ranar da Jiddah zasu tafi Kaduna ranar kamar Mustapha yai hauka haka yake ji, saboda ya buga ya raya ya rasa hanyar da zai dakatar da tafiyar Jiddah Kaduna. Sai dai ya samu dama guda ta amayar mata da abin da ke cikin zuciyarsa na sonta wanda ita da kanta ta riga ta fahimta kawai dai tana ganin abin ba zai yiyu ba saboda yana da mata har uku ita bata ma san ya rabu da guda ba, ita kam a kan me zata haye ma mai ba ɗaya ba ma har mata uku? Lallai ko a mafarki bata buƙatar irin wannan mafarkin don haka take kaucewa duk maganar da zata haɗa su ta soyayya.

Amma fa ba ƙarya ta san cewa Mustapha shi ne irin mijin da take mafarkin samu, wanda yasan darajar mace yake kulawa da mace yake ƙare lokacin gun saka mace farin ciki.

Ta wani ɓangaren kuma tana jinjinawa rashin kunya da rashin ta ido irin na maza yadda har mijin Alawiyya ya iya kiranta gaba da gaba ya gaya mata yana sonta zai aure ta. Wannan shi ne karo na uku a rayuwarta data ƙara bambance maza basu da tabbas kuma basu san kawaici da halacci ba. Ta tuna yadda ta zauna da Deeni ta kula da shi tai mai duk halacci amma ya yi mata sakin rashin tausayi a gaban gawar Uncle Salim ɗinta. Ta dawo kan Babanta yadda take son shi amma shi ko a jikinshi ganin ƙarshe da tai ma ce mata ya yi zai iya tsine mata idan bata fice daga rayuwarsa ba, me take aika mai da shi ? Nawa take ba shi duk wata? Kar da ya ƙara ganinta a gabanshi.
Na ukku kuma shi ne yadda Abubakar ya ci amanarta ya yi mata abin da bata taɓa zato ba, yasa ta kuka yasa ta tsanar kanta da kanta. To ita kam me ya yi saura a rayuwa da maza da zai birge ta?

Cikin natsuwa ta shirya kayanta dana su  Afnah su kai bankwana da su Hajjo ta fice zuwa gun su Mamar Alawiyya tai masu bankwana daga can wuce sabon garin da zatai rayuwa da sabbin mutanen da zata rayu.

Duk abin da take akan idon shi take yinshi, jikinshi duk ya yi sanyi ji yake tamkar ya sake shiryawa shi ma ya bita su tafi tare amma hakan yasan ba zata faruba.

Ga shi damuwarsa bata amsa mai tana son shi ba ko bata son shi ba, duk lokacin da yai mata maganar takan kawo wata maganar da zata kauda waccan maganar ne.

Sai yamma lis su Jiddah suka isa Kaduna a unguwar Malali gidan yake, tayi mamakin ganin gidan duk yafi sauran gidajen da su ka je haɗuwa, cikin mutunci da girmama juna aka amshe ta kowa na maraba da ita kamar daman an san ta gidan take.


Fitowar ta daga wanka kenan wayarta ta kama rurin naiman taimako. Tana dubawa taga sunan Mustapha ta ɗauka murmushi kwance kan fuskarta.

Sai dai abin da ta ji ne yasa ta tai shiru annurin fuskarta ya ɗauke nan take hawaye suka silalo daga idanunta zuwa kan fuskarta.


Ko me faruwa ? 

Ku biyo Haupha don jin abin da ya faru ga Mustapha har yasa Jiddah kuka.

Taku a kullum Haupha ✍️