LISSAFIN KADDARA: Fita Ta 5 & 6
LISSAFIN KADDARA
*ZAINAB SULAIMAN*
(Autar Baba)
*DEDICATED TO SHAMSIYYA USMAN MANGA*
P*5&6
Bayan sun gama girkin sunci Ameenatuh ta dubi Umma tace"Umma ya kamata mu tafi asibitin nan kan la'asar so nake mu samu Dr Abubakar koya kikace?""ok asibitin nan na Dawakin dakata zakuje?"sai da Ameenatuh ta gyara zama sannan ta amsawa Umma ta "eh""to ai da nasan can zaku tunjiya in dai zamu samu maganin kyauta da sai in goya ita Khadijan mu je tare tunda ba wani nisa sosai""aa ai ba asibitin da nake sa ran kyautar maganin bane kawai dai nafison muje can saboda inaso muga Dr Abubakar, Khadija tashi ki sa hijabi mu wuce",
Suna fita Umma ta tashi ta gyara gidan ta dau bokiti ta fita diban ruwa da yake ba wata tazara tsakaninsu da gurin,
Sunyi nasarar samun Dr Abubakar kuma ya duba Khadija cike da mutuntawa ba kamar wasu likitocin da Allah yayi musu daukaka ba bayan ya gama dubata ne ya rubutamusu magunguna sannan yace"in kun siya ku kawomun na gani sannan in kunje siyan kuce najikin katin akeso kar a baku makamancinsa"godiya sukayi sosai suka fita waje domin na chemist din yafi na asibitin araha,
"dubu shida kudin ku"cewar mai chemist din "to dan Allah ka duba mana wanda suka fi muhimmanci sai ka bani gobe in sha Allah zan zo na sai saura yanzu dubu daya da dari takwas garemu"karbar katin yayi ya kara duba sannan ya mika mata katin "Bari na baku guda daya shine dai babban kuma dubu biyu ne amma ki kawo abunda ke hannunki din"mika masa tayi tana masa godiya cike da jindadi,juyawa yayi ya dauko maganin ya sa matashi a leda sukayi masa sallama suka tafi,
Da kyar Khadija take tafiya daurewa kawai takeyi dan kar yayarta ta ta gane gazawarta hakan yasa take daddafawa tana tafiyar "ki daure Deejan Umma nasan kin gaji gashi baki da lafiyar ciki"murmushin yake tayi dan kuwa tabbas ta gaji din tana neman agaji "Aa sister ba wani gajiya da nayi kinsan na jima banyi tafiya mai nisa ba""hmm" kawai Ameenatuh ta iya cewa suka ci gaba da tafiya dan tasan ko tace zata dauki Khadija bazata iya ba gashi kuma tafiyar ko rabi basuyi ba har Khadijan ta gaji sai da suka fito bakin titi sannan ta fara tsaida napeep domin neman taimakon ragin hanya dan tasan duk inda Dan Adam yake ba'a rasa na Allah,ta tsaida napeep sunfi biyar sai dai ba nasara harta hakura dai da ta juyo taga yadda khadija ke faman rike ciki tana fitar da numfashi da kyar kamar ana fusga yasa ta juya tana kara tsaida napeep ana cikin haka kuwa sukayi sa'a wani yace tazo ta hau,jikinta har bari yake waje kamo Khadija ta dorata akan napeep din tana kokarin sata a booth yayi saurin dakatar da ita ta hanyar you mata magana "Kinga ku shiga kawai tana bukatar hutu"hawayen da ya gangaro mata kan kuncinta ta goge tana masa godiya da addu'a iri-iri,
Har kofar gida ya kaisu daidai ana kiran sallah magrib addu'a kam yashata kala-kala hakan ba karamin dadi yayi masa ba shima yayi mata godiya ya bar unguwar cike da nishadi,
Da sallama suka shiga gidan suka samu Umma tana alwala ita dai Khadija wucewa tayi dakin Umma ta kwanta sai da Ameenatuh ta bita ta bata maganin sannan ta gyara mata kwanciya tana niyar fita Umma ta shigo tayiwa Khadija sannu "kun samu Dr Abubakar din?" Kai Ameenatuh ta gyada kafin tace "har mun siyo magani kin ganshi wai dubu biyu,amma dai akwai saura sai gobe in Allah ya kaimu sai na taho da shi ko"ta karasa maganar tana kallon Umma murmushin yake Umma tayi kafin tace"Allah yayi miki Albarka Ameenatuh Allah yasa bakin wahalarki n..."kuka ne yaci karfin hakan yasa ta sulale a gurin dabas ta zauna tana raira abinta tuni lamarin yayiwa Ameenatuh shigar bazata itama ta zube tana kukan"Umma kece kwarin guiwarmu,kece mudubinmu Umma ki tausaya mana ance kukan uwa ko na farin ciki ne to bala'i ne Dan dan Allah ki rufawa kaskantacciyar rayuwarmu asiri kiyi shiru"ta karashe maganar tana gogewa Umma fuskarta da hijabi jikinta haka nan dai Umma tayi shiru Khadija kuwa tuni bacci ya dauketa batama san wainar da ake toyawa ba,
Bayan ta idar da sallah magrib ta fito cikin shirinta na zuwa aikinta, a tsakar gida ta samu Umma kamar kullum saboda dakin zafi ma kadai ya isheka sakamakon kankantar dakin,zama tayi kusa da Umma tace "tun jiya bamu samu yin magana akan tashinmu ba Umma ni dai ga kayana can da na Autarki na hade mana guri guda naki kuma dama a hade yake gobe ina dawowa zamu tafi ko?""muje ina Amina?""Nigar mana Umma"hararar Ameenatuh tayi sannan tace"haba Ameenatuh naga last year munje ance sun dade da barin garin kinga kuwa ai ba batun zuwa Nigar kuma in ma akwai to da wanne kudin?, kinaga waccen shekarar katifata na siyar mukayi kudin mota na zuwa da na dawowa ba biyan bukata yanzu to da mai zamuje "a jiyar zuciya ta sauke mai nauyi cikin yanayin damuwa tace "Umma banason wulakancin mutumin nan sau biyu yana watsa mana kaya waje bana son gobe yazo ya samemu a gidansa,in na samu dama goben akwai wani mai company a kusa da mu kwanaki na fada miki yace zai dauki mai masa aiki a gida amma mutum biyu yake so, to tun lokacin ban kara ganinsa ba sai jiya kinga goben sai naje na tun tubesa akan batun ko ya kika ga" "eh kuma haka ne Allah yasa a dace Allah yasa yau din yazo sai ku hadu da safen, Allah ya tsareki ya kareki ya tsaremun mutunci Ameenatuh ki kula banda shigeshige Allah ya dubi rayuwarki tashi kije Allah ya fitar dake a sa'a" ameen tace sannan ta kuma shiga ta duba khadija tayiwa Umma sai da safe ta fice a gidan,
Yadda take aiki ba kama kafar yaro hakan ba karamin girgiza mutane gurin yayi ba dan kuwa duk kwarewarka a aiki bai wuce kayi buhu uku a dare days ba sai gashi itakam yau ma kamar jiya buhu hudu tayi hadda rabi kafin gari ya waye kuma tayi sallahrta raka'a biyu kamar kullum ba yawa,
Tasha mamakin ganin mai company a cikin company dan tasan halinsa sosai kamar dan bunsuru haka yake kullum basa wanyewa lafiya da ita da shi abunda ya kara shayar da ita mamaki bai wuce yadda ya sallameta da kanshi ba batare da yayi mata wata maganar banza ba kuma har cikin office dinsa ta shiga,
Haka ta fito da safe fuskarta dauke da annuri ,farin ciki ya gaza boyuwa duk da dai bata hadu da Alhajin da taso haduwarsu ba haka ta nufi chemist din jiya dan karbo sauran maganin khadija dubu hudu ta cika masa ya bata maganin sannan ya bata budu daya yace ta hau napeep sosai ta ringa godiya tare da masa addu'a ta wuce gida,
Gabanta ne ya shiga faduwa sakamakon jiyo amon muryar Alhaji sama'ila yana fama jaraba ko ba'a fada ba tasan bazai wuce a gidansu yake ba, haka ce kuwa ta kasance dan kuwa tijara yake musu sosai yana watso musu kayansu waje yanata bala'i akan idonta ya hankado Khadija ta fada kan wani dutse dake kofar gidan tana kallo Umma ta hanzarta taro khadija amma hakan bai iyuba sai da taje kasa, gaba daya gabobin jikinta karkarwa suke da kyar take daga kafafunta zuwa inda abun yake faruwa hawaye tuni ya gama wanke fuskarta zuciyarta bugawa take na rashin ka'ida da rashin misali da gudu ta karasa inda suke duk da ji take kamar ta badi haka ta karasa ta rungume khadija tare da dafe mata goshinta da ya fashe yake jini...
managarciya