Gwamnatin Sokoto Za Ta Yi Zaɓen Ƙananan Hukumomi

Gwamnatin Sokoto Za Ta Yi Zaɓen Ƙananan Hukumomi

Gwamnatin Sokoto za ta yi zaɓen ƙananan hukumomin jahar nan da wata uku.
Mai baiwa Gwamna Shawara Malami Muhammad Bajare ya sanar da hakan a shirin Sakkwatawa kwallahiya na gidan rediyon Vision fm ya ce da zaran hukumar zaɓen jiha ta kammala shirinta za ta sanar da tsarin zaɓen.
Bajare ya ce bayan kammala zaɓen ƙananan hukumomin gwamnati za ta ba su 'yancin gashin kai Kamar yadda Gwamna ya yi alƙawarin haka.