Buhari da gwamnonin APC sun amince da fitar da shugaba ln jam'iya ta hanyar sulhu

Buhari da gwamnonin APC sun amince da fitar da shugaba ln jam'iya ta hanyar sulhu

Yayin da a ke tunkarar babban taron jam'iyar APC, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Gwamnonin APC sun amince da fitar da shugaban jam'iya ta hanyar sulhu.

A taron da su ka yi a jiya Laraba a fadar shugaban kasa, Buhari ya nuna wa gwamnonin ra'ayinsa na zabar tsohon gwamnan Jihar Nassarawa, Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jami'ya na ƙasa.

Gwamnonin kuma sun amince da zaɓinsa.

An zaɓi tsohon shugaban nahiyar dattijai, Ken Nnami a matsayin mataimakinsa da ga shiyyar Kudu.

Sai kuma Abubakar Kyari, a ka zaɓe shi a matsayin mataimakin shugaban jami'ya na yarjejeniya, ɓangaren Arewa.

Wani gwamna ya shaida wa manema labarai cewa an amince da a fitar da mataimakin shugaban jami'ya ɓangaren Arewa daga shiyyar Arewa-maso-Gabas, shine a ka zaɓi Kyari.