Sanata Wamakko Ya Samar Da Asibitoci 2 Na Zamani A Sakkwato

Sanata Wamakko Ya Samar Da Asibitoci 2 Na Zamani A Sakkwato
 
 
Shugaban kwamitin tsaro na Majalisar Dattawa ta ƙasa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yaƙin Sakkwato ya samarda ayukkan Asibitocin zamani guda biyu a karamar hukumar mulki ta Gudu a Jihar Sakkwato.
 
Asibitocin dai an Samar da su a Garuruwan Karfen Chana da Bachaka dake karamar hukumar.
 
Aikin Asibitin Garin Bachaka tuni ya Kai matakin kashi tamanin na kammalawa ya yin da aikin dake Karfen Chana ya Kai matakin kashi Sittin na kammalawa.
 
Kamar yadda tsohon Dan Majalisar Dokoki ta Jihar sakkwato da ya wakilci karamar hukumar Honarabul Sani Alhaji Yakubu Gudu ya bayyana, ya ce aikin Asibitin Garin Bachaka yana hade da Gidan Likita girmanta  zai iya daukar marasa lafiya 50 a lokaci daya.
 
Shi kuwa aikin Asibitin Karfen Chana zai dauki marasa lafiya 20 a lokaci daya.
 
Rahoton dake shigowa daga yankin mulkin Gudu, ya bayyana cewa, Dan kwangilar da ke aikin yana aikin ba kama hannun Yaro kana ana saran kammala aikin  cikin lokacin da aka shata.
 
Asibitocin guda biyu dai, duk ana yin su ne a wuraren da ake bukatar samar da ayukkan lafiya a yankin mulkin Gudu.
 
Aikin dai yana daga cikin ayukkan ci gaban mazabu da Maigirma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Mai wakiltar Gundumar Sakkwato ta Arewa ya Samar.
 
Managarciya ta samu wannan bayani ta hannun Bashar Abubakar MC, Mataimaki na Musamman ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kan kafar sada zumunta  na zamani.