Yadda Magajin Gari Na 13 Jikan Sardauna Ya Rasu

Yadda Magajin Gari Na 13 Jikan Sardauna Ya Rasu

 

Daya daga cikin jagorori a majalisar Sarkin Musulmi Alhaji Hassan Danbaba bayan rasuwarsa a ranar Assabar an yi masa sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanada, aka bizne shi a makabartar gidansu dake unguwar Binanchi.

Basaraken mai karfi fada a ji wanda yake jikan Sardaunan Sakkwato an bayar da labarin cewa ya yanke jiki ya fadi ne a Otal dinsa dake Kaduna wuraren 11:30 na safe, ana kan hanyar kai shi asibiti ne ya rasu. Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Majiyar ta ce Magajin Gari ya zo Kaduna ne a ranar Alhamis domin yi wa Janar Ali Gusau ta'aziya kan rasuwar dan uwansa.
"Kamar yadda ya saba a duk sanda ya zo Kaduna a Otal din yake sauka dake birnin Kaduna.
"Magaji da Gusau sun shirya za su koma Abuja tare daga Kaduna a ranar Assabar. Bayan ya yi wanka da misalin 11 na safe ya shirya tsaf da nufin zuwa gidan Ali Gusau don ya same shi can su kama hanya zuwa filin jirgi.
"Yana kan fita kenan ya yanke jiki ya fadi, jami'ansa dake tare da shi anan take suka yi hanzarin kai shi asibiti, ana saman hanya ne ya ce ga garinku"
Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i ya  ba da umarnin a kawo gawar magaji a gidan gwamnatin Kaduna domin daukar ta zuwa Sakkwato.
Gwamnan ya yi iyakar kokarinsa na ganin an shirya kawo gawar gidan gwamnati har zuwa  Sakkwato.
Magaji yana cikin jagororin Nijeriya da suka taru a Lagos satin da ya gabata domin samar da mafita ga kalubalen da kasar take fuskanta kan zaben 2023.
Magaji yana cikin daraktocin jaridar Thisday har karshen rayuwarsa.