Daga Babangida Bisallah, Minna.
Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello yayi kiran da a qara albashin jami'an tsaro, masu aiki da wadanda suka yi ritaya.
Gwamnan yayi wannan kiran ne a lokacin bukin ranar tunawa da 'yan mazan jiya na shekarar 2022.
Gwamnan wanda ya bayyana cewar duba da yanayin albashin jami'an tsaro a kasar nan, akwai buqatar ba mu muhimanci saboda irin ayyukan sadaukar da kai da su ke yiwa kasar nan, dan kara masu kwarin guiwa saboda gudunmawar da su ke bayarwa ga kasa, ya kamata karin nan ya zama na kowani lokaci ba karshen shekara ba.
" Abinda muke fuskanta a kasar yau abin takaici ne, ba dan gudunmawar su ba da mun koma baya, shi yasa idan irin wannan ranar tazo muke kokarin kyautata masu, dan nuna masu cewar muna tare da su".
"Abinda muke yi yau, muna nuna masu godiyar mu ne akan yadda suke gudanar da ayyukan su a jihar nan da kasa baki daya. Da yawan su sun samu mummunar matsala a rayuwarsu wajen kokarin kare rayukan mu. Suna bakin kokarin su gaya musamman a wannan lokacin na rashin tsaro.
A jihar Neja ga misali, muna fuskantar matsalar 'yan bindiga masu kashe rayukan jama'a da garkuwa da jama'a, muna da jami'an tsaro da dama suna kokarin kare mu daga wasu sassan jiha".
Maganar gaskiya a yadda kasar nan take yau, albashin jami'an tsaro ba wani abin kaiwa gida ba ne kuma yana taba rayuwarsu wajen karfafa guiwarsu.
Ina da yakinin cewar ya kamata jami'an tsaro masu aiki da wadanda suka yi ritaya ya kamata a kula da su sosai, ina nufin a karfafa guiwarsu da su san cewar kokarin su bai tafi haka nan ba kuma mutuwarsu ba ta banza ba ce.
A na shi jawabin, shugaban kungiyar tsoffin jami'an tsaro ta jiha, Mamuda Baba Ahmed, ya bayyana cewar bukin na wannan shekarar shi ne karrama gwarazan da suka taka rawar gani wajen ganin an samu zaman lafiya da hadin kan kasar nan ta hanyar karrama su.
Yace dukkan tallafin da aka samu daga jama'a za a baiwa iyalan wadanda suka kwanta dama ne.
Ya nemi gwamnati da tallafawa kungiyar da mota dan saukin zurga zurga.