Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu Ya Sauke Dukkanin Kwamishinoninsa
Daga Shu'aibu Ɗan'marayan Zaki Zagga.
Gwamna Bagudu ya amince da rusa dukkanin kwamishinoninsa daga Larabar nan.
Sanarwar hakan ta fito ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun sakataren Gwamnatin Jihar ta Kebbi Alhaji Babale Umar Yawuri mni (Fagachin Yawuri) wacce aka rabawa manema labarai a yau Laraba.
Sanarwar tace Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya godewa dukkanin kwamishinonin nasa bisa irin gudummawar da suka bayar da kuma kwazon da suka nuna wajen gudanar da ayyukan su wurin tabbatar da inganta zaman lafiya da kuma cigaban Jihar Kebbi lokacin da suke rike da mukaman nasu.
Haka kuma sanarwar tace Gwamnan zai sake naɗa wasu sabbin kwamishinonin nan bada jimawa ba.
Kuma sanarwar tayi nuni da cewar wasu daga cikin kwamishinonin da aka sauke zasu iya sake dawowa cikin majalisar ta zartarwar ta Jihar Kebbi tare da wasu sabbi.
managarciya