In Har Na Samu Shugabanci Zan Kare 'Yancin Mata-----Fatima Jajere
A zantawar ta da manema labarai Fatima Isa, tace a wannan lokacin ne ya dace a shigar da mata a tafiyar da ake yi domin an bar su a baya kuma batun gaskiya kamata ya yi ace suna sahun gaba saboda sune masu zabe da suke da kuri’u a hannu. A cewar ta ta fito takarar ne domin wakiltar Matan wannan yankin dan ganin cewa mata sun rasa jagoranci bayan su suke yawo a rana da dare wajen ganin sun zabi shugabanin da suke ganin za su shugabance su sai gashi ana yi babu su. Hajiya Fatima Jajere, tace ko a zaben da ya gabata na 2019 mata sun bada kuri’u da yawa amma sai ga shi basu da wakilci a ma’aikatun gwamnati yadda ake bukata. Tayi amfani da wannan damar ta yiwa mata albishir da cewa muddin ta zama shugabar Mata ta wannan yanki Mata za su san sun samu wakilci kuma za ta yi siyasa kofa a bude wajen bai wa kowacce Mace dama dan ta kawo korafin ta a share mata hawaye.
Daga Habu Rabeel, Gombe.
A kokarin ta na kwato wa mata yanci a arewa maso gabas Hajiya Fatima Isa Jajere, ta fito dan neman shugabancin Mata na arewa maso gabas na jam’iyyar APC inda tayi alkawarin ganin ta tsaya musu dan a dama musu a harkokin siyasa.
Fatima Jajere, gogaggiyar yar siyasa ce da ta jima tana bada gudumawa wajen ganin ta hada kan mata wanda tun kafin ta fara siyasa take taimakawa matan yankin, wajen koya musu sana’oin hannu sannan take tallafawa masu kananan jari a karkashin kungiyar ta mai suna F-Jajere Foundation.
Tace siyasa dole ne sai da mata domin Mace ce tasan ciwon Yar uwan ta Mace kuma ganin ba’a damu da taimaka musu a siyasan ce ba yasa ita da take ciki ake damawa da ita take neman shugabar Mata na arewa maso gabas dan ganin cewa an dama da su.
A zantawar ta da manema labarai Fatima Isa, tace a wannan lokacin ne ya dace a shigar da mata a tafiyar da ake yi domin an bar su a baya kuma batun gaskiya kamata ya yi ace suna sahun gaba saboda sune masu zabe da suke da kuri’u a hannu.
A cewar ta ta fito takarar ne domin wakiltar Matan wannan yankin dan ganin cewa mata sun rasa jagoranci bayan su suke yawo a rana da dare wajen ganin sun zabi shugabanin da suke ganin za su shugabance su sai gashi ana yi babu su.
Hajiya Fatima Jajere, tace ko a zaben da ya gabata na 2019 mata sun bada kuri’u da yawa amma sai ga shi basu da wakilci a ma’aikatun gwamnati yadda ake bukata.
Tayi amfani da wannan damar ta yiwa mata albishir da cewa muddin ta zama shugabar Mata ta wannan yanki Mata za su san sun samu wakilci kuma za ta yi siyasa kofa a bude wajen bai wa kowacce Mace dama dan ta kawo korafin ta a share mata hawaye.
Hajiya Fatima Jajere, ta kirayi shugabani da cewa yana da kyau ana tallafawa mata a dinga tafiya da su a duk wata tafiya ta siyasa dan karfafa musu guiwar fitowa siyasa.
Tace a Arewa maso gabas mata an bar su a baya domin idan mace ta tifo siyasa sai kaga ba’a karfafa mata guiwa da zarar an kafa gwamnati kuma sai ayi banda su inda tace tana so ta canja wannan tsari ya zama komai ana yi da mata.
Daga nan sai tayi kira ga mazaje da su dinga barin Matan su suna fitowa ana damawa da su a siyasa suna ci gaba da bada tasu gudumawa kuma a daina yi musu mummunan fassara.
managarciya