Aisha Buhari Ta Nemi Yafiyar 'Yan Najeriya Kan Rashin Tsaro Da Tsadar Rayuwa 

Aisha Buhari Ta Nemi Yafiyar 'Yan Najeriya Kan Rashin Tsaro Da Tsadar Rayuwa 

 

 Mai dakin shugaban kasa, Hajia Aisha Muhammadu Buhari, ta bawa yan Najeriya hakuri kan rashin tsaro da tsadar rayuwa da ya jefa yan kasar cikin rayuwar kunci a shekaru bakwai da suka shude.

Ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin addu'a da lakca ta musamman don bikin ranar samun yancin kai karo na 62 da aka yi a masallacin kasa a Abuja, rahoton Nigerian Tribune. 

A cewar ta, rage darajar naira da cigaba da faduwar darajar naira a kasuwannin canji ya shafi tattalin arziki wacce ta ce ya yi sanadin wahalhalun da yan Najeriya ke fuskanta wurin ilimi, lafiya da harkokin yau da kulum.
Duk da haka ta yaba wa kokarin dakarun sojoji wurin magance kallubalen tsaro a kasar kuma ta musu fatan alheri. 
"Kamar yadda kuka sani, wani gwamnatin tana dafa da zuwa karshen wa'adinta kuma wanna shine bikin yancin kai na karshe da za ta yi, ina addu'ar mu yi zabe lafiya da mika mulki.
"Ba dole ne gwamnatin ta zama ba ta da nakasu ba, amma ina son yin amfani da wannan damar in nemi yafiya daga yan malamai da yan Najeriya baki daya. Akwai bukatar dukkan mu muyi aiki tare don bunkasa Najeriya."
"Na yi murnar gani cewa jami'an tsaron mu sun tashi suna tunkarar kallubalen fiye da kowane lokaci. A wannan lokacin a baya. A yanzu suna kokarin kawo karshen yan bindiga, masu garkuwa da sauran bata gari. Ina jinjinawa kokarin jarumar jami'an tsaron mu kuma ina addu'a Allah ya kara musu nasara."