Gwamnan Katsina Zai Baiwa  Ƙananun 'Yan Kasuwa  Bashin Biliyan 1 

Gwamnan Katsina Zai Baiwa  Ƙananun 'Yan Kasuwa  Bashin Biliyan 1 

Gwamnatin jihar Katsina ta hada gwiwa da hukumar SMEDAN domin bayar da lamunin Naira biliyan 1 ga kananan ‘yan kasuwa a jihar. 
Gwamnatin Katsina ta nemi wannan lamun ne ta hannun hukumarta ta bunkasa sana’o’i (KASEDA), wanda ke dauke da rangwamen kudin ruwa. 
Mai ba Gwamna Dikko Umaru Radda shawara kan kafofin sada zumunta, Isah Miqdad ne ya sanar da hakan a shafinsa na X. 
Sanarwar Isah Miqdad ta ce an rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a hukumance (MOU) a ranar Alhamis, 25 ga Janairu, 2024, a hedikwatar hukumar SMEDAN da ke Abuja. Sanarwar ta kuma ce wadanda suka aiwatar da yarjejeniyar sun hada da Mista Charles Odii, shugaban SMEDAN, da Misis Aisha Aminu, shugabar hukumar KASEDA.