Yaran Bello Turji 57 Ne Suka Shiga Hannun 'Yan Sanda A Sokoto

Yaran Bello Turji 57 Ne Suka Shiga Hannun 'Yan Sanda A Sokoto

 
 

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta samu nasarar kama 'yan bindiga 57 bayan wasu sun rasa rayukkansu a wani farmaki da aka kai masu a kananan hukumomin Goronyo da Rabah da Illela.

Jami'an 'yan sanda na musamman karkashin jagorancin mataimakin shugaban 'yan sanda na kasa DIG Zaki M. Ahmad ne suka yi nasarar wannan farmakin in da suka kama mutum 37 da ake zargin 'yan bindiga ne sai wasu 20 da ake zargi da hulda da 'yan bindigar kai tsaye.

A taron manema labarai da aka gudanar a Sakkwato Zaki Ahmad ya ce sun samu nasarar kama mutanen ne a wadan nan garuruwan Gudugudu, Illela, Heli, Goronyo, Mayel, Sakanau, Kuka, Zangon Isu, Tsamaye, Dunawa, Tangaza, Isa, Bungo, Sangari da sauransu.
Mataimakin shugaban ya cigaba da cewa sun kama 'yan bindigar ne a wurare mabanbanta kan alakarsu da samamen da ake yi, an kama miyagun makamai hannunsu, "dukkan wadanda aka kama suna da alaka da ayarin sanannen dan bindigar nan Bello Turji, kuma sun fadi suna aikata miyagun laifuka na fashin daji.
"Haka ma ana cigaba ana cigaba da bincike kan lamarin, da zaran an kammala za a kai wadanda ake zargi gaban shari'a." a cewar Zaki Ahmad.
Ya ce daga cikin ababen da aka samu hannunsu akwai shanu 150 da Ak47 guda 32 da harsasai 2700 da babbar bindiga mai harbo jirgi daya da babur biyu da motoci uku da wayar salula 16 da Katon 10 na allurar Penta da sauransu.
A cikin manyan 'yan bindigar akwai Likitansu Abubakar Hashimu Kamarawa da mai kai masu makamai Musa Kamarawa da sauransu.