Zamu Kawo Karshen Rikicin Matasa Dake Janyo Rasa Rayukka A Neja----Babangida

Zamu Kawo Karshen Rikicin Matasa Dake Janyo Rasa Rayukka A Neja----Babangida

Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna

Sakataren kungiyar tsaro tsakanin al'ummar unguwan Dana da ke Maitumbi da jami'an tsaro (Police Community Relations Commitee) na karamar hukumar Chanchaga, Kwamaret Babangida Mudi ya bada tabbacin kungiyarsu na bakin kokarinta wajen kawo karshen rikicin matasa da kan janyo rasa rayuka a wasu unguwanni bisa kwarin guiwar da suke samu wajen jami'an 'yan sanda da gwamnati.

Babangida ya cigaba da cewar yanzu haka mun kafa kwamitoci daban-daban da suka shafi al'ummar unguwar, wanda yanzu haka mun gyara motar 'yan sanda saboda su samu damar gudanar da aikin su yadda ya kamata.

Yace babban matsalar da muke fuskanta shi ne yadda wasu iyayen ke boye 'yayansu idan sun aikata laifi, wajibi ko wani uba ya bari kwamitin tsaro tayi aikinta wajen tsaftace unguwar nan, domin alhakin wannan aikin ya rataya ne a wuyan mu gaba daya.

Yanzu muna da yarjejeniya da 'yan sanda tare da 'yan banga ba wani bata gari da zai janyo rikici ya fado unguwar mu sannan yayi tsammanin ya sha, mun ga yadda take kasancewa a wasu unguwanni cikin garin nan yadda matasa kan dauki makamai suna aikawa jama'a, suna sace-sace wani lokaci har rasa rayuka, duk matashin da muka damke tabbas za mu tsaya kai da fata sai ya fuskanci shari'a, saboda haka duk wanda bai gamsu da matakan da muke dauka ba ya tabbatar ya kwashe inashi ya bar unguwar nan.

Saboda haka zamu cigaba da baiwa jami'an tsaro goyon baya, da aljifan mu da lokuttan mu wajen ganin suna gudanar da ayyukan su yadda ya dace.

Kwamret Babangida, ya nemi mutanen Dana da su cigaba da baiwa jami'an tsaro goyon baya, da kuma hada kai a tsakanin su wajen ganin unguwar su ta zama zakaran gwajin dafi a karamar hukumar Chanchaga da jihar Neja.

Yace wannan shirin na gwamnati na PCRC, wato hadin guiwa ne tsakanin jami'an tsaro da al'umma abin a yaba ne domin zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro a cikin al'umma ta yadda kowani dan kasa na gari zai bada tashi gudunmawa wajen karya lagon matsalolin tsaro a kasar nan, domin shiri ne da duk masu ruwa da tsaki zasu bada tasu gudunmawa ga tsaron lafiyarsu da dukiyoyin su.