Gwamnatin Sakkwato za ta baiwa 'yan Kasuwa tallafin kudi domin bunkasa kasuwancinsu

Gwamnatin Sakkwato za ta baiwa 'yan Kasuwa tallafin kudi domin bunkasa kasuwancinsu

 

Gwamnan Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto ya ce gwamnatinsa nan ba da jimawa ba za ta fara ba da tallafin kudi ga 'yan kasuwa domin bunkasa kasuwancinsu.

 
Gwamna ya ba da tabbacin ne a ranar Assabar da ya karbi kungiyar Zumunta Furniture dake Kofar Taramniya da suak kai masa ziyara ya ce tallafin zai bunkasa kasunci a jihar.
 
Gwamnan ya ce bunkasa tattalin arzikin jiha yana cikin kudurorin gwamnatinsa guda 9, domin ganin an rage zaman banza da cima kwance a cikin matasa.