Samoa: Sheikh Gumi Ya Yi Martani Kan Yarjejeniyar, Ya Shawarci Gwamnati
Sheikh Ahmed Gumi ya yi martani kan yarjejeniyar Samoa da gwamnati ta sanyawa hannu.
Sheikh Gumi ya yi gargadi kan lamarin inda ya ce manakisar Turawa ta wuce yadda mutane ke tunani.
Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da @el_uthmaan ya wallafa a shafin X a yau Lahadi 7 ga watan Yulin 2024.
Malamin ya ce ya duba yarjejeniyar tabbas babu auren jinsi amma akwai ta a kunshe watakila son kudi ya rufewa gwamnatin ido.
Ya bayyana cewa idan Turawa ne, za su iya yaudararsu babu auren jinsi da zarar an zo karbar kudi sai magana ta sauya.
"Daga samun labarin rahoton Daily Trust na cewa an sanya hannu kan yarjejeniyar na kira Minista Atiku Bagudu inda ya tabbatar babu auren jinsi a ciki."
"Ya ce kafin rattaba hannun sun samu ma'aikatu guda uku suka duba suka tabbatar babu abin da ya shafi auren jinsi a ciki."
"Daga baya an turomin yarjejeniyar na gani, maganar gaskiya a bayyane babu amma a kunshe akwai."
"Watakila idon gwamanti ya rufe saboda son kudi ba su kula da hakan ba saboda suna ganin za su yiwa Turawa wayo."