DCP Abba Kyari Da Tsohon Gwamnan Jahar Plato Sunyi Batan Dabo   A Gidan  Yari  Dake Kuje

DCP Abba Kyari Da Tsohon Gwamnan Jahar Plato Sunyi Batan Dabo   A Gidan  Yari  Dake Kuje
 

Daga Jabir Ridwan.

 

A daren jiya ne wasu da ake zargin Yan bindiga ne suka Kai hari a gidan gyara Hali Dake kuje Wanda ya dau tsawon lokaci, daga bisani jami'an tsaro Dake bakin aiki a wajen suka shawo kan matsalar.

 
Yan bindigar dai sunyi amfani da sinadari Mai fashewa Inda suka lalata kayayaki da dama.
 
Tsohon gwamnan jahar Plato Joshua Dariye da takwaransa na jahar taraba Jolly Nyame wadanda majalisar jahohi ta kasa tayiwa afuwa na daga cikin wadanda suke a tsare cikin gidan gyara halin.
 
To sai dai gwamnatin tarayya har yanzu Bata ce uffan ba dangane da wannan lamarin.
 
Wata majiya Mai Karfi da ke kusada gidan gyara halin ta shaidawa jaridar thenation cewa bayaga manyan mutane Dake ciki harda wasu Dake zaman gyara Hali da suka tsere sakamakon duhu da Kuma musayar wuta da Yan bindigar ke yi.
 
Haka ma an ce shi ma Abba Kyari na cikin wadan da ba a gani ba kamar sauran fursunonin dake tsare a gidan.