Gara Ta Lalata Wasu Muhimman  Bayanai Kan Yadda Aka Kashe Naira Billiyan 17: Inji Asusun Kyautata Rayuwar 'Yan Ƙasa

Gara Ta Lalata Wasu Muhimman  Bayanai Kan Yadda Aka Kashe Naira Billiyan 17: Inji Asusun Kyautata Rayuwar 'Yan Ƙasa

Daga Jabir Ridwan.

Jamian Asusun kyautata rayuwar yan kasa ya shaidawa majalisar Dattawa ta kasa cewa gara ta lalata wasu muhimman takardu dake dauki da bahasin yadda aka kashe naira biliyan 17 da miliyan 1.

An bayyana cewa muhimman takardun na dauki da bayanin yadda asusun ya kashe kudin da yayi aiki a shekarar 2013.

Jaridar daliytrust ta ruwaito cewa, Jamian Asusun sun bayyana haka ne a lokacin da suka bayyana gaban kwamitin majalisar dattawa dake kula da yadda aka kashe kudaden gwamnati a ranar Jumua.

Bahasin yadda aka kashe kudaden da wasu na kunshi ne a cikin rahoton binciken kudi na ofishin babban mai binciken kudi na kasa na shekarar 2018.

A cikin rahoton wanda yanzu haka ke gaban kwamitin majalisar dattijai kan binciken yadda aka kashe kudaden gwamnati, ofishin babban mai binciken kudi na kasa ya zargi asusun da kashe biliyoyon kudi ba bisa kaida ba. 

Sai dai jamian asusun sun kasa yiwa kwamitin cikakken bayani kan yadda aka kashe kudaden.