Dokar Zabe:Malami Da Amaechi Da Sauransu Ba Za Su Shiga Zaben Fitar Da Gwani Na Jam'iyyya Ba

Dokar Zabe:Malami Da Amaechi Da Sauransu Ba Za Su Shiga Zaben Fitar Da Gwani Na Jam'iyyya Ba

 

Ministan shari'a babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami da ministan sufuri Rotimi Amaechi da sauran masu rike da mukaman siyasa a Nijeriya dake da kudirin  neman kujerun zabe, ba su iya shiga zaben fitar da gwani na jam'iyyunsu da ake sa ran farawa a watan Mayu har sai sun yi murabus daga mukamansu da aka nada su.

Wannan ya biyo bayan watsar da bukatar shugaban kasa ta yi wa dokar zabe gyaran fuska da majalisar dattijai suka yi a laraba data gabata.

Ofisoshin da zabarsu aka yi kamar Gwamna da mataimakinsa da mataimakin shugaban kasa da 'yan majalisar tarayya dana jihohi suna da damar da za su shiga zaben fitar da gwani ba tare da sun yi murabus ba.

A watan da ya gabata a lokacin da shugaban kasa zai sanya hannu a dokar zabe ya yi kira ga majalisar tarayya ta yi gyaran fuska ga sashe na 84 wanda ya hana duk wanda yake rike da mukamin siyasa da aka nada ba zai shiga zaben fitar da gwani na jam'iyya ba sai ya ajiye aikinsa bai zabe ba a zabarsa  don ya wakilci jam'iyya a takarar kowace kujera a babban zabe na kasa.
Duk jam'iyar da ta kasa biyar wannan dokar a jihohi ko ta gabatar da dan takara ba zai shiga cikin jerin sunayen 'yan takarar da za a zaba ba.

Buhari ya nemi majalisa ta yi gyaran fuska ga dokar domin ta sabawa kundin tsarin mulkin kasa.