Gwamnatin Kaduna ta kulle otel guda hudu bisa kin biyan haraji da ya kai Naira miliyan 16.8
Hukumar tara haraji ta jihar Kaduna, KADIRS, ta rufe wasu otal guda hudu a garin Kafanchan, karamar hukumar Jama’ah bisa kin biyan haraji da ya kai Naira miliyan 16.8m.
Shugaban KADIRS, Jerry Adams ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai bayan sun kai samame a yau Alhamis a Kaduna.
Ya ce hukumar ta gudanar da samamen ne a jiya Laraba a Kafanchan inda ta rufe otal guda hudu, wato; Kyus hotel, Sunshine lodge, Bayan hotel da Cloud-9 lounge, bisa zargin rashin biyan haraji.
Adams ya bayyana cewa, wannan aikin ya yi daidai da ikon da dokar haraji ta jiha ta 2020 ta baiwa hukumar.
Ya kuma bayyana cewa ma’aikatar ta ba da umarnin Kotu na rufe otel din nan take tare da kwace lasisin su har sai sun biya duk harajin da ba su biya ba.
Adams, ya ce kafin aiwatar da aikin, hukumar ta samu umarnin kotu na rufe otel-otel din.

managarciya