Hukumar Zaɓe Ta Sanarda Ranar Zaɓen Ƙananan Hukumonin Jihar Neja

Hukumar Zaɓe Ta Sanarda Ranar Zaɓen Ƙananan Hukumonin Jihar Neja

Za A Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomin Neja Satin Farkon Nuwanbar Shekarar Nan


Daga Awwal Umar Kontagora, A Minna


Hukumar zaben jihar Neja, NSIEC ta bayyana cewar za ta gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi da kansulolin jihar ranar alhamis 10 ga watan Nuwambar shekarar nan da mu ke ciki
A wata takardar sanarwa da shugaban hukumar, Alhaji Baba Aminu ya sanyawa hannu talatar makon nan, yace dokar zaben kananan hukumomi na shekarar 2002 da aka yiwa gyaran fuska da zaben kananan hukumomi na shekarar 2001 da aka yiwa gyara ya baiwa hukumar damar gudanar da zaben.
Ya cigaba da cewar yanzu haka hukumar na shirye shiryen gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi da kansuloli na kananan hukumomi ashirin da biyar da gundumomi dari biyu da saba'in da hudu a dukkanin mazabu a ranar alhamis 10 ga watan Nuwamban 2022.
Yace za a fara tantance masu zabe karfe takwas na safe tare da fara jefa kuri'a zuwa karfe hudu na yamma a dukkanin mazabun jihar.