Dakarun Soji Sun Kama Kasurgumin Ɗan Bindiga Da Wasu Hatsabibai 4 a Zamfara da Sokoto 

Dakarun Soji Sun Kama Kasurgumin Ɗan Bindiga Da Wasu Hatsabibai 4 a Zamfara da Sokoto 

Dakarun sojin Operation Hadarin Daji (OPHD) da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a shiyyar Arewa maso Yamma sun cafke wani ƙasurgumin shugaban 'yan bindiga mai suna, Jabi Ruwa.

Haka nan kuma sojojin sun damƙe wasu kwamandojinsa hatsabibai guda 4 a wani samamen shara da suka kai jihar Zamfara da maƙociyarta jihar Sakkwato. 
Wata babbar majiya a hukumar sojin Najeriya ta shaida wa jaridar Tribune ranar Asabar cewa baki ɗaya hatsabiban yan bindigan da aka kama suna ƙarƙashin bincike. 
Jami'in sojan ya bayyana cewa rundunar Operation Hadarin Daji ta ƙara matsa ƙaimi a samamen da take kai wa maɓoyar ‘yan ta’adda a Arewa Maso Yamma. 
A cewarsa, rundunar zata ci gaba da kai samame sansanonin yan bindiga da nufin kakkaɓe su a shiyyar Arewa maso Yamma wacce ta ƙunshi jihohin Kebbi, Katsina, Zamfara da Sakkwato. 
"A ranar 28 ga watan Yuli, 2023, muna samu wasu sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa wani ƙasurgumin ɗan bindigan daji mai suna Jabi Ruwa da yaransa huɗu sun ɓuya a ƙauyen Dambala." "Bayan tattara bayanan ne dakarun sojin FOB da aka girke a Gwadabawa da sojojin da aka tura Raka, tare haɗin guiwar yan sa'kai suka haɗa tawaga suka durfafi ƙauyem Dambala, suka cafke su baki ɗaya."