Ambaliya: Mutane Sama da 200,000 Sun Rasa Gidaje, Yara Sun Bace a Maiduguri

Ambaliya: Mutane Sama da 200,000 Sun Rasa Gidaje, Yara Sun Bace a Maiduguri

 

Mazauna Maiduguri sun fara lissafa irin asarar da suka yi bayan mummunar ambaliyar ruwa. An samu bayanai kan adadin mutanen da suka rasa gidajensu a birnin Maiduguri a ambaliyar ranar Talata. 

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa har yanzu ba a samu adadin yaran da suka bata a cikin garin Maiduguri ba. 
Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta tabbatar da cewa sama da mutane 200,000 ne suka rasa gidaje a Maiduguri. Hakan ya faru ne sakamakon ambaliyar ruwan da ta kutsa cikin gidaje, kasuwanni da gonakin al'umma. 
Al'umma da dama sun gaza ganin yaransu da yan uwansu da ambaliyar ruwa ta afka musu a Maiduguri. Wata mata mai suna Fatima Ali ta bayyana cewa ta samu kubuta da kyar amma har yanzu bata ga kannenta shida ba. Haka zalika wata mata da ake kira Ya'ana ta ce tun karfe 3:30am aka tayar da ita domin neman mafita amma har yanzu ba ta san inda yaran ta suke ba. The Sun ta wallafa cewa hukumomi sun tabbatar da batan yara sakamakon ambaliyar sai dai har yanzu ba a fitar da adadin yaran da suka bata ba a hukumance. 
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar gidan dabbobi a Maiduguri ta fitar da sanarwa bayan ambaliya ta shiga gidan tare da tafiya da dabbobi masu yawan gaske. Babban manajan gidan dabbobin ya bayyana cewa wasu dabbobi masu hadari da yawa sun shiga cikin al'umma saboda haka aka bukaci yin taka-tsan-tsan.