Matsalar tsaro: Yadda Shugabannin 'Yan Bindiga Ke Jagorantar Zaman Lafiya a Zamfara 

Matsalar tsaro: Yadda Shugabannin 'Yan Bindiga Ke Jagorantar Zaman Lafiya a Zamfara 


Sannu a hankali zaman lafiya na ci gaba dawowa a wasu ƙauyukan da ƴan bindiga ke riƙe da su a jihar Zamfara. 
Hakan ya faru ne sakamakon sulhu da shugabannin ƴan bindiga suka yi da mutanen waɗannan ƙauyukan. 
Jaridar Leadership ta rahoto cewa shugabannin ƴan bindiga huɗu da ake nema ruwa a jallo ne suka samar da yarjejeniyar.
Shugabannin ƴan bindigan su ne Ado Alero a Zamfara ta tsakiya, Bello Turji da Dankarami waɗanda ke yankin Arewa, da Dogo Gide wanda ya ke da yammacin Zamfara Sama da ƙauyuka 100 ne a baya suka kasance a ƙarƙashin ikon ƴan bindiga a faɗin jihar. 
Kowane daga cikin shugabannin ƴan bindigan daga cikin mazaɓun sanatoci uku na jihar, waɗanda ƴan asalin wajen ne, sun mayar da kansu sarakuna inda suke kafa dokoki kan mutane yadda suke so. 
Bayan sauran ƙungiyoyin ƴan bindiga 30 da ke Zamfara, shugaban ƴan bindigan huɗu su ne suke da iko a ƙauyukan da ke a mazaɓun sanatoci uku na jihar. 
Mutanen da ke ƙauyukan yammacin Tsafe a ƙarƙashin Ado Alero, na yankin Dansadau a ƙaramar hukumar Maru ƙarƙashin Dogo Gide da ƙaramar hukumar Shinkafi ƙarƙashin Bello Turji, sun ce suna zaune lafiya da ƴan bindiga. 
Bayan zaman lafiyan da suke yi da su, har kare su suke yi daga hare-haren wasu ƴan bindigan da ba a yankin suke ba. 
Mutanen sun yi amanna cewa Allah ya amsa addu'arsu domin jihar ta samu zaman lafiya kuma manoma za su samu amfanin gona mai yawa. Sai dai, yayin da wasu ƙauyukan ke zaune cikin kwanciyar hankali da ƴan bindigan, wasu ƙauyukan da ke a hannun ƴan bindigan da ke gaba da su Dogo Gide na shan wahala a hannun ƴan bindigan.