Gwamanatin Kebbi Ta Kaddamar Da Sabbin Motoci Ga Rundunar 'Yan Sandan Jihar
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Gwamnan jihar kebbi Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya kaddamar da sabbin motoci masu sulken yaki ga rundunar yan sandan jihar kebbi.
An samar da sabbin motocin ne a cigaba da yaki da masu aikata laifuka da kuma kokarin dakile ayyukan ta'addanci.
Wannan yar manuniya ce kan yadda gwamanatin jihar kebbi ta dukufa wajen kawo karshen matsalolin tsaro a ko ina cikin sassan fadin jihar kebbi.
A yau ne Gwamnan jihar kebbi Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya jagoranci mukarraban Gwamnatin kebbi zuwa Shelkwatar rundunar yan sanda da ke kebbi don kaddamar da sabbin motoci.
Dr Nasir Idris ya kaddamar da sabbin motoci masu sulken yaki ga rundunar yan sandan jihar kebbi domin magance matsalar tsaron da ta addabi al'ummar jihar kebbi.
Gwamanatin kebbi ta kaddamar da sabbin motocin yakin ne ga rundunar yan sanda domin tallafawa yan sanda wajen yaki da yan ta'adda da suka addabi wasu sassan jahar.
managarciya