Gwamnatin Tinubu ƙara talauta ƴan Nijeriya ta ke, in ji Shugaban Yarabawa, Gani Adams
Aare Ona Kakanfo na Ƙasar Yarubawa, Iba Gani Adams, ya koka kan yadda ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta zama me nuna halin ko-in-kula, da rashin tausayi da halin da ‘yan Nijeriya ke ciki.
Adams a wata budaddiyar wasika mai taken ‘Shugaba Bola Tinubu, lokaci na tafiya’, ya kuma ce gwamnatin mai ci ta ci amanar yan ƙasa, inda ya kara da cewa Nigerians ba za su iya jurewa matsin rayuwar da aka jefa su ba.
"A lokacin da ka zo da taken‘Emilokan’ wajen tunkarar zabukan 2023, ‘yan Nijeriya da dama sun gamsu cewa a matsayinka na mai bin tafarkin dimokaradiyya da tsarin mulkin zamani, za ka fi Muhammadu Buhari, sojan da ya ta'azzara talauci ga Nigerians da karuwar rashin tsaro daga 2015 zuwa 2023.
"A yau al’amura sun tabbatar da cewa ba daidai ba ne, mai girma shugaban kasa. Ni gaskiya nake fada ba sani ba sabo, ka kunyata ’yan Najeriya da dama da suka dauka kai ne Almasihun da suke jira.
“Gaskiya ta baiyana. A ranar 29 ga Mayu, 2023, lokacin da ka zama babban kwamandan sojojin Najeriya, farashin litar man fetur bai kai Naira 200 ba.
" A yau, ya haura N1000. A matsayina na Ministan Man Fetur, ina tambayarka, wane irin gyara ne wannan? A watan Mayun 2023, Naira zuwa Dala bai kai N740 ba. A yau, ya haura N1,600.
"Ya shugaban kasa, ba ka ganin miyagu da tsadar man fetur na karuwa, especially, at this time that Nigerians have been pushed to the wall, is a huge recipe for crisis? Nigerians can no longer bear this economic hardship any longer.”
managarciya