Bashin Tiriliyan 77  Da Wasu Abubuwa 4 Da Tinubu Zai Gada Ga Buhari

Bashin Tiriliyan 77  Da Wasu Abubuwa 4 Da Tinubu Zai Gada Ga Buhari

 

Gwamnatin da za ta shigo 29 ga watan nan na Mayu ta Bola Tinubu  za ta haɗu da wasu ƙalubale guda biyar.

Gwamnatin Buhari za ta bar bashin Tiriliyan 77, da maganar tallafin man fetur da maganar fasalin kuɗin ƙasa da rashin aikin yi a tsakanin matasa da maganar ƙidayar jama'a da sauransu.
Maganar tallafin man fetur abu ne da ya ƙi ya ƙi canyewa da ya gagari gwamnati ta magance shi.
Ƙidayar jama'a Buhari ya aminta a yi aikin daga baya kuma ya soke ƙamarin.
Bashin Tiriliyan 77 ya zama abin damuwa ga mutanen ƙasa musamman yanda ake son a yi amfani da harajin ƙasa don biyan bashin.
Hukuma ta tabbatar da rashin aikin 'yan ƙasa ya ƙaru da kashi 40 daga 37 a shekarar 2022