Gwamnan Sokoto ya ba da goron sallah ga dukkan ma'aikatan jiha

Gwamnan Sokoto ya ba da goron sallah ga dukkan ma'aikatan jiha
Gwamnan jihar Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ya aminta da fitar da kudi domin bayar da goron sallah ga dukkan ma'aikatan jiha da masu karbar fansho da masu karbar alawus a ƙananan hukumomi da hukumar kiyon lafiya matakin farko.
Goron Sallar Gwamna ya raba shi gida biyu, ma'aikatan jiha dana ƙananan hukumomi za a ba su dubu 30 kowanensu.
Masu karbar fansho da alawus dana hukumar lafiya matakin farko za su amfana da dubu 20 suma don shagalin sallah.
Wannan kyautar za a fara biya ne daga 13 ga watan Yuni 2024 a gobe Alhamis kenan kamar yadda sakataren yada labarai na Gwamna ya sanar.