Sanata Lawan Babban Jigo ne Wajen Ganin Nijeriya Ta Ci Gaba Da Wanzuwa Ƙasa Ɗaya---Gwamnan Yobe
Daga Muhammad Maitela, Damaturu.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Lawan, a matsayin jigo wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa domin ganin Nijeriya ta ci gaba da wanzuwa a matsayin kasa daya tare da hadin kan ya'yanta.
Gwamna Buni ya bayyana hakan da yammacin ranar Asabar, a lokacin da yake jawabi ga dubban magoya bayan jam'iyyar APC a wani gagarumin liyafar girmama wa wanda gwamnatin jihar Yobe ta shirya domin karrama Shugaban Majalisar Dattawan, a Gashuwa da ke jihar Yobe.
Hon. Buni ya kara da cewa manyan nasarorin da Sanaa Lawan ya samu a rayuwa wadanda suka hada da kishin Nijeriya tare da hadin kan yan kasa, suna daga cikin dalilan da suka tilasta gwamnatin jihar Yobe shirya wannan gagarumar liyafar ban girma a mahaifrsa.
Ya ce, “Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, shi ne shugaban majalisar dattawan Nijeriya na farko wanda ya fito daga jihar Yobe, kuma na farko a Arewa Maso Gabas, wannan babban abin alfahari ne garemu kuma hakan yana da nasaba da hazaka tare da jajircewar sa."
“Sannan duk wanda ya san waye Sanata Lawan zai yi masa shaidar wakili nagari wanda yake aiki domin ganin an wanzar da dunkulaliyar Nijeriya, kullum ha'awarsa ita wanzuwar wannan kasa tamu tare da ganin ci gabanta. Wanda taken sa kullum shi ne 'Unity''.
A hannu guda kuma, ya yaba da muhimman ayyukan raya kasa wadanda ya kawo wa yankin sa da jihar Yobe baki daya. Yayin da ya bayyana cewa ayyuka ne wadanda sun fi gaban a lissafa saboda yawansu tare da muhimmancin su ga ci gaba da inganta rayuwar al'ummar jihar Yobe da Nijeriya baki daya.
A nashi bangaren, shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ce, “Na yi matukar farin ciki da jama’ata suka yanke shawarar karrama ni. Kuma ko shakka babu wannan karramawa ce ga al'ummar Arewacin Yobe baki daya."
“Saboda ba don kun zabe ni a 2019 ba, da ban zama shugaban majalisar dattawa ba. Babu abin da zan fada yayi daidai da kwatankwacin goyon bayan da kuka ba ni a cikin wadannan shekarun da na dauka ina wakilatar ku, amma zai jaddada yi muku alkawari da cewa muddin muka ci gaba da kasancewa tare da gwamnatin tarayya, to kuwa ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba." In ji Sanata Lawan.
managarciya