Buni ya ƙayyade farashin takin zamani kan Naira dubu 13 a Yobe

Buni ya ƙayyade farashin takin zamani kan Naira dubu 13 a Yobe

 

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya tsayar da farashin takin zamani, samfurin NPK kan Naira dubu 13 domin noman bana.

 
A jawabin da ya yi yayin ƙaddamar da shirin takin, Buni ya yi gargaɗi cewa iya manoma kawai za a sayar wa da takin.
 
"Ina mai gargadar ku cewa gwamnati ba za ta lamunci yin sama-da-faɗi ko kuma karkatar da takin ko ma zagon-ƙasa ba.
 
"Jami'an gwamnati da a ka amince da su sayar da kayan, su tabbata sun taba shi daidai a dukkanin Kananan Hukumomi 17 na jihar," in ji shi.
 
Ya kuma yi kira ga manoma da kada su sayar da takin saboda sun same shi a farashi mai sauki.