Hukumar Zabe Ta  Neja Ta Fitar Da Jadawalin Zaben Shugabannin Kananan Hukumomi Da Kansuloli

Hukumar Zabe Ta  Neja Ta Fitar Da Jadawalin Zaben Shugabannin Kananan Hukumomi Da Kansuloli
 

 

Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna.

 

 

A daidai lokacin da ake tun karar babban zabe na kasa a 2023, in da gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello ke cika wa'adinta  karo na biyu, sai ga shu ta fara shirin gudanar da zaben kananan hukumomi.

 
Shugaban hukumar zabe ta jihar, Alhaji Aminu Baba ya fitar da jadawalin zaben shugabannin kananan hukumomi da kansulolin jihar dob zabar sabbin shugabanni. 
 
A baya dai an yi ta dauki ba dadi tsakanin gwamnatin jiha da shugabannin kananan hukumomi dake kan mulki kan wa'adin shekaru biyu da gwamnatin ta bayyana cewar shugabannin kananan hukumomi 25 na jihar  wa'adin shekaru biyu za su yi kan kujerar mulki.
 
Sai dai  bayan wani hukuncin kotu ya janyo aka kara wa'adin zuwa shekaru uku, ganin lokacin saukar yayi ranar 27/07/2023 hukumar zaben ta fitar da jadawalin zaben da ake sa ran fafatawa tsakanin jam'iyyun siyasar jihar.