An Dakatar Da 'Yan Majalisar Dokoki Biyu A Zamfara Bisa Zargin Taimakawa 'Yan Ta'adda

An Dakatar Da 'Yan Majalisar Dokoki Biyu A Zamfara Bisa Zargin Taimakawa 'Yan Ta'adda
Honarabul Magarya

   Biyu daga cikin yan majalisar dokokin jihar zamfara, Yusuf Muhammad Anka wanda ke wakiltar mazabar  Karamar hukumar mulkin Anka, da   Ibrahim T. Tukur Bakura wanda ke wakiltar mazabar karamar hukumar mulkin  Bakura, an dakatar dasu har tsawon wata ukku kafin a gama binciken zargin da ake yi masu na taimakwa yan ta'addan jihar ta Zamfara. 

  An umurce su da su bayyana a gaban kwamitin da ke kula da sha'anin yanayin rayuwa, hadi da jami'an tsaro domin su amsa tambayoyi.

  Wannan wani banga rene da yan majalisun dokokin suka cimma lokacin da suka yi wani  zaman gaggawa  a yau Talata, bisa jagorancin kakakin majalisa  Rt Honorabul  Nasiru Mu'azu Magarya.

  Bayan duk  yan majalisar sun yi rantsuwa da Allah, sai dan majalisa mai wakiltar Maru ta yamma Honorabul Yusuf Alhassan Kanoma, ya  ce akwai wani zargi mai mahimman ci da akeyiwa mutun biyu daga cikin su, wanda yana da kyau a tattauna wannan zargin, domin majalisar ba zata bari wayan nan yan majalisun biyu suci gaba da yin wannan rashin da'a ba.

   Kanoma ya kara da cewa, lokacin da  yan bindiga sukayi garkuwa da mahaifin kakakin majalisa, Alhaji Mu'azu Abubakar Magarya,  Yusuf Muhammad Anka, da Ibrahim T Tukur Bakura sun nuna jin dadin su gameda abunda ya faru. 

  Ya kara da cewa wayanda ake zargin, sune suka kitsa makarkashiyar kashe daya daga cikin mamban su, watau  Honorabul Muhammad G. Ahmad ( walin Jangeru ) mai wakiltar mazabar karamar hukumar mulkin Shinkafi, inda suka hada baki da yan bindigar ta yi masu waya, har aka kai ga halaka shi. 

  "Saboda haka ina kira ga jami'an tsaro da su bibiyi magan ganun da wayan nan yan majalisun suka yi domin kara samun hasken abunda ya faru har aka kai ga hallaka muna abokin aikin mu. 

" Ina kira ga reku sauran yan majilisa da ku gaggauta dakatar da wayan nan mutanen ga duk abunda  ya shafi harkar majalisar dokokin jihar zamfara, har na tsawon wata ukku kafin a gama binciken su."

  Da yake bada tashi gudum muwa mamba mai wakiltar mazabar karamar hukumar mulkin  Birnin Magaji, Honorabul Nura Dahiru Sabon Birnin Dan Ali, nan take ya goyi bayan maganar da Honorabul Kanoma ya fada ta dakatar da su, inda yace duk kokarin da yayi na shiga tsakani da rikakken dan ta'addan nan mai suna  Bello Turji domin yaga an sako marigayi  Alhaji Mu'azu Magarya, bazai tafi a banza ba. Ya kara da cewa duk masu kawo matsalar rashin tsaro a wannan jihar  ba za'a barsu ba sai an gurfanar dasu a gaban kuliya manta sabo domin su girbi abunda suka shukka.

 Da yake yanke hukunci bisa ga wannan badakalar, Kakakin majalisar  Honorabul Nasiru Mu'azu Magarya, nan take ya aminta da kiran da yan majalisar suka yi masa, ya kuma bada umurmin dakatar da yan majalisar biyu da ake zargin har na wata ukku kafin a kammala binciken su. 

 Magarya ya kara bada umurnin  cewa shugaban  kwamitin 
da zai gudanar da  binciken Honorabul Kabiru Hashimu Dansadau  da yayi binciken kwakwaf, akan su kuma ya bada rahoton kwamitin sa, nan da wata ukku lokacin da zasu kara zaman majalisar.
.
  "Nayi matukar bakin cikin wannan tuhumar da akeyi maku na sa hannun ku a cikin matsalar rashin tsaron da muke fama da ita, saboda haka na sauke ku bisa ga kwamitotan da kuke jagoran ta a wannan majalisar, na nada Honorabul Yusuf Alhassan Kanoma ya kula da kwamitin ayukka da zirga zirga, wanda   Yusuf Muhammad Anka ke jagoranta, na kuma nada  Honorabul Nasiru Atiku Gora, jagoranci kwamitin jinkai da walwala, wanda ada can  Ibrahim T Tukur Bakura, ke jagoran ta". Inji Magarya.

Daga Aminu Abdullahi  Gusau.