Nijeriya na cikin ƙasashen da aka fi yawaitar mutuwar aure -- Rahoto

Nijeriya na cikin ƙasashen da aka fi yawaitar mutuwar aure -- Rahoto

Shafin Divorce.com na kasar Amurka da ke bada shawarwari don kaucewa  mace-macen aure, ya sanya Nijeriya a matsayi na 7 cikin kasashe 26 da aka fi samun yawaitar mutuwar auren.

Premium Times ta rawaito cewa ya Divorce.com ya fitar da sakamakon ne bayan binciken da ya gudanar daga kasashen kuma ya tattara bayanai bisa tsarin ka'idar binciken.

Rahotan ya kuma bayyana cewa, mata a kasashen yammacin Afrika, mussaman Nijeriya su ne ke haddasa yin sakin aure fiye da maza.

Acewar bayanan, kasar Maldives ce ta daya wajen sakin Aure da kaso 5.52 sai kasar India wacce ta zama mafi kankanta a batun mutuwar aure da kaso 0.01.

Kasar ta Maldives ta zama ta farko ne kasancewar mata a kasar suna dogaro da kansu ta hanyar kudade ba tare da miji ba kuma ba a samun tsangwama ga matan da aurensu ya mutu.

Haka kuma, ana samun karancin mutuwar aure a India kasancewar Aure na da tsada, haka kuma mata na shan wahala idan an sake su.

Acewar rahotan, mutuwar Aure a Nijeriya ya kai kaso 2.9 a shekarar 2023.